Skip to content

Chapter 103

Chapter 103

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ta koma kamarwata wadda sanyi ya taɓawa ƙwaƙwalwa. “Kana ji ko?!” Ta tambaya tana mammarin gefen fuskarsa, idonsa da ya lumshe ya buɗe a kanta. “Kar ka mutu baka haɗu da Zaid ba!...” Kuliya ya ja wani kalar numfashi yana buɗe idonsa da ƙyar, cikin wani irin sauti yace. “A... Ina... Ki... Ki ka san... Za... Zaid?” Ba dan babu sautin komai a ɗakin ba, da balalle ta ji abun da yake faɗi ba. “Yau Anti Adawiyya ta zo makaranta ta same ni, shi ne take faɗamin cewar Zaid ne mijinta, kuma... Kuma da ma ina ganinsa a layin makaranta” Kansa ya kawar gefe yana ƙoƙarin ƙwato numfashinsa da ya nufi wata duniyar. “Zaid ya gudu... Gu... Guduwa aka ce ya y... yi” Da sauri Mishal ta share hawayenta, hakan ya sa gefen fuskarta ɓaci da jinsa. Ta gyara zama ta shiga ba shi labarin da ta sani a kan Zaid ɗin. Duk kuwa da ba ta da tabbacin yana fahimta. Sai de kuma yana fahimtar, dan babu abu ɗaya da ta faɗa wanda bai samu mukkulin kansa ya buɗe ƙofa ya shiga ba, ya ji komai, kuma ya haddace komai. Kallonta yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa gaba ɗaya. “Hafsat! Ballale... Na... Na kai gobe ba... Amma idan... Idan kin haɗu... Haɗu da Zaid, ki ce... Ki ce masa ina kewarsa... Sa... Sannan... Sannan kuma ba duk tswon wannan lokacin, ban manta da shi ba... Ki kuma faɗa masa cewar... Cewar ke matata ce, ya kula min dake!” Mishal ta ƙarawa kukanta sauti tana kamo hannunsa. “Aliyu Dan Allah ka dena faɗin haka... Na rantse za ka rayu, Allah na tare da mu... Yanzu Aliyu idan ka mutu ina zan sa kain?... Aliyu ba ni fa da kowa sai kai. Kai ne kawai ka rage min, dan Allah kai ma ka zauna, kar ka mutu ka barni kamar Babana da Mamana da kuma yayana, a ƙalla de ya kamata ace na samu ko da mutum ɗaya ne a cikinku!” Tausayinta ya ƙara kama raunanniyar zuciyar Kuliya, hakan ya sa shi ɗagowa da hannunsa na hagu dake ɓace da jini, ya kama gefen fuskarta, hannun nasa gaba ɗaya karkarwa yake, hawaye na fita daga idonsa, wanda ya haɗe da zufar da yake. Matsowa ya yi da fuskarta dab da tasa, har tana iya jiyo yanda numfashisa ke fita a gurɓace, saboda hancinta da ya kara da nasa, hakan ya sa Mishal lumshe ido tana buɗe wani sabon babin na kuka. “Idan na mutu kar ki yi kuka, na san ma Zaid ba zai bari ki yi kukan ba, amma zan yi kewarki, Allah ya haɗani da ke a aljanna!...” Da sauri Mishal ta kai hannayenta kan fuskarsa tana girgiza masa kai. “Dan Allah kar ka tafi... Allah ina sonka... Wallahi ina sonka” Cikin wani irin ƙarfin hali ya mata murmushi. Da gaske yake faɗa mata cewar ba ya jin zai iya kaiwa safiyar gobe, ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa da ita, haka kuma ba ya jin zai ƙara buɗar idonsa ya ganta kusa da shi. Wasiyya ce yake bata, dan wata ƙila bai sani ba, ko wanna ne kaɗai lokacin da Allah ya ara masa dan ya yi magana da ita ta ƙarshe. “Silly girl... Ki me... Me da hankali kan karatunki, ki zama yarinyar kirki, idan kuma Allah ya sa akwai rabo tsakanina da ke, Allah ya raya mana shi, dan ina zaton kamar na baki baby shekaran jiya, ki kula da shi pleace” Duk da halin da yake ciki sai