Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

da ƙaninsa, ɗan uwansa abokin tagwaitakarsa. Sai ku ma Maman Rhoda, wata mace da ta taka rawa mai makuƙar muhimanci a cikin rayuwarsa. Wani irin wahallallen nunfashi ya ja, ya samu kansa cikin irin yanayin da ya saba shiga a duk sanda zai ga wutar. Duk da yanda yake ta kokawa da tunaninsa kan kada ya koma baya, amma sai hakan ya ci tura. LABARINSA na baya ya soma kunno kai cikin nazarinsa. _“Zaid, ku tafi, kada ku tsaya a nan.....idan kuka tsaya wutar za ya iya ƙona ku....ku tafi na ce!.....” _ Amon wannan sautin nata ya shiga maimaita kansa a cikin tunaninsa, falon ya shiga rikiɗewa yana komawa gidansu, gidan da suka rayu a ciki, gidan da suka ci gaba da kwana a cikinsa har bayan sanda wuta ta gama ɗaita shi, wannan gidan da suka gina yarintarsu shi da ƙaninsa a ciki. Sannan hoton ya sauya a idonsa, ya na ganin yanda take watso musu kayansu ta window, yayin da ƙofar falon take a kulle, ta kasa fitowa bare ta buɗe ƙofar har ta samu damar tsira. Sannan ya kallin kansa da ma ƙaninsa Aliyu dake ta kuka, ƙaninsa me tsantsar kama da shi, dan idan suka kalli juna sai ka ce kansu suke kallo a madubi. Dan kammanin da suke ya ɓaci, tsayinsu ɗaya, farar fatarsu ɗaya, girman idonsu ɗaya, komai na hallitarsu ɗaya ne, in ka ɗauke ƙwayar idon Zaid da ta kasance ash, sai kuma totsiyar karen dake haƙorin Zaid ɗin. Amma hatta wata ɗabi'a ta ɗaga kafaɗa dukaninsu suna yi. “Jagwado menene haka ?, Sarai ka sani cewar Raja ba ya san ganin wuta!” Muryar Rhoda da ke wa Jagwado faɗa ta dawo da shi zahiri. Bai ƙara ce musu komai ba, ya miƙe tsaye, tare da ɗaga kafaɗarsa ta dama, ya yi ɗakinsa, yana jin yanda Rhodan ta balbale Jagwado da faɗa, shi kuma sai aikin bata haƙuri yake. _________________ _To fa.... Bana kuma nan muka leƙo?_ _Na ce ba, wai Rajan ne ko Zaid ne?_ _Dan ni na kasa ganewa, kamar Zaid da Aliyu mutum ɗayane, kamar kuma....._ _Ko da yake, ba sai na faɗa ba ai😂_ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #Taurariwriters °°°°°°°°°°°°°° *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *04* ~~~ _-*What she really craves is a wild love, from a steady pertner...*-_ *** *1987* Alhaji Ali Wakili, babban mutum ne me tarin arziƙi. Haifaffen garin haɗejia ne, kuma ya ci gaba da zama a cikin garin har bayan lokacin da ya fara tara iyali. Kasancewarsa mutum me nasibi a harkokin kasuwancinsa, ya sa shi gyara gidansu na gado, ya ci gaba da zama a ciki shi da 'yan uwansa. Alhj Ali na da mata biyu, hajiya A'i, yaransu tara da ita mata biyar maza huɗu, matan sun haɗa da Lawisa, Fatsima, Kaltume, sai 'yan biyun gidan, Maryam da Rabi'a, Mazan kuma sun haɗa da, Abdullahi, wanda ya kasance shi ne na farko, sai Mansur, Haladu da lawan Hajiya Kande ita ce matarsa ta biyu, yaranta huɗu da shi, kuma dukansu maza ne, Kabir, Sagir, Jamilu da kuma Jibrin. Duka yaran gidan suna karatu, matansu da mazansu, kuma duk da kasan cewar sun taso a gidan yawa, akwai zaman lafiya a tsakanin yaran ahalin, dan iyayensu jajirtattu ne a kan tarbiyar yaran nasu. Rana ɗaya da gaba ɗaya ahalain gidan ba zasu manta da ita ba ta kasance Asabat, inda labari ya riske su cewar an yi wa Rabi'a 'yar biyun Maryam fyaɗe. Duk wani nau'i na tashin hankali babu wanda bai yi ba a gidan, dan