Skip to content

Chapter 76

Chapter 76

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

na cutu, an cutar da ni, kai ne me girma, kai ne sama da kowa, kai ne sarkin da babu wani me milki irin nasa, Allah kana gani ya Allah! Ya Allah ka bi min haƙƙina!” Cikin gunjin kuka da ƙaraji take furta hakan, ta na yi tana kallon sama, can kuma da takaici ya ciwota ta sa hannunta ta ture kayan da suke kan mirrorn. Sannan ta saki wani ƙaran takaici, ta riƙe kanta tana faɗin. “Me ya sa komai sai ni?, me yasaaaa!” Kuma a dai-dai lokacin aka turo ƙofar banɗakin. RAJA POV. Kamar Kullum, yau ma ya na zaune a gaban gadon Rabi ya na kallonta, yau kwanansa biyar kenan ya na jinyarta, kuma in har ya zauna a wurin nan ba ya tashi sai lokacin sallah, haka Rhoda za ta zo ta yi ta masa mitar ba ya san cin abinci, ko kuma ta kawo masa abincin, amma ba zai ci ba. Wayarsa ce ta yi ƙara, alamun shigowar kira, sai da ta yi ringing kusan sau uku, sannan ya ja dogon tsaki ya na saka hannunsa a aljihu ya zaro wayar. 'Huzaifa' ya gani rubuce kan screen ɗin, sai ya ɗaga kiran ya na dawowa da dubansa kan fuskarta. Huzaifan ne ya masa magana kan ya zo office ya na san ganinsa, ba dan ya so ba haka ya tashi ya je office ɗin. Kuma sun ɗan jima suna tattaunawa kan gwaje-gwajen da ya ce a yiwa Rabi'an, kuma an yi ɗin, sannan result ya yi kyau, babu wata matsala tare da ita, komai nata lafiya ƙalau, matsala ɗaya ce, ita ce wanan doguwar sumar da ta yi, kuma ga shi ba su san takamemen lokacin da za ta farfaɗo ba, duk da ya ji daɗin kyan result ɗin, sai kuma zuciyarsa ta cika fal da tsoron kada ya rasata, tun da sun ce ba su san lokacin da za ta tashi ba. Da waɗanan saƙe-saƙen ya iso ƙofar ɗakin, sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, wani irin bugu zuciyarsa ta yi, a sanda ya kalli kan gadon ya ga wayam, kuma kafin ya yi wani tunani, ya jiyo kukanta haɗe da maganarta a cikin bayi. Tsabar kiɗima bai san sanda ya saki file ɗin hannunsa ba, sannan ya nufi banɗakin da gudu. Kallonsa ta tsaya ta na yi da jajayen idanunwata, waɗanda bai hango komai a ciki ba face ɓacin rai da takaici, bai san me ya da ba, sai ya samu kansa da kasa ƙarasawa cikin bayin. Nan take fuskar Rabi ta rikeɗe zuwa mamaki ma bayyani, wai me ya sa Raja ba zai rabu da ita ba ne, ta ya aka yi ya san inda take?, tukkunna ma ta ya aka yi ta zo asibiti?, kuma ma me yake a nan ɗin?. “Me kake a nan?” Ta tambaya tana ja da baya, a wannan karon da Raja ya saurari muryarta, sai hankalinsa ya dawo jikinsa, ta farka!, Rabi'a ta farka, sai ya shiga takowa cikin banɗakin fuskarsa ɗauke da murmushi, a gefe guda kuma ga hawaye na zubowa daga idonsa. “Ka dakata daga inda kake!” Ta faɗa cikin ƙaraji, ta na nuna shi da ɗan yatsa. Cak, ƙafafun Raja suka tsaya, baki sake yake kallonta. “Kada... Ka ƙara ko da taku ɗaya ne” Still bai ce komai ba, kawai ya tsaya ya na kallon fuskarta. “Ka juya ka fita, ba na san ganinka” Wata iriyar hautsinawa zuciyarsa ta yi a ma'ajinta, bakinsa da zuciyarsa suka shiga rawa a lokaci guda, da ƙyar ya iya faɗin. “Ni... Ni ne fa Ammata...” “Kada ka ƙara kiran sunan!” Ta faɗi a tsawace ta na nuna masa ɗan