da ya bawa Mishal haushi, ana ga yaƙi shi ya na ga ƙura, ɗan ƙaramin mari ta masa a kuncinsa, hakan ya sa ya buɗe idonsa da ya lumshe. “I love you Teddy Bear... Mishallyn Aliyu...!” Da sauri ta haɗe bakinta da nasa ta shiga kissing. Kafin a hankali ta saki bakinsa tan kallon idonsa. “I love youuuuu too Abu Aswad!” Murmushi ya mata, yana ɗaga hannunsa ya shafa kanta. Nan take kuma jikinsa ya saki, hannun nasa ya dawo ƙasa yaraf, fuskarsa dake hannunta ta ƙara nauyi, idonsa ya rufe ruf. Daga can wajen gidan kuma, bayan da 'yan ta'addan da suka zo ɗaukar fansa suka gama dube-dubensu a cikin gidan ba su ga kowa ba, sai suka yanke shawarar kiran ogansu dan su sanar masa da su fa basu ga kowa ba. Ogan yace su bar gidan kawai tun da har sun ce sun harbe shi, ko haka ma suka barshi ai shikenan, sun ɗau fansar abin da ya musu, na kama babban ogansu da ya yi. ZAID POV. Da misalin ƙarfe 12:40am, ya fice daga gidansa, yayin da ya bar Rabi kwance tana bacci, shi ba zai iya jira har zuwa gobe da safe ba, dan tun bayan da ta kawo masa maganar Aliyu na raye ya shiga mata tambayoyi a kan Aliyun. Amma sai ta ce masa ita ba ta san komai a kansa ba bayan inkiyarsa, wato Kuliya, sannan kuma ta san cewa ma'aikacin DSS ne. Yanzu haka tafiyar da yake a motar, tunani, ruɗani, jimami da mamaki su ne suka cika kansa taf. Ya rasa ma wani kalar yanayi yake ciki, amma idan ya duba wani ɓangaren sai ya ga cewar kamar mamakin da yake ciki ya fi yawa. Dan ya na mamaki mutuƙa, na yanda Aliyun ya iya tserewa wutar da ta kama a gidan marayu, sai kuma mamakin sanin cewa shi ma SS ne, su na aiki a hukuma ɗaya, amma ba su san juna ba. Sai kuma wani murmushi ya suɓuce masa, tunawa da ya yi da alƙawarin da suke yawan ɗaukawa juna, na idan sun girma aikin SS shi ne za su yi. Wato bai manta ba kenan, tun da ga shi ya cika alƙawari. Hannunsa ya kai ya ɗauki wayarsa, a sanda yake faka motar a gefen hanya. Cikin jerin gwanon lambobin dake wayarsa, ya nemo ta RAM, tare da aika masa kira. Kusan ringing uku ta yi ba tare da an ɗaga ba, har ransa ya soma ɓaci, dan ya san halin RAM ɗin, shi a rayuwarsa sam bai iya zama da waya ba, wayat ma sam ba ta gabansa, mutumin da sai ya yi sati ba tare da ya san inda wayar tasa take ba. Sai a kira na biyar sannan ya ɗaga. Cikin magagin bacci ya soma gaida Zaid ɗin, ya amsashi a dake. “Ina san ka buɗe bayanan ma'aikatan hukumarmu, ka duba min wani wai shi ALIYU ZAID, inkiyarsa KULIYA!” Umarnin ya biyo baya. Daga ɗayan ɓangaren Ram ya miƙe tsaye daga kan gadonsa yana fita daga ɗakinsa, gudun kada ya tashi matarsa a bacci, ya koma falo ya zauna, har zuwa lokacin wayar na kare a kunnensa. Sai da ya murza idonsa kusan sau biyu, kafin ya sosa wuyansa, dai-dai kan wani tatto dake rubuce a wuyan nasa. “Sir a yanzu ba zai iyu na duba bayanan ba, sai de na datsi na'urar, amma ni zan iya baka amsa!” Daga ɗayan ɓangaren Zaid ya gyara zamansa ya na ɗaga kafaɗa. “Umhumm, Ina jinka” Ram ya ɗauko numfashi, sannan ya dire, dan kuwa ya san abun da zai aikata a yanzun, saɓawa ƙa'idar aikinsa ne, ba'a yarda su bawa juna sirrin wasu jami'an ba, amma kuma dole ne

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112