Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Rabi'a ta isa garin Kano lafiya, kamar yanda mahaifiyarta ta buƙata ta sauƙa a gidan da ta bata takardunsa, sai dai gidan babu kayan buƙata a cikinsa. Dan haka washe garin ranar da ta sauƙa a garin Kano, ta fita ta je ta yi siyyayar kayan da zata buƙata na amfanin gidan. Bayan ta samu sati biyu a garin, ta shiga fafutikar neman aiki, cikin sa'a ta samu aiki a wata asibiti, kasancewar aikin nurse ta karanta. Haka rayuwarta ta ci gaba da gangarawa ita ɗaya, kullum cikin ƙunci da tunanin gida, Allah ya sani tana kewar gidansu, sai dai kuma ba za ta iya rabuwa da cikin jikinta saboda san gidan da take ba. Sau tari ta kan zauna ta yi tunani a kan rayuwarta, da ma haka duk macen da aka mata fyaɗe ba tare da san ranta ba rayuwarta ke kasan cewa?. Kowa ya na nuna mata ƙyama, saboda kawai Allah ya ɗora mata ƙaddara?. Watan cikin jikinta tara dai-dai, naƙuda ta tashi mata, Allahn da ya temaketa tana asibitin da take aiki a ranar, dan ba ta wani ɗauki hutu ba. Kuma ita kaɗai take rayuwarta, babu ruwanta da kowa a unguwar da take zaune ko a asibitin. Cikin ikon Allah ta sauƙa kafiya, ta samu yaranta 'yan biyu maza. Bayan ta dawo hayyacinta ne ta raɗa musu suna da kanta, na farkon ZAID, na biyun kuma ta saka masa ALIYU. Ba ta yi taron suna ba, dan bata da wanda za ta gayyata, mahaifiyarta kawai ta kira a waya ta faɗa mata. Hatta da Maryam, 'yar uwarta, kuma abokiyar tagwaitakarta, wadda ta fi shaƙuwa da ita fiye da sauran 'yan uwanta bata da masaniya kan inda take. Ita kanta Hajiya A'in taƙi faɗawa kowa inda Rabi'an take ba. Duk da wahala irin ta renon tagwaye, haka Rabi'a ta reni yaranta ita kaɗai. Sosai take nuna musu soyyaya da kuma basu kyakyawar tarbiyya. A koda yaushe tana nuna musu su so juna. Haka yaran nata suka taso masu tsananin kama da juna, banbancinsu a hallita biyu ne, shi Zaid yana da ash ɗin ƙwayar ido, yayin da Aliyu tasa take brown, sai kuma totsiyar karen dake a bakin Zaid, wadda shi Aliyu ba shi da ita. Haka kuma halayensu sun banbanta, dan Zaid yaro ne me sanyin hali, ga haba-haba da jama'a, amma Aliyu mugun muskili ne, babu ruwansa da yawan magana, ga masifa, da saurin fishi. Kuma har suka yi wayo ta saka su a makaranta, a cikinsu babu wanda ya taɓa tambayarata ina mahaifinsu. Ko a makaranta ma da sunan junansu suke amfani, shi Aliyu amfani da Aliyi Zaid, Zaid kuma yana amfani da Zaid Aliyu. Tana ƙara nusar da su cewa ba su da kowa sai junansu. Suna primary 5 ne, Zaid ya taɓa tambayarta ina mahaifinsu. Kuma bata ɓoye musu ba, a lokacin ne ta sanar musu da komai da ya danganci ita kanta da kuma su. Suna da shekara goma sha ɗaya, wata rana sun tafi islamiyya. Rabi'a na kitchen tana girki. Bayan ta gama girkin sai ta manta bata kashe gas ɗin ba. Ta koma ɗakinta ta shiga wanka. Ta ɗau tsawon mintuna a banɗakin. Kafin ta fito, kuma tana fitowar, ta ji ƙauri na tashi, kamar wani abu na ƙonewa, hakan yasa ta fito falo, don ta duba abin da yake faruwa, me za ta gani?. Gaba ɗaya kitchen ɗin ya kama da wuta, kasancewar a falo kitchen ɗin yake. Har ya bawa falon, yana ƙoƙarin kama ɗakuna, a lokacin hankalinta ba ƙaramin ta shi ya yi ba . Ga shi labulayen ƙofar falon