Chapter 6
Chapter 6
tana miƙawa Baba pure water. Sai kuma ta sauƙe hannun nata. “To ai shi ne ya min tsawa, kuma ya dake ni....” “Ai haƙuri ake uwata, idan kika yi haƙuri sai labari, dan wata ƙila ma kina gama makarantar auren ki za ki yi” Ido waje take duban Baba. “Aure fa Baba ?, a'a ni ba wani aure da zan yi yanzu, nawa ma nake da har zan wani yi aure?” Abinda bata sani ba shi ne, waɗanan kalaman nata zasu mai-maita kansa a cikin kanta kwanaki kaɗan masu zuwa, dan bata da masaniyar ƙaddarar da Allah ya hukunta za ta faru a 'yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura, ta kuma zama silar ɓacin wasu. A wurinsu ta zauna ta sha ruwa, har sanda su Baba suka fita Sallah, Sai da Mama Ladi ta mata jan ido a kan ta tashi ta je ta yi sallah, dan Allah ya sani, zuciya ɗaya take zaune da yarinyar, ganin ta ɗauketa kamar uwa, shi yasa ita ma ta ɗauketa kamar 'ya. Saboda rayuwar yarinyar tana buƙatar kulawar uwa, gashi ita kuma bata taso ta samu hakan ba. Ko da ta koma cikin gidan ɗakinta ta wuce. Wani haɗɗaɗe kuma ƙawattacen ɗaki wanda aka cika shi da kayan buƙata irin na matasa dai-dai shekarunta. Komai na cikin ɗakin peach color ne, sannan ga tarin teddies a ko wata kusurwa ta ɗakin. Lokarta ta buɗe, da ƙyar ta samu hijabin da ta saka, dan ba saka hijabai take ba, hatta da kayanta yawancinsu ƙananu ne, bata sakka kayan hausawa sam, a cewarta takura mata suke. Bayan ta yi sallar ta fita falo, a lokacin Daala ce kaɗai, zaune kan kujrarta tana ta gwalantunta, bakinta sai zubar da yawu yake. Zama ta yi kusa da ita, ta kunna musu tashar mbc 3, sannan ta shiga bata labarin da ita kanta tasan cewa Daalan ba fahimta take ba. Hammad ne ya shigo falon ta ƙofar ɗakinsa,byana shigowa ya ɗauki remote control ya sauya tasha. A fusace Mishal ta yi kansa. “Sh*ge ub*n baƙin hali, dan me zaka sauya mana tasha?, dan ka ga ban maka magana a kan munafurcin da ka min ɗazu ba ko?” Ta ƙarashe tana ƙwace remote control ɗin tare da maida mbc 3n da suke kalla. “Bar falon nan kafin na karya maka wuya” Da gudu ya yi sama. Kuma bai tsaya ko ina ba sai a ɗakin Hajjara, wadda ke kwantar da Fahima a kan gado, sakamakon baccin da ta yi. Ƙarya da ƙarerayi ya sameta ya zayyana mata. Kafin ita kuma ta bazamo ta sauƙo ƙasan ta samu Mishal ɗin tare da balbaleta da masifa, cikin ƙaraji da ɗaga murya take faɗan. “Wai ke yarinyar nan me kike nufi ?, so kike mu fice mu bar miki gidan ko me ?, to wallahi baki isa ba, shi har gwara shi, tun da nan gidan ub*nsa ne, ke kuma fa ?, sakabu fa kike, to wallahi ki fita idon yarana!......” Ba komai Mishal ke fahimta cikin kalaman nata ba, sakamakon ciwonta da ya shiga ƙoƙarin tashi, dishi-dishi take ganin komai, numfashinta ya shiga ƙoƙarin ɗaukewa daga ƙirjinta, waccan ranar ta soma dawowa cikin kanfa. _“Yau daga ni sai ke, kuma babu me ƙwatarki a hannu na!....”