Chapter 97
Chapter 97
f... Fyaɗe!” Wani irin duka Zaid ya kaiwa katangar dake gabansa kamar zai fasata, a fusace ya juyo zai kuma dawowa kansu, amma Rhoda ta yi saurin riƙe shi. “Ya isa haka Zaid.... Ya isa, tun da sun riga da sun amsa lefukansu, ka ƙyalesu kawai!” Leɓensa na ƙasa ya ciza ya na huci, ji yake kamar wuta ce ke ci a ƙirjinsa, kamar idan be daki bayin Allahn nan ba ba zai huce ba. KULIYA POV. “An ce yau Lion ya kawo ziyara fa!” Da sauri ya ɗauke idonsa daga kan laptop ɗin gabansa ya kalli Symon dake wannan batu. Symon ya gyaɗa masa kai. “Da gaske nake, haka na ji ɗazu ana ƙus-ƙus ɗin zancen... Amma an ce bai jima ba ya tafi, kuma ma wai na ji ana cewa ya kawo ƙarshen assignment ɗinsa ne” Ba shiri Kuliya ya saki wani murmushi, dan kuwa burinsa na gab da cika, Chidera ya masa alƙawarin daga zarar Lion ya kammala assignment ɗinsa zai haɗasu. Har ya tashi daga aikin ransa ƙal, haka ya nufi gida cikin farin ciki. Da sallama a bakinsa ya tura ƙofar falon gidan nasa. Mishal dake zaune a kan kujera tana rubutu ta aje rubutun ta iyo kansa da gudu, shi ma yana dariya ya buɗe mata hannyensa ta shige jikinsa, harda ɗagata sama, dan tsabar farin cikin da yake ciki. “Wannan farin cikin fa?... Na menene?” Mishal ta tambaya a sanda ya sauƙeta. Hancinta ya ɗan ja yana murmushi. “Kin tuna da labarin wani lion da na baki?” Ta ɗan yi shiru tana san tunawa, can kuma sai tace. “Haaaa! Na tuna... Ko ba labarin wannan zakin da yake cinye 'ya'yan wata barewa ba?... Wannan wanda ka karanta min a cikin littafin stories ɗin nan?.” Kuliya ya dunguri kanta yana faɗin. “Silly girl, ba shi ba, wannan role model ɗin nawa da na taɓa baki labari, ki tuna” “Eh yanzu na gano... Kun haɗu ne?” Kansa ya girgiza yana ɗaga kafaɗarsa. “A'a, da yarar Allah mun kusa haɗuwa dai” “To Allah ya yarda... Yanzu ka je ka yi wanka, na tanadar maka abincin da ka fi so” Peck ya mata a kumatu yana sakinta. “Ok bari na yi sauri” Mishal ta bi bayansa da kallo tana murmushi. *No.86, Garki 2, Abuja...* *10:30pm* RABI POV. Tana daga zaune a falo tana warewa Zaid kayan bikin da Umma ta bata ta kawo masa, dubulan da alkaki ne, cikin wata farar roba guda ta bata tace ta kawowa Zaid. Ta kasa misalta kalar farin cikin da take ciki a yau, dan sai a yanzu take ganin rayuwarta ta dawo dai-dai, rayuwarta ta hau seti, wani irin setin da a da ma bata dedetu kamar yanzu ba, Allah ya shirya Abbansu, Habiba ta gane kurenta, Mama ta yi nadama, Allah ya bata miji na gari, budu da ƙari yau an ɗaurawa Anti Saratu aure da mijin da take so, kuma a yau ita ma anti Saratun za ta kwanan gidan mijinta, menene ya fi wannan daɗi?. Jin an banko ƙofa yasa ta miƙe da sauri tana kallon side ɗin ƙofar. Ganin Zaid ya shigo cikin wani irin yanayi ya sa da sauri ta nufe shi tana faɗin. “Raj!... Me ya sameka?” Tsayawa ta yi a gabansa tana dubansa, kallonta kawai yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa duka. Gaba ɗaya oxford shirt ɗin jikinsa ta jiƙe da gumi, tie ɗin ya warware a wuyansa, ga kuma suit ɗin riƙe a hannunsa. Ba tare da ta ankata ba ta ga ya saki suit ɗin daga hannunsa, sannan ya fincikitota ta faɗo jikinsa, ƙanƙameta ya yi kamar me shirin tsaga ƙasusuwanta. Wannan sanyi Rabi ta ji ya shiga bin jikinta, ga wata siriryar iska da ta ke bi ta saman kunenta. A hankali ta ɗago da hannunta ɗaya ta ɗora shi a kan bayansa, ɗayan kuma ta ɗora shi a kansa. “Menene ya faru?” Ta tambaya da ƙyar. Saboda shirin zamewa ta faɗi ƙasa da take. Zaid ya ƙara matseta a jikinsa ya na faɗin. “Na je Madallah, sai suka ce min wai kina gida” Kanta ta gyaɗa tana shafa bayansa. “Umm... 