Chapter 38
Chapter 38
zo tana ta ya shi yin hidindumun azimin, kuma duk sallah sai ta masa sabon ɗinki. Kamar yanda take tafiya da shi can Enugu garinsu idan Christmas ta zo, kuma hatta da 'yan uwanta na can ba sa nuna masa ƙyama, sannan ko da sau ɗaya ba ta taɓa masa tayin shiga addininsu ba, shi ma kuma bai taɓa musu ba, dan ya ga kamar idan ya musu ma bazasu karɓa ba. Rayuwarsa ta ci gaba da wanzuwa a haka, cikin farin ciki da samun nasarori, kafin giftawar wata ƙaddara, wadda ta tarwatsa komai na rayuwarsu shi da Rhoda, ta yi fata-fata da jin daɗinsu!, Ƙaddarar ta hargitsa komai!. *Present day...* RABI'A POV. Da sassafe ta farka kamar kullum, sai da ta yi sallah, sannan ta gyara alkama, ta kai niƙa, ta ɗauko niƙan, sannan ta haɗawa Habiba kayan suyar funkasonta kamar yanda ta saba. Kana ta share gidan tas, sannan ta shiga wanka, a lokacin da ta fito har masu siyan funkaso sun fara taruwa a gidan, don Habiban da kanta take soyawa, tun da yau akwai makaranta. Ɗakinsu ta shiga, ta saka kayanta, ta ɗan shafa mai, sannan ta yi wa Anti Saratu sallama, ta fita. Yau ta yi mamaki sosai ganin har kusan kwana uku kenan ba ta ganin Mishal a makarantar, ita kuma ba ta santa da wata ƙawa ba bare ta tambayeta, wannan baturiyar ma da ta saba ganinsu tare ba ta san inda za ta sameta ba. Hakan yasa tunanika sukai mata yawa, ta shiga saƙe-saƙe kala-kala, har zuwa lokacin da aka tashi. Kuma kamar yanda zuciyarta ta raya mata, kamar yanda ta saba ganinsa. Tana fita idanuwanta suka sauƙa a kansa, jingine jikin gate ɗin estate ɗinsu, sanye cikin wasu ash jogger set. Hannayensa sanye cikin aljihun hoodie ɗin kayan, sai dai saɓanin kullum, yau ba shi kaɗai ba ne, shi da wannan budurwar ne, wadda ya kira da ƙanwarsa, sanye take ita ma cikin irin kayan jikinsa, hatta da takalmansu iri ɗaya ne. Kamar yanda suka saba a kwannakin hannu ta ɗaga masa, hakan yasa Rhoda ta juya ta kalleshi, sannan ta kalli Rabi'an. Bisa ga mamakinta sai ta ga Rajan ya sha mur, ya na bin bayan Rabi'a wadda ta fara tafiya, sai kawai ta yi murmushi ita ma ta bi bayansu. “Me ya same ki yau ?” Raja ya tambaya, ganin yanayinta ba kamar yanda ya saba ganin ba, Rabi'a ta ɗago ta kalleshi, sannan ta kalli Rhoda dake biye da su, ganin hakan yasa Rhodan ta ɗauke kanta sama tana fito, sannan ta ƙara da. “Ni fa ba na jin komai...” Raja ya tsaya, sannan ya waiga ya kalleta. “Da ma biyoni kika yi ?” Ta girgiza kanta. “A'a fa, ni saƙo zan je na karɓo a nan bakin titi” Raja ya finciko hannunta yana kama kanta ya matse, hakan yasa ta saki ƙara. Duk abun da suke Rabi tsaye a gefe tana kallonsu. Sai kuma ya dafa Rhodan, sannan ya yi wa Rabi alama da su ci gaba da tafiya. Tafiyar suka ci gaba da yi, Raja na dafe da kafaɗar Rhoda. Ya ɗaga kafaɗarsa sannan yace. “Baki amsa ni ba Ammata” Ko kafin ta ba shi amsar Rhoda ta yi wuf tace. “Ammata?, What a wonderful name!” Raja ya kama kunnenta ya murɗe, hakan yasa ta saka ƙarar azaba. “Raja mana!” Ta faɗi a shagwaɓe. “Ammata manta da wannan yarinyar, neman magana take” Sai faɗan nasu ya bawa Rabi dariya. “Kwana biyu kenan wata ƙanwata ba ta zo ba shi yasani a damuwa!” “Gidan ku ɗaya ?” Rhoda ta tamabaya daga ɗayan ɓarin, Raja ya ranƙwashi