Chapter 11
Chapter 11
shekarunta babu iyaye. Ita da ta rasa iyaka mahaifiya ma kawai rayuwarta ta hargitse bare ita da ta rasa duka biyun. Kuma bama wannan ba, ba ma ta sansu ba, bata taɓa ganin ko ɗaya daga cikinsu ba. “Ke Rabi? Tashi ki zo ki soya mana doyar nan!” Muryar Habiba ta dawo da ita zahiri, a hankali dubanta ya kai kan Habiban dake tsaye a kansu. “Umma ki bari mana na ƙarasa mata, saura guda biyu fa....” “Ban yi niyya ba, yanzu nake so ta tashi ta min aiki na....” Ba tare da Rabi'a tace komai ba, ta shiga ƙoƙarin jan doguwar kalbar dake riƙe a hannun Saratu dan ta miƙe, amma sai Saratun ta mayar da ita ta zaunar. “Gaskiya Umma ba kya kautawa, Wallahi wannan ba adalci ba ne, yarinyar nan ta je ta yini tana aikin bautar da ba ita take cin kuɗinta ba, dan ke take kawowa, sannan ta dawo ta yi aikin gidan nan, kuma yanzu ta samu ana ɗan mata kalbar da za ta yi adon salla sai ki ce baza'a mata ba ?!” Habiba ta ɗan sunkuyo tana miƙowa Saratu bayanta. “Da ke ni mama Saratu, na ce inji didim!, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci....” Ta miƙe tana ci gaba da faɗin. “Na taɓo uw*r ki Rabi ko?, To baki isa ba, dole sai ta tashi ta soya doyar nan!....” Kafin Saratu ta sake cewa wani abu, Rabi ta yi wuf ta miƙe tsaye, tana ƙoƙarin ɗaure kanta da ɗankwali. Gashin kanta da tsayinsa ya ragu a yanzu ya kwanta luf a gadin bayanta, har yana reto. “Gaskiya Umma na gaji!, Wallahi na gaji da abinda kikewa yarinyar nan a cikin gidan, ita ma fa 'ya ce, kuma ko baabaarta bata raye hakan ba ya nufin a cusguna mata. Umma kema uwar 'ya'ya mata ce, wata rana gidan wani za muje. Na tabbatar da idan uwar miji ko 'yan uwansa suka mana haka ba za ki ji daɗi ba. To ita ma kamar haka ne, tana da dangi bayan mu. Dan tsabar san zuciya irin naki yau shekarar yarinyar nan biyar a gidan nan, amma kin hanata ta je ta ga dangin mahaifiyarta, dan kar ta je ta faɗi irin azabar da ake bata a cikin gidan nan su hanata dawowa ki rasa baiwa. Wallahi Umma wannan ba adalci ba ne, ke ba kya tunanin wata ƙila wannan abun da kike shi ne ya zama sannadiyyar tagayyarar mu?, Ita 'yar taki ta fari, bata jin daɗin aurenta, sannan ni, shekaruna 27, amma na rasa mijin aure, ko sau ɗaya saurayi bai taɓa zuwa ƙofar gidanan yace yana sallama da ni ba, ga kuma Mama, wadda ta lalace da bin maza!.....” “Ya ishe ni haka Saratu, ki rufa min baki ko na make ki a wurin!” Saratu ta share guntuwar ƙwallar da ta zubo mata ta buɗe labulen ɗakinsu ta shige ciki. Rabi'a da ke kiciniyar hura wuta ma ta share tata ƙwallar, saboda tunawa da ta yi da dangin Ummanta, ta tuna yanda suke matuƙarsanta da 'yar uwarta, sai kuma tunanin Anti Saratun, Allah ya sani kuma ita ma ta sani, ba ƙaramin cutuwa baiwar Allahn nan take da zaman gidan. Kuma ta san cewa Anti Saratun na matuƙar san aure, dan tasha kamata tana kuka, kan abun da ke damun rayuwarta, sai dai ta zauna ta bata baki har ta samu ta yi shiru. *DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja* *10:30am* KULIYA POV. “Aliyu Zaid Bichi!” Cewar shubansa, yayin da yake tsaye a gaban shugaban, ya ƙame cike da girmamawa. Wani murmushi kwance a fuskar ogan. Kuma cikin abinda bai wuce sakan biyu ba, wannan murmushin ya sauya zuwa