Chapter 54
Chapter 54
Tsaye take a kitchen tana girka jallof ɗin couscous, fuskarta kawai idan ka kalla za ka gano tsantsar farin cikin da take ciki, don yau da safe da ta tashi ta shiga kitchen ɗin ta tarar da tarin kayan abinci da kayan girki. Allah ya sani, ita ba san wannan abincin restaurant ɗin take ba, shi yasa ba ta ci sosai, don har wata 'yar rama ta yi a kwanakin. Daga ƙasan marbles ɗin kitchen ɗin kuma Ayra ce ke cin kifin da Mishal ɗin ta saka mata. Mishal ta kwashe jallof ɗin tare da zubata a kan wani plate me kyau da ya fi burgeta cikin kayan kitchen ɗin, dai-dai da lokacin da aka turo ƙofar kitchen ɗin. Kallon ƙofar ta yi, duk da ta san cewa shi ne, kamar kullum sanye cikin baƙar suit, yana kallonta a sanyaye, wani abu sabo game da shi. “Ina kwana Abu Aswad!” Ta faɗi a sanda yake shigowa cikin kitchen ɗin, cak Kuliya ya dakata da tafiyar da yake, sannan dubansa ya zarce zuwa kan fuskarta, yayin da take zama a kan kujerar island. Abu Aswad?, shi ɗin ne Abu Aswad?, don kawai ya na saka baƙaƙen kaya, sai ua zama Abu Aswad? Sai ya ƙi tanka mata, saboda wani daddaɗan ƙamshi da ya ziyarci hancinsa, kuma ƙamshin ba na turera ba ne, na girki ne, hakan yasa ya kalli plate ɗin dake gabanta. Sai da ya baɗiyi wani kakkauran yawu a sanda kalolin jallof ɗin gaban nata suka shiga idonsa, kayan lambun da ta ƙawata girkin da shi yasa girkin ɗaukar ido, ga kuma kamshin da girkin ke yi, kenan dai ta iya girkin kamar yadda ta faɗa?, kai ina!, ta ya za ayi ace wannan ta iya girki?, ai sai dai jagwalgwalo, don wata ƙila kyan da ƙamshin ne kawai, a baki ba llale abincin ya yi ɗanɗano me daɗi ba, saboda haka ba zai yi kasadar cin abun da zai zo ya ɓata masa baki ba, ko ma ya ɓata masa ciki, shi da ko abincin daren jiya bai ci ba. Sai ya ƙi amsata ya juya zuwa wajen da ya saba a je kayan haɗa coffeensa, sannan ya haɗa shi a coffee maker, kafin coffeen ya haɗu, ya zaro wayarsa yana daddanawa. “Abu Aswad! Na ga kayan girki, kuma nagode” Sunan ɗazu ta kuma faɗa, hakan ya sa ya ɗago da kansa daga barin kallon wayar ya kalleta, a wannan karon ita ma shi take kallo, me makon ya bata amsa da baki sai ya gyaɗa mata kai. Yana ɗaga kafaɗa. “Ga abinci nan na rage maka. Za ka ci?!” Yawu ya haɗiya a fakaice, ya ɗan saci kallon abincin nata, a kan me zai ci wannan abinci? Zai fiye masa sauƙi ya sha coffeen sa, duk da ransa ya biya abincin, ga ƙamshinsa da ya cika masa hanci. Sai ya daure ya girgiza mata kai alamun a'a. Juyawa ya yi ya kashe coffee maker ɗin, sannan ya fara firfita shi. Mishal ta taɓe baki cikin faɗin. “Ba dole ma mutum ya gamu da ulcer ba, ba tare da ka ci abicin ba ka tashi ka ɗirkawa cikinka baƙin shayi da sassafe, kuma fa ita ciyawar shafin nan, amfanita a jikin mutu shi ne saka digestive system aiki cikin gaggawa... To ka tashi ka sha baƙin shayi ba tare da ka ci abinci ba, me zai faru kenan?!” Kuliya ya aje mug ɗin hannunsa ya na kallonta, wai da shi take?, to ai shi ba ma baƙin shayi yake sha ba, coffee ne. Sai ya ƙi ya kulata, ya shiga shan coffeensa a nutse, har ta gama surutanta ta cinye abincinta ta wanke kwanukan ta ɗauki Ayra ta