sun kama da wuta, babu damar ƙarasawa jikin ƙofar bare ta buɗe. Haka ta dawo ɗakinta ta shiga kai kawo na neman mafita. Bata ankara ba har ɗakin ma ya kama da wutar. Ta shiga kiran mutane domin a kawo mata agaji, sai de babu wanda yake ji, bare a kawo mata agajin, kamar yanda take buƙata. Kuma a lokacin ne, Aliyu da Zaid suka dawo daga makarantar. Tun daga ƙofar falon suka ga wuta na ci, hankalinsu ya tashi sosai, suka shiga kiran sunan mahaifiyar tasu tun da sun san cewar tana cikin gidan. Jin kiran sunanta da suke ne yasa Rabi'a ta shiga amsawa tana kiran sunayensu, bayan gidan suka zagaya, jin muryar mahaifyar tasu na futowa daga can, dai-dai tagar ɗakinta suka tsaya. Kuka suka ci gaba da yi suna faɗin ta fito daga cikin gidan kada wuta ta ƙonata. “Zaid, ku tafi, kada ku tsaya a nan...idan kuka tsaya wutar zata iya ƙona ku... Ku tafi nace!.....”. Fitar suka yi, sannan suka shiga neman wanda zai temaka ya zo ya fitar musu da mahaifiyarsa. Kasantuwar unguwar tasu babu kai kawon mutane da yawa, kuma su ba gidan kowa suke shiga ba, yasa saida suka jima, kafin suka samu wasu maza suka shiga gidan suka ga abinda ke faruwa. Ko da aka kashe wutar har ta gama ƙona ko ina ƙurmus, ta ƙona komai na gidan, ita kanta Rabi'an haka aka fito da ita babu rai a jikinta... *Present day.....* *Unguwar Madallah, Suleja, Niger state* RABI'A POV. _🎶Ramadanal kareem, ramadanal kareem!_ _Watan ramadana, wata mai alfarma......🎶_ A hankali waƙar ke tashi ta cikin radion da Habiba ke sauraro. Zaune take a kan tabarma tana dudduba kayan ɗinkinsu Mama na sallah da aka kawo daga shagon ɗinki, don yau jajiberan sallahr. Mama, Fati da Mahmud sun kewaye da ita, kowa na gwada nasa a jikinsa. Rabi dake zaune daga can bakin murhu tana soya musu kajin da za'ayi miyar sallahr da su sai satar kallon kayan nasu suke. Don Allah ya sani, tana kewar samun sabon kaya, kayan Mama sun fi mata kyau, ta san da cewar kuɗin albashinta na makarantar da take aiki da shi aka musu dinkunan, amma ita da take shan wahalar aikin ko fallen zani na atamafa roba ba'a samu arziƙin siya mata ba. Ta juya kanta tana tsame kajin da suka soyi daga cikin mai. “Salamu alaikum... Rabi wai ki zo in ji Yaya!” Wani yaro me zaƙin baki ya faɗi yana shigowa cikin gidan. Rabi ta juyo ta kalli yaron. Yaya?, wani mutum ɗaya a duniya da yake santa a yanda take. Yake santa duk da ita ba kowa ba ce. Yake nuna mata so duk da ita bata da komai. Kuma ita ma ba za ta yaudari kanta ba, tasan cewa tana sansa, dan ba ta ga wani bayan shi ba, to ina ma za ta samu ?, waye zai so ta a haka ?, ta sani cewar ita ba mummuna ba ce, tana da kyau dai-dai nata, amma ai hausawa ma sun ce idan kana da kyau ka ƙara da wanka. “Je ka ce ba za ta zo ba!” Muryar Habiba ta katse mata tunani, juyawa ta yi suka haɗa ido, a take ta watsa mata wani mugun kallo. Rabi'a ta yi saurin ɗauke kai, wani abu na taruwa a maƙoshinta. “Rabi! Ɗan siyo min kati dan Allah” Muryar Saratu ta faɗa, a sanda ta fito daga ɗaki, sai da Habiba ta harareta sannan tace. “Ba zata je ba, ba ki ga aiki take min ba?” “To tunda ba za ta je ba, Mama ko Fatima wani ya siyo min a cikinsu” “Ba ta ta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112