ɓacin rai ma bayyani. “Kai wai me yasa ba zaka taɓa sauyawa ba?, yanzu saboda shashancin da ka yi, ɗaya daha cikin criminal ɗin ya mutu, kai kwata-kwata baka iya controlling fishinka ne ?!” Kuliya ya ƙara ƙamewa yana kallon wani wurin da ban, dan da ma yasan hakan sai ta faru, ba ma yasan ya kalli fuskar ogan, dan idan har ya kalleta, zai iya hasaso kansa yana marin shugaban nasa, kuma wata ƙika ma hasashen ya zama gaskiya. Dan baya san a ɗaga masa murya, daga an ɗaga masa murya yake kai hannu, shi kansa yasan cewa zuciyarsa a kusa da take, abu kaɗan ne ke tunzura shi. Ya ɗaga kafaɗarasa yana ci gaba da kallon wani hoto dake aje a bayan ogan nasa. “A haka kake san zama kamar Lion ɗin ?...... Shi Lion ɗin da kake san zama sam ba haka yake ba, cikin basira da taka tsan-tsan yake gudanar da aikinsa, ba shi da saurin fusata kamar kai, ba shi da saurin kai hannu kamar kai!....” Lion?!, wani suna guda ɗaya da yake ƙwarara masa gwiwa a kan aikinsa, wani sunan da ko jinsa ya yi sai ya ji jinin jikinsa na tafasa. Kuma ba shi kaɗai ne sunan Lion ke bawa ƙwarin gwiwa ba. Kusan duka ma'aikatan DSS sun san sunan Lion, dan abu ne mayuwaci, ka je training ɗin DSS ba tare da an baka maka tarihi da kuma sunan Lion ba. Duk wani jarumi da mai hazaƙa a hukumar burinsa kawai ya zama kamar Lion. Sai dai kuma duk da wannan nasara da kuma jarumta irin ta Lion ɗin, in ka ɗauke manyan hukumar tasu, babu wanda yasan kammanin fuskarsa, sunan nasa kawai ake ji, sai kuma ƙwazon da yake a aikin nasa, sunan nasa ma ba na ainahin kowa ya sani ba. Code name ɗinsa kawai suka sani. Amma duk da haka yana burge kowa, dan duk wanda zai gwada wata jarumta da kuma san nuna role model ɗinsa sunan Lion za ka ji ya kira. “Sam shi Lion ɗin ba haka yake ba....” Muryar Ogan nasa me amsa sunan Chidera Kingsly ta katse masa hanzari. “Lion yana da basiri, he is so intelligent, amd smart, ya san aikinsa, baya komai cikin fushi, cikin nustuwa da tunani yake gudanar da aikinsa.....” Kuliya ya sauƙe kansa ya ɗora manyan idanuwansa a kan fuskar shugaban nasa. Kuma har zuwa lokacin bai ce komai ba, dan tun bayan gaida shi da ya yi a sanda ya shigo office ɗin, bai ƙara cewa komai ba. Kuma shima Chideran yasan cewa ba lalle ya sake cewa komai ɗin ba, dan kowa yasan miskilancin bawan Allahn nan. “Na san cewa yanzu haka ka rayawa ranka cewar; ka dalle min fuskata da mari!” Wani abu me kama da murmushi ya faru a cikin zuciyar Kuliya, dan ya canka dai-dai, hasasowa kansa yake yayin da yake kashe sauraye a kan fuskar chideran, dan ba sauro ɗaya ba. * “Ehemm!” Muryar Kuliya ta yi gyaran murya, alamun ya bawa wanda yake buga ƙofar izinin shiga, dan wannan ɗabi'arsa ce. Kusan duk wanda yake headquarter ɗin yasan da hakan. Shi a ganinsa magana ma wani kayan gabar ne, amma idan masifarsa ta tashi yafi ub*n kowa iya ɗaga murya. Zaune yake a office ɗinsa, yayin da yake daddana system. Kamar kullum; sanye yake da baƙaƙen kaya, wata baƙar suit ce a jikinsa. Hatta da long sleeve oxford shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin baƙa ce. Ƙofar office ɗin ta iyo ciki, alamun dai wanda yake bayan ƙofar yana shirin shigowa. Suffar Abubakar ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112