kanta daga sama, kasancewar ya fita tsayi. Ta dafe wurin tana turo baki. Rabi'a kuwa sai murmushi take. “Ki kwantar da hankalinki Ammata, lafiya ita ce ke ɓuya, da yardar Allah tana cikin ƙoshin lafiya” “Kawai ki manta” “Rhoda hoo!” Raja ya faɗi yana ƙara dukan kanta, ta ƙwace kanta, sannan ta koma layin da gudu, tana faɗin: “Kada ki dumu Ammata! She dey fine oo!” Daga Rajan har Rabi'a sai da suka yi dariya. Tafiya sukaci gaba da yi suna 'yar hira, har suka iso bakin titi, kamar kullum haka y tsaidamata ta hau, har suka ƙulewa ganinsa ya na ɗaga mata hannu. Kamar daga sama ya ji muryar Rhoda daga bayansa. “Hooo!, Raja ya kwarewa soyyayar me kama da shi...” Juyawa ya yi ya kalleta, tsaye take a bayansa, kenan dawowa ta yi?. “Ki bari na zo na sameki a nan” Ya yi maganar yana nufar inda take. Rhoda ta fita da gudu tana dariya, shi ma ya bi bayanta yana dariyar, har ya cimmata, kafin ya riƙe kumatunta yana ja. “Ke ba kya jin magana ko?” Rhoda ta dafe wurin da ya ja mata tana kumburo baki. “Ayya mana Zaid, wannan ai mugunta ce ” “Ni ne mugun?” Ya faɗi yana ƙoƙarin ƙara kamata. Ta kuma saka gudu tana dariya. “I'm sorryyyyy!” Ta faɗi tana kama kunnuwanta, a sanda ya kuma cimmata, sai ya dafata kamar ƙawarsa, suka jera suna tafiya. Har suka koma gidansu. *No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.* “Assalamu Alaikum... Karima!” Muryar Anna ta faɗi, yayin da wayarta ke kare a kunneta, bayan da ta aikawa Karima yayar Siyama kira. Daga cikin wayar muryar Karima ta amsa da. “Wa Alaikumu Salamu, Na'am Anna, ya kike, ya gidan ?” “Lafiya ƙalau Karima, ya Siyama da yaran, da kuma me gidanki ?” “Suna lafiya” “To da ma so nake dan Allah ki kira mijin naki ki sanar masa da cewar ina son ganinki, idan xai iya miki lamuni” Karima ta ɗan yi jim, kafin ta amsa da: “Ba damuwa, Insha-Allah zai bari, amma Lafiya kike nemana Anna ?” Anna ta ɗan shafo gefen fuskarta, sannan tace. “Lafiya... Ban faɗa muku ba ne, An ɗaurawa Kuliya aure, kuma yau za mu je mu ɗauko amaryar, su Laraba ma duk na kirasu, dan haka kema sai ko taho...” Tsabar razanar da Karima ta yi sai da ta miƙe tsaye, hannunta kan ƙirjinta wanda ya shiga bugu da sauri. “Aure kuma Anna!, Kuliyan ?!, Shi da wa ?!” Sai da Anna ta ɗan yi shiru, kafin ta amsa mata da. “Wannan ba huruminki ba ne, matar Aliyu kuma idan kin zo za ki ga ko wacece!...” Daga haka ta sauƙe wayar. Ɗazu da safe Kuliya ya zo yace mata kawun su Abubakar yace tun da jiya aka yi bakwai ya zo ya ɗauki matarsa yau. Kuma su yake so su je su ɗaukota. Shi yasa ya zo ya sanar da ita. A lokacin kallonsa kawai ta ci gaba da yi, ganin yanda ya rame, ya yi wani irin baƙi, kamar wanda ya tashi daga jinya. Kafin ta daure ta tambayeshi shirin da ya yi domin bikin. Ya shaida mata da; babu wani abun da ya tanada, kawai a je a ɗauko amaryar, koma miye daga baya sai a yi, ba ta ƙara cewa komai ba, dan wata ƙila a ganinsa hakan ya masa, a irin halin da yake ciki ba ta jin za ta iya tirsasashi kan wani abu da baya so ba. Daga can gidan Anti Karima, Siyama dake kan danning ta nufota a razane, jin ta ambaci aure da kuma suna Kuliyanta. “Anti Karima wai menene?” Cike
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112