Skip to content

Chapter 52

Chapter 52

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

Ke kuma ya faɗa min suna ki Hafsatu ko?” Mishal na murmushi tace. “Hafsat dai, amma Mishal ake cemin” Anna ta yi dariya tana kallon Kuliya da ya maze yana kallon tv, kamar ma be san abun da suke ba. Anna ta ƙwalawa Siyama kira. Ba tare da wani ɓata lokaci ba, sai ga Siyama ta bayyana a falon. Kamar yanda dalar ƙanƙara ke zaftarewa ta faɗi a yayin da zafin rana ya bugeta, haka zuciyarta ta zaftare ta faɗi lokaci guda, sakamakon idonta da ta ɗora a kan wata kyakkyawar yarinya me kama da 'yartsana, zaune a gefen Anna. Ganin Kuliya da ta yi a gefe guda ya sa ta ji ƙarar faɗowar wani abu a ƙirjinta, kenan wannan ita ce matar Kuliya?, in dai kuwa wannan ita ce matar da ake ce ya aura, to babu ta yadda za ayi Kuliya ya kalli inuwarta bare ita kanta. Duk da ta san cewa ita ma tana da kyau dai-dai gwargwadon, kuma a shekaru ba za ta wuce 23 ba, amma tun da Kuliya ya riga ya samu wannan kyakkyawa kuma sabon jini irin wannan yarinyar babu abun da zai yi da ita. Yanzu ita shi kenan ta rasa Kuliya?, to yanzu ina za ta sa kanta?, ba ta jin za ta iya rayuwa me kyau tare da wani namijin da ba shi ba, ko da da take faɗin ta haƙura da shi faɗa kawai take, don ba ta hangowa kanta rayuwar da babu Kuliya a cikinta. “Ba ki ga matar yayanki ba ne? Ki gaisheta mana” Muryar Annan ta dawo da ita zahiri, hakan yasa ta ɗauke idonta daga kan Kuliya da ta kafe da kallo, ta dawo da su kan 'yar ficilar yarinyar dake gefen Anna, duk da ba za ta kirata da yarinya can ba, don jikinta a murje yake, ta na da duk wata cikar sura irin ta 'ya mace, babu abun da Siyama za ta faɗa mata da ya wuce yawan shekaru. “I'm the one that supposed to greet her... Tun da ita ce babba” Sassanyar Muryar yarinyar ta kuma katse mata tunani. “A'a ita ya kamata a ce ta gaida ki” Siyama ta haɗiye wani ƙullutun baƙin ciki a sanda take gaida yarinyar, cikin mutuntawa Mishal ta amsa ta, cikin san gano wani abu tsakaninta da Kuliya, don da ace ƙanwarsa ce kamar yanda Anna ta faɗa, ko kallonta ya yi, amma ji yanda ya hakimce ya na kallon tv abunsa kamar bai san akwai wasu hallitu a falon ba, kuma duk ta lura da irin kallon da Siyaman ke binsa da shi tun sanda ta shigo falon. “Anna! Na roƙi wani abu a wurinki?” Mishal ta tambaya, bayan da Annan ta sa aka kawo mata abinci, zuwa lokacin Kuliya ba ya falon, don waya ce ta sameshi daga wani wai shi Symon, kuma bisa ga dukkan alamu maganar aiki ce, hakan yasa ya fice daga falon baki ɗaya, wannan Siyamar ma ba ta falon, saboda ba ta jima da shigewa ɗaya daga cikin ƙofofin dake falon ba. “Ina jin ki 'yata, faɗi ko me kuke so, in dai bai gagara ba zan miki shi da yardar Allah!” Mishal ta aje spoon ɗin hannunta tana sosa kai. “Da ma so nake ki masa magana kan ya siyo min kaya girki, ina so na riƙa yin girki da kaina. Abincin wajen nan ba ya min daɗi” Anna ta yi 'yar dariya. “'Yata kin iya girki ne?” Da sauri ta gyaɗa kanta tana faɗin. “Sosai ma kuwa, tun ina da shekara goma sha ɗaya na fara girki fa” ”Aaaa, ahse 'yar tawa babbar cooker ce” Mishal har da dariya, irin an yabeta ɗin nan. “To kada