Chapter 48
Chapter 48
na ji daɗin shawarar nan taki Rabi... Sam ni tunanin hakan bai zo cikin raina ba” Rabi ta ɗan yi murmushi. Ta na so ta ga an yi wannan auren, ko ita ba ta fita daga rayuwar ƙuncin gidansu ba, wata ƙila ita anti saratun za ta fita daga rayuwar ƙuncin gudan. Kusan sati biyu kenan da tafiyar Mama, duk wanda ya tambayesu ina Mama sai Habiba ta yi wuff ta ce wai ta tafi ziyara. Hira suka ɗan yi kafin Rabi'an ta fara jin bacci, hakan yasa ta yiwa Anti Saratu sallama ta koma kan tata katifar ta shimfiɗe, sai dai kafin ta gama addu'ar baccin da ta saba yi, waɗanan fuskokin guda biyu masu kama da tata da kuma ta Umma suka gifta ta cikin idonta. Hakan yasa ta buɗe idon nata, tana shafa addu'ar da ta ida, ba ta san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce mata ba, tunawa da ta yi da shi, wannan innocent voice ɗin, waɗanan drunken eyes ɗin, wannan nitsataiyar tafiyar da ma yanda yake ɗaga kafaɗarsa bayan shuɗewar duk wani ƙaramin lokaci. Wai me kike shirin yi ne Rabi?, kar fa ki zarme da yawa, don ya na kama da ke ya sa kar ya sa ki dauka cewar shi sa'an ki ne!, Raj sam ba sa'an ki ba ne, kamar da kuke ba ita za ta sa ku dace ba, dacewa da ban kamanni ma da ban!. Yayan da kika samu shi ne dai-dai ke, kar kuma ki shiga shirin ɓallowa kanki ruwa!. Wani yanki na zuciyarta ya ba ta wannan shawarar, kuma ta yarda da shi ɗari bisa ɗari, don da alama zuciyar tata na shirin sakata ɗaukar dala ba gammo, don kuwa sam babu haɗin zuma da maɗaci, Raja ba sa'anta ba ne ita ma ta sani. Saboda haka duk wani abu da za ta bari ya shiga tsakaninsu yaudarar kanta za ta yi. RAJA POV. Cike da mamaki suke kallon ire-iren muggan makaman da mutumin da Alhaji Bala ya haɗusu da shi ya turo musu wai su zaɓi wanda suke so, daga Raja har Rhoda babu wanda bai saba riƙe makami ba, amma kalar waɗanan makaman ko jami'an tsaron Nigeria ba su da irinsu. “Zaid this thing is getting worst!” Rhoda ta faɗi, mamaki kwance a kan fuskarta. Raja be iya amsa mata ba, kansa kawai yake girgiza wa. Mamakin abun da yake gani ya hana shi cewa komai. “Raja we have to do something about this” Yanzunma kansa ya girgiza mata yana ɗaga kafaɗa, shi ji yake kamar an sakawa bak8nsa wani shirgegen kwaɗo an kulle. Lalle Alhaji Bala ya wuce yanda suke tsammani, abun nasa ma ya wuce hankali, ko da wasa ba su taɓa tunanin cewa ya kai haka ƙarfi a harkar tasa ba. Kallon hotunan kawai yake yana ƙarawa, ya rasa wanne daga cikin hotunan zai nazarta. Ture ko wani tunani ya yi, dan yasan zuwa yanzu lokacin tashinsu ya kusa, hakan ta sa ya rufe laptop ɗin, dan ba ya so ko da wasa ya yi missing ganinta. Rhoda ta bi shi da kallo a sanda ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa. “Wait for me Abeg” Rhodan ta faɗi tana miƙewa, tare da bin bayansa, dan so take ta je ta yi neman tsokanar da ta saba. *Brickhall school, Kaura District, Abuja.