_ Abinda ya biyo bayan kalaman nasa sune ya zama silar shigarta cikin halin da take a yau. Numfashinta ya ci gaba da yin sama, da ƙyar take iya janyo shi. Zuwa lokacin Hajjara ta tuna da ciwon nata, sai ta tsaya a gefe tana kallonta kawai, a ranta addu'a take, kan Allah yasa idan nunfashin nata ya yi sama kada ya dawo. Mishal ta kai ƙasa tana dafe da wuyanta, sai neman iskar da za ta shaƙa ta ke, duk da sanyin acn dake falon sai gumi take, tuni idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, har hawaye ya fara sulalowa ta gefnsu, sai jan nunfashi take kamar me asthma. Fatan Hajjara bai karɓu ba, dan a dai-dai lokacin da ta faɗi ƙasa gaba ɗaya, a lokacin ne ƙofar falon ta iyo ciki, alamun wani ne zai shigo, kuma bai fi tazarar sakan ɗaya ba, siffar Abubakar ta bayyana a cikin falon. RABI POV. Zaune take daga gefe a kan dakalin ƙofar ɗakinsu, yayin da Habiba da sauran yaranta ke zaune a kan tabarma suna kiciniyar shan ruwa. Ba yau aka saba haka ba, kusan kullum hakan ake, a duk sanda za su taru irin haka, to ita za ka ganta daga can gefe tana kallonsu. Amma yau ɗin ba kallonsu take ba, tunanine fal kanta, tunani take kan abinda ya faru ɗazu a makarantar da take aiki, abinda ya faru ɗazu tsakanin Malamar nan da yarinyar da ta kira kanta da Mishal. Yanda yarinyar ta haƙiƙance kan ba za ta kwashe sharar ba, ita da ta mata magana, sai ta ganta a matsayin me sauƙin kai, ashe ba haka ba ne. Dan da ƙyar ta samu ta tausheta, sannan ta haƙura ta tafi, kafin ita Rabin ta dawo kan malamar ta bata haƙuri, kana ta ci gaba da sharar da ta fara. “Ni ban ga Abba ba” Cewar Saratu, kuma maganar tata ce ta dawo da Rabi zahiri. Habiba ta yi tsaki tana taɓe baki. “Yana can yawon gantalinsa mana” “Gaskiya Umma bakya kyautawa Wallahi, kullum ina faɗa miki cewar abinda kike bai dace ba....” Cewar Saratu, kuma tun kafin ta ƙarashe Mama ta tari numfashinta. “Eh, me u*a, an taɓo mata ƙahon zuciyarta, yau ni Allah na tuba har na kalli wannan abun na ce shine ub*na?!....” “Mama ya isheki haka.... Da kike rena shi a yanda yake, gwara shi sau dubu da iyayen wasu, kuma ub*n mutun ko a bola yake kwana indai har shi ne ya haifi mutum ro ub*nsa ne, ko miji bai isa ya amsa sunan uba ba.... Kuma ki sani cewar; da ub*a ake ado.....” Kuma Saratun na kaiwa nan ta miƙe daga kan tabarmar ta faɗa ɗakinsu har tana ƙoƙadin bangaje Rabi. “Aikin banza.... Umma mi ye na faɗa ba dai-dai ba ?” Mama ta tambaya tana tauna doyar bakinta, dan bisa ga dukkan alamu ma ba ta yi azumin ba yau” “Wallahi baki da laifi, me ake da Ɗan Lami a rayuwa?!, ita ma in ta gaji da abinda ake masa ne a gidan nan,ta yi zuciya ta nemi mijin aure....” Ita dai Rabi sai ido, dan bata isa ko tari ta yi ba, bata da wani kataɓus a gidan, yau wanda ya kawota ya aje ma bashi da iko da gidan bare ita karan kaɗa miya. “Umma babu ruwan sanyi fa...” Habiba ta kalli Fatima, sannan ta kalli ruwan dake aje a can baranda. “Yanzu ke dan baƙin hali kinsan babu ruwan sanyi a gidan shi ne kika yi shiru, yanzu da an kira sallah fa?” Ta kawar da kanta. Habiba ta yi ƙwafa tana cince ƙullin dake gefen zaninta, ta fito da nera ɗari biyu, sannan ta cillawa Rabi. “Karfa, uw*r 'yan baƙin hali, tashi ki je ki siyo mana ruwan sanyi leda ɗaya, kuma idan kin so ki zauna a can kin ji ?” Rabi ba tace komai ba, ta miƙe tsaye, sannan ta shiga ɗakinsu ta ɗauki hijabinta, ta fita. Mama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112