ki damu. Da yardar Allah zan sa ya sai miki kayan girki, ta yadda za ki riƙa yin girkinki da kanki” “Kai amma fa da na ji daɗi Sweet Anna” Anna ta kwashe da dariya, da ma Rahila na ba ta bayanin yarintar Mishal ɗin, ba ta taɓa ɗaukar cewa haka take ba sai yau, amma ita yatinyar tata ta birgeta, don akwai nustuwa a ciki. Siyama dake cikin ɗaki ta silale a kan gado tana danne bakinta da hannunta, gudun kada kukan da take riƙewa ya suɓuce mata, da ace ta na da ikon cire son Kuliya a ranta da ta yi ta huta da wannan azabar da take sha, ta gaji, Wallahi ta gaji har ranta, amma soyyayarsa ta hanata gannin gazawarta. Ta riga ta yankewa kanta hukuncin gobe da sassafe za ta haɗa kayanta ta koma gidan Anti Karima, don su sake sabon lale. ___________________ _Salmanians, shin ba mu jawa Siyama kunne kan kada ta fara ba?_ _Godiya ta musamman zuwa ga dukan Salmanians na fili da na ɓoye, haƙiƙa kune ƙwarin gwiwata a ko da yaushe_ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *13* ~~~ *Some people are your happy pill, no matter how sad you are...* *** Follow my Wattpad account 👇 https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends ~~~ *Brickhall school, Kaura District, Abuja.* RABI'A POV. Za ta iya!, tabbas za ta iya. Wannan shi ne abun da take faɗawa kanta, a dai-dai lokacin da take tsaye a filin ball ɗin makarantar, sanye take cikin kayan ball ɗin da Mishal ta ba ta jiya, a cikin filin kuma akwai wasu 'yan mata guda biyar, waɗanda su ma ke sanye cikin kalar nasu kayan wasan ball ɗin. Daga can wajen ragar filin kuma, Mishal ce tsaye, ta yi ƙuri da idonta a kansu, yayin da take jiran ganin salon wasan Adawiyyan. Rabi ta lumshe idonta na wasu 'yan sakkani, kafin ta buɗesu ta ɗora a kan ball ɗin dake tsakiyarsu, daɗewar da ta yi ba ta buga ball ba ba ya nufin cewa ta manta yanda ake buga ball ɗin, ko wani salo da ko wani taku na yin ball babu wanda ta mance, a da tasha dakun rana makamanciyar wannan, yau sai ga shi Allah ya cika mata fatanta, don haka za ta gwada, za ta gwada duk wata iyawa tata a kan wannan wasan. Cike da ƙwarewa suka fara wasan, a tashin farko sai da suka ci Rabi sau biyu, duk da Mishal ta yaba da iya wasan nata sai da ta sare, amma kuma bayan tasu nasarar sai Rabin ta shiga yankasu, ba ta sarara ba sai da ta ci su uku. Wani irin ihun murna da Mishal ta saki ne ya sa hankalin kowa ya dawo kanta, don zuwa lokacin hatta da ɗaliban dake kaikawo a wurin sai da suka tsaya kallon wasan, don wasan nasu akwai ban sha'awa. Da gudu Mishal ta shiga cikin ragar ta rungume Rabi suna dariya, ba tare da sun ankara ba suka hautsina suka faɗi ƙasa, Mishal ta sauƙa daga kan Rabi ta kwanta a ƙasa suna dariya, ba ƙaramin burge Mishal Rabi ta yi ba. Ita kuma Rabi tana farin ciki ne don samun damar buga ƙwallo bayan tsawon lokaci, ita kanta ba ta zaci cewa za ta iya buga wasan da kyau irin haka ba, bayan shuɗewar wani dogon lokaci, yau ita ce take dariya sosai, wadda take fitowa tun daga ƙasan ruhinta, har ta manta rabonta da ta yi irin wannan dariyar. RAJA POV. Tafe suke shi da Rabi a kan titin Joy Emodi CI,

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112