yatsa, idanunwata sun firfito waje, sannan ta ci gaba. “Ba na san ganinka Zaid, ka fita daga nan, babu abin da ya haɗa hanyata da ta ɗan daba, me kashe mutane! You are a goon Zaid!” Wannan karon muryar tata a raunane ta fito, kuma har zuwa yanzu ƙafafunta rawa suke, ta kasa tsayawa a gu ɗaya, saboda jikinta babu ƙarfi, hatta da maganar da take ƙarfin hali kawai take. “Na yi nadamar saninka da na yi, na yi nadamar barin zuciyata ta fara sanka, na yi nadamar haihuwata ma da aka yi, na yi na damar komai a duniyar nan.... Da ma duka maza halinki ɗaya, baku da kirki, kanku kawai kuka sani, kun fi san kanku a kan komai, in dai za ku samu abu to kowa ma ya rasa, kun fiya san kai da yawa, wani mugu ya lalata rayuwar me sunana, shi ne har ta samu cikinka... Sannan kuma tsabar san kai irin na kakana, shi ne ya koreta daga gidansa, wai don ta ƙi yarda ta zubar da cikin jikinta ba... Daga nan kuma sai babana... Babana ya lalata rayuwar Ummana, yanzu kuma tawa rayuwar ce aka lalata, wasu mugaye ne suka lalata min rayuwa... Me ya sa ma na sanka Raja?, eh? Na ce me ya sa?!” Ta tambaya tana nuna shi da ɗan yatsa, Raja da ya daskare a wurin dan tsabar mamaki ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, abubuwa da dama sun haɗu cikin maganar tata, na farko ta ambaci cewar zuciyarta tana sansa, na biyu kuma yau ita da bakinta take furta cewa shi jininta ne, ita da bakinta ta furta masa labarin mahaifiyarsu da shi kansa bai sani ba. “Ka fita daga nan, idan zai iyu ka fita daga rayuwata!” Ta faɗi tana nuna masa hanya cikin kuka, a memakon Rajan ya fita kamar yadda ta buƙata, sai ya ci gaba da takowa zuwa gabanta, kuma kafin ta yi wani yunƙuri ya haɗata da jikinsa, ya rungumeta sosai ya na sauƙe ajiyar zuciya. Rabi'a ta saki wani sabon kuka, don da ma abun da take buƙata a irin wannan lokacin kenan, ta na buƙatar wani a kusa da ita, tana buƙatar jin ɗumin wani a jikinta, ta na san ta samu kafaɗar da za ta kwantar da kanta ta rera kukanta yanda take so. Don haka ta ɗago da hannayenta ta kewayasu ta bayansa ta ƙara ƙanƙameshi tana sakin kukan cikin 'yancinsa. Raja ya ja hancinsa ya na ɗaga kansa sama, tare da ƙara riƙe Rabi a cikin jikinsa da kyau. Sai dai kuma cikin sakan ɗaya... Biyu... Uku... *Unguwar Madallah, Suleja, Niger State* A hankali motar Raja ta tsaya a bakin lungun su Rabi, daga cikin motar shi ne zaune a mazaunin driver, yayin da ita kuma Rabin ke zaune a gefensa. Sanye take cikin wata blue abaya, wadda Rahoda ta kawo mata ɗazu, ta yafa mayafin abayar a kanta, har zuwa gefen fuskarta na hagu da ta ɗan rufe gun ya kan nan. A jiya da take cikin jikin Raja tana kuka, ta manta ma da wa take tare, ta manta a cikin jikin wa take, sai a sakan na uku da aka turo ƙofar bayin, a lokacin kuma hankalinta ya dawo jikinta, ta yi saurin sakin Raja ta na tureshi baya, sannan ta zuba idonta a bakin ƙofar bayin, inda Rhoda ke tsaye ta na kallonsu. Kuma bayan faruwar hakan Rajan bai ƙara minti ɗaya a wurin ba ya fice, da Rhodan suka zauna har ta temaka mata ta yi wanka, ta ɗauro alwala ta zo ta shiga biyan sallollin da ake binta, duk

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112