'Yan kaiwa amarya na bi, kuma da muka gama da gidan amaryar sai kawai na ce su kawoni gida, na san babu abinci a gidan, shi ya sa na dawo na maka girki” Sai ya saketa yana kallon fuskarta. “Ammata!” Rabi ta amsa tana kewaya hannayenta ta bayansa. “Dan Allah kada ki rabu da ni... Ko me zai faru ki zauna da ni... Dan Allah!” Rabi ta girgiza masa kai. “Ban taɓa tunani rabuwa da kai ba Raj... Za ku rayu tare har zuwa lokacin mutuwar ɗayanmu” Haɓarta ya kama yana matsar da fuskarsa kusa da tata. “Kin tabbata?” Ta gyaɗa masa kai, wanda yasa nasa kan ma kotsawa, dan zuwa lokacin ya haɗe goshinsa da nata yana goga mata hancinsa a kan nata. Rabi ta lumshe idonta a hankali, sakamakon ɗumin leɓensa da ya sauƙa kan nata. Zaid ya soma kissing ɗinta kamar yau ya fara. A hankali Rabi ta ture shi tana faɗin. “Ka je ka yi wanka” Sai ya girgiza mata kai yana ƙara kamo hannunta. “No... I just need you” Ya ƙarashe yana mannata da jikinsa. Rabi ta kuma tureshi. “Ka fara zuwa ka yi wanka” Sai ya shinshina jikinsa yana faɗin. “Wari kika ji ina yi ne?” Duka ta kai masa a ƙirji tana faɗin. “Haka na ce?” Hannunta ya ƙara kamawa ya mayar kan ƙirjin nasa. “Ba haka kika ce ba...” “To ka je ka yi wanka” Kansa ya gyaɗa yana sakin hannunta. Sannan ya kama hanyar stairs. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••••••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *25* ~~~ *Heart broken over a love that didn't even exist...* *** *No.181, Guzape, Abuja...* MISHAL POV. Zaune take kan gadonta, babban yatsan hannunta na dama sanye a bakinta tana sha. Hannunta na hagu kuma riƙe da wani littafi me ɗauke da rubutun "The Happiest Baby on the Block" . Kuliya ne ya shigo ɗakim yana dube-dube, tare da faɗin. “Hafsat ina kika aje min cable ɗin system ɗina?...” Ba tare da Mishal ta kalleshi ba ta amsa masa da: “Ka duba drawerta. Yana ciki” Drawer ya nufa, ya shiga duddubawa, kafin ya samo abun da yake nema, har ya juya ya nufi ƙofar ɗakin, sai ya tsaya ya kalli inda take. Abun na farko da ya fara kalla shi ne, sunan littafin dake hannunta. Wata dariya ta shiga ƙoƙarin ƙwace masa, amma sai ya shanye yana kallonta. “Mishally!” Hannunta cikin baki, kuma ba tare da ta kalleshi ba ta amsa da. “Umm!” “Me kike ne?” Ya tambaya yana isowa jikin gadon, littafin ta sauƙe ta kalleshi. “Littafi nake karantawa a kan yara!” Ta amsa masa tana maida littafin saitin fuskarta. Dariya ya yi mara sauti, ya zauna a bakin gadon, hannunsa ya miƙa saitin side drawer ya aje cable ɗin da ya ɗauka. Sannan ya dawo da dubansa kanta, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana cewa. “Yara kike so?” Da fara'arta ta sauƙe littafin kan cinyarta, har wani farr ta yi da idonta kafin tace. “Ehen nah!” Ya yi dariya yana sosa kansa. “Da gaske kina san yara?” Sai kuma ta cire hannunta daga bakinta tana ɓata fuska. “To wai miye na tambayar?”
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112