Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

“To ki sanar mata da ku yi maza-maza ku taho International Hospital, Abubakar ba lafiya!...” Duk rashin hankalinta, da ƙarancin shekarunta a duniya ta san cewa jinya kawai ba za ta saka babban mutum kamar Ammunsu kuka ba, dole akwai wani abu dake faruwa da yayanta mara kyau, kk mutuwa ya yi ?!. RABI'A POV. Kamar yanda ta saba ganinsa jingine jikin gate ɗin estate ɗin nan, yana kallonta da lumsassun idanuwansa. Yau ma haka ɗin ne. A memakwan kullum da ta saba wucewa ba tare da ta masa magana ba, yau sai ta ɗago masa hannu, sannan ta yafito shi. Sai da gaban Raja ya faɗi, ganin yanda ta kira shin, amma sai ya dake, ya fara takawa zuwa gabanta. A lokacin da ita kuma ta hau hanya ta fara tafiya, kamar jiya sai ya fara binta a gefe. “A can kake da zama?” Bayan ɗan wani lokaci ya ji ta tambaya. Sai ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan ya amsa mata da. “Eh, a nan nake da zama” “Wannan ɗayar ƙanwarka ce ?” Ta kuma tambaya, hakan yasa ya kalleta kaɗan, wato jiya shi ya mata tambayoyi, yau kuma ita ce ke masa. Kafaɗarsa ya ɗaga cikin faɗin: “Sunanta Rhoda, kuma ƙanwata ce” Rabi ta gyaɗa kanta tana kallon hanya. “Kai ma Cristian ne ?” Sai da ya ɗan tsaya ya kalleta na 'yan wasu sakkani, sannan ya ci gaba da tafiyar. “Ni musulmi ne” “To miye ma'anar RAJA ?!” Ta tambayi abin da ke mata yawo a ka tsawon lokacin da ya faɗa mata sunansa. Bisa ga mamakinta sai ta ji ya yi murmushi, hakan yasa ta juya ta kalleshi, murmushin kuwa yake, wanda ya ƙara bayyana kamarta da shi. “Raja na nufin Fata, i mean wish, za kuma ki iya kiransa da hope, amma sunana na gaskiya Zaid ne!” Zaid?!, Zaid!?, Zaid?!... Ta maimaita sunan kusan sau biyar a cikin ranta, to Zaid ɗin bai fi ba?, amma ya na wani kiran kansa da Raja. Sai ta tsaya a sanda suka fito bakin titi. Kamar jiya yau ma sai da ya tsaida mata taxi, sannan yace kada a ɗau kowa sai ita. Daga haka ya ɗaga mata hannu, ya koma layin da ya fito. Rabi ta yi murmushi tana kallon hanya. Hirarta da shi na sa ta nishaɗi sosai. *No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja* KULIYA POV. A hankali ya sako ƙafarsa ta dama cikin falon gidan Anna, wadda take zaune a kan kujera tana tsige zogale. Kanta ta ɗaga ta kalleshi. Ba shiri ta miƙe tsaye, hakan yasa trayn zogalen dake kan cinyarta kifewa a ƙasa, zogalen ya zube. Ba komai ya bata tsoro ba, sai ganin yanda idanuwan Kuliyan suka yi ja, fuskar tasa ma ta yi ja, bisa ga dukkan alamu kuka ma ya yi. Suna haɗa ido da ita ya fashe da kuka, ba ƙaramin razana Anna ta yi ba, sanin halin ɗan da ta rena, Kuliya ba ya kuka a kan abu ƙarami, idan har ka ga ya yi kuka, to abun ba ƙarami ba ne, ita za ta iya cewa ma tun ranar da ta dawo da shi Abuja har wa yau bata taɓa ganin kukansa ba. Da sauri ta ƙarsa kusa da shi, kuma tana zuwa kusa da shi ɗin ya rungumeta yana fashewa da kuka. Anna ta ja hannunsa ta zaunar a kan kujera bayan da ya saketa, da gudu ta shiga kitchen ɗinta, ta ɗauko ruwan sanyi ta ba shi. Sannan ta zauna a gefensa tana shafa kansa. “Me ya sameka Aliyu?” Kuliya ya aje gorar ruwan da ya shanye kusan rabinta, sannan ya share hawayensa. Yana