da aka tambayeta ta shin san wanda ya mata fyaɗen?. cewa ta yi bata sani ba, dan hankalinta a gushe yake. Haka aka gama jajjaɓin lamarin kafin aka watsar da zancen, kowa ya ci gaba da lamuransa. Bayan kwanaki da faruwar lamarin, Alhj Ali ya nemawa Maryam gurbin karatu a garin Suleja, dan haka ta tafi can ta ci gaba da karatunta. Watanta ɗaya da tafiya, alamun samuwar ciki suka fara bayyana tattare da Rabi'a. Tun tana ɓoye abun har ya zo ya bayyana, har kowa na gidan ya sani. Alhaji Ali ya yi tsallen albarka ya ce sai dai a zubar da cikin. Itama kuma Rabi'a ta yi tsallen albarka kan cewar ba za ta zubar da cikin jikinta ba, hakan yasa shi kuma yace sai de ta bar masa gidansa. “In dai har ba za ki zubar da cikin jikin ba sai dai ki bar min gidana Wallahi!...” Haka ya faɗi, a ranar da yake watso mata kayanta ƙofar katafaren gidan nasu. Gaba ɗaya mutanen gudan sun firfito, an tsaya a bakin gate ana kallon abin da ke faruwa. Babu yanda yayun Alhaji Ali ba su yi da shi ba kan ya yi haƙuri, amma ya ce Wallahi sai Rabi'a ta bar masa gidansa, dan baza'a haife cikin shege a gidansa ba. Ba zata ɓata masa sunan zuri'a ba. Rabi'a ta tsugunna ta tattare sauran kayan da Abban nata ya watso mata, sannan ta haɗe su a wuri ɗaya, tana ta sharar hawaye. A hankali ta miƙe ta kalli idon Abban nata. “Da na zubar da cikin jikin, gwara na bar maka gidanka Abba.... Ba zan roƙi ka bar ni na zauna a gidan ka ba, abinda ya sameni ƙaddara ce daga Allah, kuma shi ne zai temakeni na iya cinyeta.....Ni dai buƙa tata ita cee ka yafe min Abba!....” Ta ƙarashe tana fashewa da kuka, babu wanda bai ji tausayinta ba a wurin, amma banda Alhaji Ali, wanda ya kawar da kansa gefe, ya gwammace da ya sallamarta, da ta ja masa a bun kunya, ace yau a gidansa aka haifi ɗan gaba da fatiha?, kuma ace 'yarsa ce ta cikinsa?. “Na san ba lalle ka yafe min ba, amma ni dai ina meneman yafiyar taka, zan yi nesa da kai, zan yi nesa da gida, zan je na haife cikin jikina, kuma zan basu labarin abinda rayuwata ta fuskanta sakamakon fyaɗen da aka min ba tare da san rai na ba...Yaran da aka haifesu ba tare da aure ba suma 'ya'ya ne, ƙaddara ce ta hukunta zuwansu ba tare da auren ba!...” Ba tare da ta sake cewa komai ba ta ɗauki sauran kayanta tana ta sharar hawaye, ta kama hanyar barin unguwar tasu. Sai da ta yi tafiya mai nisa, sannan ta ji muryar mahaifiyarta na ƙwalla mata kira. Cike da mamaki ta juya. Da gudu ta ruga wurinta tan kuka, suna haɗewa ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana sakin sabon kuka, Ita ma Hajiya A'in kukan take. Kafin ta share hawayenta ta ɗago da 'yarta. Hannunta ta kama sannan ta danƙa mata wata jaka. “Akwai kuɗi, da takardun karatunki a ciki, sannan akwai takardun gidana na kano a ciki... Ban ce ki faɗawa kowa inda za ki ba.... Ni dai ina so ki je ki kafa sabuwar rayuwarki a garin kano, idan zai iyu bayan kin haifi yaranki, ki yi aure Rabi'a!.....” Rabi'a ta ƙara faɗawa jikinta tana sakin sabon kuka. “Aure be dace da ni ba Mama, sanin kanki ne babu namijin da zai auri macen da ta yi ciki ba tare da aure ba” Hajiya A'i ta shiga kwantarwa da 'yarta hankali, tana haɗa mata da nasiha, har zuwa lokacin da suka yi sallama. sallamarsu ta ƙarshe kenan.

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112