bar kitchen ɗin shi bai gama shan coffeen ba. Ko da ya fito daga kitchen ɗin a falo ya sameta, zaune kan kujera tana kallo tv. “Sai na dawo” Ya faɗi murya ƙasa-ƙasa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama. Mishal ta miƙe tsaye, hannunta na hagu riƙe da Ayra. “Na raka ka ne?” Ya ɗan ja da baya ya na kallon kayan jikinta, har yanzu pyjamas ne, da alama ko wanka ma ba ta yi ba. “Na gode. Ki kula da kanki” Ya na ƙarashewa ya kama hanyar fita, bakinta ta taɓe tana zama, ai shi ya jiyo. Yinin ranar haka ta ƙarashe shi cikin farin ciki, da rana sakwara da miya ta girka, kuma har me gadin gidan ta zubawa, da daddare kuma ta girka tuwon shimkafa, bayan ta ci, sai ta ɗan yaɓa aikin makaranta, kafin ta kwanta, ita zama cikin kaɗaicin ma sam be dameta ba, don ta saba zama ita kaɗai, bare kuma akwai girki, ga kallo ga kuma Ayra. Mamakinta ɗaya, ta na som sanin dalilin da ya sa ya fita yau, bayan yau ana cikin weekend, kuma har ta kwanta bai dawo ba. *Hotoro, Ring Road, Kano...* “Sai na dawo Mesoma” Cewar Uchechi tana rungume da yayarta, sakin juna suka yi Mesoman na mata murmushi, a satin da ya wuce Uchechi ta riga ta yankewa kanta shawarar tafiya Abuja, kuma ta yarda da za ta yi abun da Mesoman ta ce mata, don ta samu ta cimma burinta a kan Raja. Wato bugar da shi ta hanyar saka masa maganin bacci a cikin abun sha, ta riga ta yankewa kanta hukuncin za ta iya, kuma ba ta jin akwai abun da zai dakatar da ita daga yin hakan. A da ta na tunanin ta ya za ta aikata masa hakan saboda su Rhoda dake tare da shi a koda yaushe, sai kuma ta samo mafitar ɗaukarsa ta bar gidan da shi. Za ta cemasa ya ɗauketa su fita yawo, kuma a wannan yawon da zai kaita za ta samu damar da za ta cimma manufarta a kansa. *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja...* “Nemo min lambar Nimra” Cewar Jadda wadda ke danƙawa Hajjara wayarta, Hajjara ta karɓa tana yatsina fuska, don Allah ya san,i ita Wallahi ta gaji da zama da wannan masiffafiyar tsohuwar, duk ta bi ta isheta, Allah-Allah take ta koma Maiduguri. Zaune suke a falo, daga can gefe kuma Mama Ladi ce ke bawa Daala abinci. “Ga shi. Ta shiga” Ta ƙarashe tana miƙawa Jadda wayar, Jadda ta karɓa tana tsara kalar masifar da zatawa Nimran. “Falmata! Tun muna sheda juna da ke ki saka wanan ɗan yankan kan da ya aurar min jiki ya saketa, Wallahi idan ba haka ba zan ɗau mummunan mataki a kanku daga ke har shi!” Kalamanta na farko kenan, bayan da Nimra ta ɗaga wayar, daga cikin wayar Nimra dake zaune a office ɗinta ta yi murmushi. “Da ma na san mijin Mishal ɗin ne?” “Ko kin san shi ko ba ki sanshi ba wannan be shafe ni ba, abun da na sani kawai shi ne ke ce kika danƙa masa jikata ya tafi da ita, don haka tun muna sheda juna ki nemo mun gidan da ya kaita, in ba haka ba!...” Daga haka ta kashe wayar tana kumfar baki, A fakaice Hajjara ta saci idon Jadda tana watsa mata harara. Jadda ta miƙe tare da nufar hanyar ɗakinta rai a ɓace. “Mtswww!, aikin banza, wai ita a nan me san jikoki, ƙaaaa!” Ta ƙarashe da ƙwafa. * Jadda na sauƙe wayarta, Nimra ta lalubo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112