kamo hannun Anna. “Ba na faɗa miki cewar yau za mu fita kame ba ?” Ya faɗi cikin wata murya mai rauni, wadda za ta iya cewa sam ba ta san ɗan nata na da ita ba.Da sauri ta gyaɗa masa kai tana shafa kansa. “To a wurin ne... Ɗaya daga cikin 'yan ta'addan ya yi ƙoƙarin harbi na, shi... Shi ne Abubakar abokina, ya ture ni... Shi... Shi kuma harbin ya same shi!” Annan ta gyaɗa kai, dan tasan Abubakar ɗin. “To yanzu me ya samu Abubakar ɗin ?” Ya haɗiye yawu yana share hawaye. “Shi ne muka kai shi asibiti... Bayan an masa tiyata an cire alburushin... Yace a kira masa kawunsa... Ni da kai na... Na kira kawun nasa, na yi masa kwatance, ya zo ya samemu har asibitin...” Ya kai hannu yana share hawaye, sannan ya ci gaba. “To Kawun nasa na zuwa, yace yana so a ɗaurawa ƙanwarsa aure kafin ya rasu... Da kawun nasa ya tambayeshi waye mijin... Sai... Sai yace ni ne, cewa ya yi ni ne Anna!” Ya ƙarashe a raunane. Anna da ta fara fahimtar inda zancen ya dosa, ta share masa hawaye ta na masa alamun ta na jinsa. Sai da ya ja hanci sannan ya ci gaba. “Yanzu haka an ɗaura mana aure da ƙanwar tasa, Anna wani irin so Abubakar yake min?, da har zai iya kasada da rayuwarsa ya ceci tawa, sannan ya aura min ƙanwarsa da yake ganin ita kaɗai ce ta rage masa!” “Kana da zuciya me kyau Aliyu, duk da kana da saurin fusata, ni nasan kana da kyawawan halayen da za'a so a tare da ɗan adam na gari... Yanzu ina Abubakar ɗin?” Annan ta tambaya tana ƙara share masa hawaye, bisa ga mamakinta sai ta ga ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana fashewa da kukan da ya fi na ɗazu, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Anna Abubakar ya mutu!, Muntuna biyar da gama ɗaurin auren ya mutu!, Anna kuma bai mutu ba sai da ya kama hannuna, sannan yace na kula masa da ƙanwarsa, kada na bari ta wahala, Anna ina zan kai wannan nauyin?, Ina zan kai nauyin da ya ɗora min?!” Anna ta rintse ido, a sanda take jin sauƙar hawayensa a kan jikinta, da ƙyar ta daure ta ci gaba da shafa bayansa. “Allah zai temakeka Aliyu, shi kuma Abubakar Allah ya ji ƙansa, ya sa mutuwar ita ce hutu a gareshi, Allah ya baku zaman kafiya da matarka, ya kauda idomln maƙiya daga kanku!...” #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *10* ~~~ *Do something for her that no one has ever done, love her for who she is.* *** *Shekara ta 2000.* “Malam Ila ina kwana” Cewar Zaid yana tsugunnawa har ƙasa, a sanda ya shigo shagon Malam Ila, wanda ke saida kayan provision a 'yar ƙaramar containerrsa. Baki washe Malam Ila ya amsa masa, kafin Zaid ya miƙe ya zauna a kan bencin da Malam Ilan ke kai, suka kuma gaisawa, kafin Malam Ilan ya ba shi abincin da ya siya ya aje masa, kamar yanda suka saba kullum. Don a kwanakin kullum idan ya zo sai ya ba shi abinci, karɓa ya yi sannan ya ci, suna 'yar hira jifa-jifa. Kuma a cikin hirar ne Malam Ilan ya sosawa Zaid inda ke masa ƙai-ƙayi. “Ya kamata ka je ka dubo ƙanin naka, ka ga fa yau kusan satinsa ɗaya a can!” Aliyu ya aje kwanon hannunsa sannan yace. “Ai wai kar su ga gaggawata ne shi yasa, amma ina kewarsa, don ba mu taɓa nisa da juna irin

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112