* MISHAL POV. A karo na barkatai, Rabi'a ta kuma ɗaga jerseyn da Mishal ta kawo mata, ta juya rigar a hannunta ya fi sau abun da ya fi. Yau gaba ɗaya ba su haɗu ba sai yanzu, kasancewar yau ita Rabin har ɓangaren hostel ɗin mata ta je yin shara, kasantuwar makarantar a haɗe take da boding. Wadda ta saba yi ma 'yan hostel ɗin shara ce ba ta nan, hakan yasa aka turata ta je ta yi. Kuma ta na gama sharar hostel ɗin ta ɗora da ta makarantar, hakan ta sa ba su haɗu ba sai yanzu da aka tashi, ba wai iyaka jerseyn ta kawo mata ba, akwai wani baƙin baby hijab, da leggins, da kuma short ɗin jersyn, sai wani farin canvas. Mishal ɗin ta faɗawa Rabi'a cewa Akinta ne ya siya mata mata kayan saboda da farko cewa ta yi ɓangaren ball za ta zaɓa a sport, amma bayan ta ga cewa ana koyar da kungu fu a makarantar sai ta sauya ra'ayi, hakan yasa ta aje kayan, yanzu kuma da ta ji cewar yayarta na son buga ball sai ta kawo mata su. “Ki na ji ko?, gobe ki saka su, ina san na ga irin wasan da kike” Cewar Mishal tana zuge zip ɗin jakarta, Rabi ta kalleta da mamaki. “Na sa kuma?, da wa zan buga ball ɗin?” Mishal ta yi dariya tana saɓa backpack ɗinta a baya. “Akwai matan da suke buga ball a makarantar nan... Da su nake so ku buga” Ido waje Rabi take duban Mishal. “Ni zan buga wasa da su?” Ta tambaya tana hango waɗanan marasa mutuncin 'yan matan dake yawan buga ball a filin. “Seesee kin iya ball ko ba ki iya ba?” Mishal ta tambaya. Rabi'a ta sunkuyar da kanta tana faɗin. “Na faɗa miki cewar I can't recall when last na buga ball, amma na san na iya, kuma a yanzu ma zan iya buga ball” “To me yasa kike jin tsoro?, na san tsoron su Precious kike, kisa a ranki cewar su ba su isa komai ba, kuna na san cewa kina ganin saboda ke ba 'yar makaranta ba ce shi ya sa ba za ki iya bugawa da su ba, ki barni da wannan, nasan yanda zan yi da su” Rabi'a ta ci gaba da kallonta, kafin ta rungume ƙanwar tata da take jinta kamar ƙanwarta ta jini. “Na gode sosai ƙanwata” “Don't mention it Seesee” Daga haka suka yi sallama, Rabi'a ta fita daga makarantar, kasancewar har zuwa lokacin Kuliya be zo ɗaukan Mishal ba, ya sa ta samu bencin me gadin makarnatar taeu ta zauna kusa da shi, za ta iya cewa for the very first ita ce yau ke jiran a zo a ɗauketa, kullum kafin ta fito Malam Ali ya riga ya zo, shi ma Kuliyan ya mata hakan na kwana ukun da suka wuce, amma yau sai ga shi ya makara. Kamar yanda aka saba Rabi'a na fita ta haɗu da shi, to yau ba ma shi kaɗai ba ne, ya na tare da Rhoda, wadda zuwa yanzu suka ɗinke ita da Rabi'a, don sosai suke hira idan sun haɗu. “Menene wannan Ammata?” Raja ya tambaya a sanda suka jera su ukun suna tafiya, Rabi ta kalli ledar hannunta da yake magana a kai. “Jersyna ce a ciki” “Kin iya ball ne?” Rhoda ta tambaya ido waje, Rabi ta gyaɗa mata kai. “Wow?, da ma a arewa akwai matan da suka iya ball?” Raja ya ranƙwashi kanta, ta yi sauri ta dafe tana sosa wurin. “Me kika mayar da matan arewan ne?, ko da yake ai ke ma a arewan aka haifeki, don haka ba ki isa kin ce wani abu a kansu ba” “To ai ban ce komai ba... Kawai dai ina mamakin abun ne” “Wannan kuma ke kika jiyo” Rabi ta yi dariya kamar yanda ta saba musu idan suna faɗa irin haka. “Wani club
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112