Chapter 8
Chapter 8
mu juya....” A wannan karon fushi ne kwance a fuskar matashin. “Waye shi ?, kira mana shi ya zo ya ƙwata da ƙarfinsa” Bisa ga mamakinsa sai ya ga budurwar tana murmushi. Sannan ta juya kanta kaɗan, ba tare da ta kalli bayanta ba, idonta a kan matashin ta kira sunan na cikin motar. “RAJA!” A hankali mutumin cikin motar ya buɗe idonsa dake rufe, kafin ya sauƙe kansa, idonsa ya sauƙa a kan mutanen dake gaban motar tasu, ɗan guntun tsaki ya ja. Sannan ya buɗe ƙofar motar ya fito. Hannunsa kan ƙofar motar ya ci gaba da kallonsu. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya kai hannu ya sodai tattoo ɗin kan zakin dake bayan wuyansa, ya fara takawa zuwa wajen da suke tsaye.A gaban matashin ya ja ya tsaya. “Ka bamu kayan za mu juya” Muryarsa me cike da kamala da kuma nutsuwa ta furta, idan ka ji muryarsa ba tare da ka ganshi ba sai ka rantse da Allah ba daga bakinsa ta futo ba, dan sam yanayinsa baya kama da yanayin muryar tasa. “Sai kun bamu kuɗi tukkuna“ Raja ya kuma yin guntun tsaki, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Kana ji ko bana san jayyaya, sannan nakan jima banyi fushi ba, ka bamu kawai mu juya” Wannan karon muryar tasa cikin wani irin taushi ta fito. “Ni ma ba na san jayyaya.....” Bai ko gama rufe bakinsa ba, Raja ya ɗauke shi da mari, sannan ya ci kwalarsa da hannunsa na dama, tare da zaro bindigarsa da hannunsa na hagu, ya ɗorata a kan matashin. Yaron dake tsaye a bayan matashin ya fiddo da tasa bindigar ya nuna Raja da ita, yayin da mutanen Rajan ma suka fiddo da tasu bingidar. Matashin ya shiga ƙoƙarin motsa bakinsa cike da tsoro. “Shhhhh!” Rajan ya faɗi yana ɗauke bindigar daga kan matashin, tare da ɗora bindigar a bakinsa, alamun ya masa shiru. “Ba na san jayyayya!......” Ya ƙarshe yana maido da bindigar kan matashin, cike da tsoro matashin ya gyaɗa kansa, sannan ya yi wa mutuminsa alama da ya basu kayan. Da sauri mutumin ya juya cikin motarsu ya buɗeta, sannan ya ɗuko wani brief case, ya danƙa a hannun macan nan, ita kuma macen ta miƙawa ɗaya daga cikun mazan dake tsaye a bayata. Kuma har zuwa lokacin Raja na riƙe da kwalar matshin nan, sannan bindigar Rajan sete a gosbinsa. Sai da mutumin su Rajan ya buɗe brief case ɗin, ya tabbatar musu da sahihancin abin da ke cikin brief case ɗin, sannan Raja ya saki matashin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya maida bindigar bayansa, yana kallon matashin da shanyyayun idanuwansa, hannunsa ya kai yana gyarawa matshin kwalar rigar jikinsa. Da farko saida matshin ya razana, ya ɗauka cewar wuya zai shaƙe masa. Kuma har lokacin cike da tsoro yake kallonsa. “You are such a good boy, ka kyauta, da ka yi abinda na ce” Kuma daga haka ya juya. Da hannu ya yi wa yaransa alama da su shiga mota. Har motar tasu ta bar wurin matashin na tsaye a wurin yana kallonsu, a ransa yake hasaso irin masifar da ogansa zai masa idan har yasan cewa ya basu kayan ba tare da sun bashi kuɗi ba. *Unguwar Karkasara....* *12:30am* “Da kyau Raja!” Cewar Garuje, wanda yake shugaba a wurin Rajan, yana faɗin hakan tare da bubbuga kafaɗar Rajan. Bayan da ya duba kayan da ya aikasu su karɓo masa. Raja ya yi murmushi yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Ka ga yanzu nan muka gama waya da me gida, yana ta tambayata akan kayan....” Garujen ya kuma faɗa. Kuma yanzun ma Rajan bai ce masa komai ba, sai juyawa da ya yi ya kalli yaransa huɗu dake tsaye a bayansa,Rhoda, ta hannun damansa kenan, sai Zuzu, Alandi da kuma Jagwado. Sannan ya juyo ya kalli Garuje, a hankali cikin nutsuwarsa wannan kamillaliyar muryar tasa tace. “Kai ma ka sanni ai” “Ai dole ne ma na sa me gida ya maka kyauta, sbd wannan ƙwazon da ka nuna” Lumsassun idanuwansa na ci gaba da kallon Garuje, yayinda ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. *No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja* KULIYA POV. Har zuwa yanzu a idonsa yana ganin abinda ya faru a ɗazu, ɗazun da ya buɗe ƙofar kai tsaye wuta ya buɗe musu. Bai ankara ba ashe wani daga cikinsu yana riƙe da bindiga, kuma shi ne ya yi yunƙurin harbinsa. Sai de cikin ikon Allah sai ya bashi damar kaucewa, bullet ɗin ya samu bango. Kuma bayan ya juya ta kalli bangon da bullet ɗi ya fasa, juyowa ya yi ya kalli yaron da hannunsa ke karkarwa, kuma bai jira komai ba, ya riƙe gaban rigar yaron, ya shiga dukansa da hannunsa, har saida yaransa suka shigo sannan suka raba shi da shi...... “Yau ma halin aka sake?....” Muryar Wata dattijuwar mata ta dawo da shi zahiri. Hannunsa na dama ya sauƙe daga kan bakinsa, kafin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Bai cewa matar komai ba, har ta samu wuri ta zauna kusa da shi, matar ta ci gaba da kallonsa tana nazarinsa. Kamar kullum, kamar yanda ya taso a wurinta, kamar yadda ta rene shi, sanye yake cikin baƙaƙen kaya, wasu jogger set ne sanye a jikin nasa, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin rigar. Idonta ya sauƙa a kan hannunsa na dama, rauni ta gani, kuma da ma ɗazu tun da taga labarai, ta ji an sanar da cewa hukumar DSS sun yi kame a wani gida, har sun kashe mutum ɗaya, ta tabbatar da shi a cikin aikin. Dan yanda tasan Kuliya, haka ta san yunwar cikinta, bata jin akwai wani da zai faɗa mafa halayensa. Hannun nasa ya farfashe daga kan yatsunsa, alamun dai ya daki wani abun da shi. Kanta ta girgiza sannan ta miƙe ta bar falon. Jim kaɗan sai gata ta dawo, hannunta riƙe da plate ɗin abinci, sanna firstaid box. A kan coffe table ta aje masa abincin, sannan ta ɗauki firstaid box ɗin ta ɗora akan cinyarta kafin ta buɗe. Hannun nasa na dama ta kama sannan ta shiga shafa masa maganin zafi a wurin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana kallonta. A duk sanda Anna zata nuna masa kulawa, idan ya kalleta sai ya ga fuskarta na rikiɗewa tana koma irin tata. Mahaifiyarsa, mahaifiyarsa da a duk sanda zai tuna da ita sai ya tuna da mahaɗinsa, ɗan uwansa, abokin tagwaitakarsa, Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya ƙara sunansa a gaban nasa sunan, sai dai kuma idan ya ci gaba da san zurfafa a cikin tunanin LABARINSU na baya zuciyarsa ƙuna take, wani abu ne ke maƙale masa a wuya, shi bai faɗa cikinsa ba shi bai fito daga bakinsa ba. “Ga abinci ka ci” Anna ta faɗi a sanda ta gama shafa masa maganin,tana miƙa masa plate ɗin. Yanda yake kaiwa lomar abincin ne kawai ya shaida mata da kalar yunwar da yake ji, bisa ga dukkan alamu ko da aka yi buɗa baki bai ci abinci bw. Masifar zurfin cikinsa da miskilancinsa da kuma taurin kansa shi ne ke haɗata faɗa da shi, dan da ace bata kawo masa abincin ba, haka zai ƙaraci zamansa a gidan, har ya tashi ya tafi ba tare da ya ce ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112