Chapter 104
Chapter 104
ya yi hakan, dan yana da tabbacin temako ne zai yi. “Tun shekaru biyar baya na fara aiki da kai Sir, haka ne?” Zaid ya gyaɗa kansa, a idonsa yake hango haɗuwarsu ta farko da Ram ɗin. “Haka ne” Ya faɗi cikin tabbatarwa. “Bayan shekara uku da fara aiki da kai, sai aka haɗani aiki da wani me kamarka, dan kuwa ba zan kirashi da kai kai tsaye ba, saboda akwai wasu banbaci biyu tare da ku. Wannan banbanci shi ne yasa na gane cewa, ku mutane biyu ne mabanbanta. Shi wannan wanda aka haɗani aikin da shi, sunansa ALIYU ZAID BICHI, inkiyarsa KULIYA. Confusing ɗin da kuka saka ni a ciki ya sa na fara bincike a kan rayuwar ko wannenku ba tare da sanin kowa ba. Kuma cikin ikon Allah sai na gano komai a kanku, sai de kuma na gano cewar ba ku san da zaman juna ba, kai kana zargin cewa Aliyu ya mutu, shi kuma an sanar da shi cewar ka gudu. A lokacin sai na samu Sir Andi, na masa bayanin abun da na gano, shi ne ya gargaɗeni da kada na kuskura na ɗaga zancen, na barku a haka, domin kuwa sanin junanku zai iya haifarwa da ɗaya daga cikinki matsala a aikinku. Sai na yarda da abun da ya faɗi, hakan tasa na yi shiru da bakina. Amma tun da har ka tambayeni a yau, na ji cewar ba zan iya ɓoye maka ba!” Shuuuuuu! Wata iska ta shiga wucewa ta gefen kunnen Zaid da ba wayar, hannunsa na hagu dunƙuke a kan bakinsa. Wai shi kam meke damunsa ne yau?. Ji yake kamar duk abun da yake faruwa a mafarki ne, kamar idan wani ya zungureshi zai farka ya ga cewar ba gaskiya ba ne. Ashe kenan duk tsawon wannan shekarun Aliyunsa na raye?. Miyau ya haɗiye da ƙyar, yana laluben muryasa a maƙogwaransa. “Ina ne address ɗin gidansa?” Da gudu motar Zaid ta shigo layin gidan Aliyu, Allah-Allah yake ya isa gidan, dan zuciyarsa na faɗa masa kamar biyuninsa baya cikin ƙoshin lafiya. A dai-dai ƙofar gidan da Ram ya faɗa masa ya yi parking, bai ko kashe motar ba, ya fito da gudu ya shiga cikin gidan, da megadin y fara cinkaro, yashe a ƙasa,, hakan ya sa hankalinsa ninkuwa wurin tashi. Zuciyarsa ko kamar za ta fashe dan tsabar bugun da take da ƙarfi. Cikin gidan ya kutsa, ya shuga dube-dube, amma be ga kowa a falo ba, ya shiga kitchen, babu kowa, ya fito ya nufi corridor ɗin dake ƙunshe da ɗakunan gidan, haka ya yi ta shiga ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, kafin ya samu nasarar gano ɗakin Kuliyan a cikin ɗakunan uku. Ya bincika ko ina be ga kowa ba, kuma tun da ya ga me gadin gidan a sume, ya fuskanci cewar hari aka kawo musu, imma de sun tafi da su, shi da matarsa, ko kuma suna ɓoye a wani ɓangare na gidan. Tun da de har aka faɗa masa cewar Aliyun SS ne, to tabbas akwai maɓoya a cikin gidan, dan su ba sa zama haka kawai, hatta shi kansa akwai maɓoya a gidansa. To amma a ina ta gidan Aliyun take?. Ya tambayi kansa, sa'ilin da yake dudduba ɗakin, wai ko Allah zaisa ya samu wata makama, amma haka ya hargutsa ɗakin, ba tare da ya samo komai ba. Har ya fara karaya, sai kuma idonsa ya sauƙa a kan ƙofar toilet, dan haka ya shiga ya dudduba nan ɗin ma. Amma bai samu komai ba, ya fito yana jin ƙirjinsa ya masa nauyi, kamar da aka ɗora masa wani gingimemen dutse a kan zuciyarsa, kamar da aka sa igiya aka ɗaure masa magudanar nunfashinsa haka yake ji, kansa ya masa nauyi, dan tarin abubuwan dak ciki za su iya sakawa ya tarwatse ma. Haka ya kai ƙasa yana haki, kamar wanda aka koro, idonsa har lumshewa yake, kuma a cikin lumshewar idonsa ya hangi ƙofar closet. Kamar an cillo shi daga wata uwa duniya haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar closet ɗin. Ya shiga cika ya na ta dube-dube. Har ya fara fawallawa Allah, yana tunanin cewa wata ƙila sun tafi da su ɗin. Kuma a dai-dai lokacin idonsa ya sauƙa a kan wani ɗigon jini, kamar ƙofar da aka buga da ƙarfi haka zuciyarsa ta buga. Ya dawo da dubansa kan lokar da yake tsaye a gabanta. Ya shiga bin jikinta da kallo a hankali, kafin ya samo wata makkuna a jiki. Hannunsa na rawa haka ya danna switch ɗin. Lokar ta zuge zuwa gefe, wata ƙofa ta bayyana a gabansa. Sai da ya haɗiyi yawu, na tsoron abun da zai iya tararwa a bayan ƙofar. Kafin ya kai hannunsa ya turata ciki. Abu na farko da ya fara cin karo da shi shi ne; wannan yarinyar da tace yana kama da yayanta ce durƙushe a ƙasa tana kuka, gefen fuskarta ɓace da jini. Daga ɗayan ɓangaren kuma, Aliyunsa ne jingine da bango. Shin kun san yanda mutum kan ji a sanda ya ga wani abunsa da ya cire rai da samunsa?. Ko kun san yanda ake ji a sanda ka samu abun da baka taɓa tsamaninsa ba?. To idan de har kun sani, wannan shi ne halin da Zaid Aliyu ya shiga. *There is no WiFi in forest, but you will find a better connection.* *** *No.86, Garki 2, Abuja...* RABI'A POV. A hankali ta shiga ƙi-ƙifta idonta, kafin ta buɗesu gaba ɗaya. Hannunta ta kai kan side drawer tana kunna wutar ɗakin, kafin dubanta ya dawo gefen inda take kwance, inda take kyautata zaton Zaid na kwance a wurin. Sai de me?, wayam haka ta ga wurin, sai wata takarda da aka yi rubutu a jiki, ajet a kan pillownsa. Ganin hakan ya sa hankalinta da ya fara tashi kwanciya. Hannunta na dama ta miƙa tana ɗaukar takardar, a lokaci guda kuma tana hamma, dan baccin be isheta ba. _Ba zan iya jira zuwa gobe ba, dan haka na tafi, zan turo Rhoda ta kaiki AS roma Academy, ki je, ki buga wasa me kyau, ba na son ki bani kunya, na san matata jarumace, dan haka ki nuna ƙwarewarki... Daga mijinki abun somki... Zaid (Raja)_. Dariya ta ɗan yi tana aje takardar. Abun be bata mamaki ba, dan ta ga ƙoƙarinsa a jiyan da tace masa ya bari sai gobe kuma ya bari ɗin, ashe shi bai haƙura ba. Sauƙa ta yi daga kan gadon tana hamma. Kamar jiya, yau ma bata jin daɗin jikinta. Ita ta rasa abun da yake damunta a kwanakin nan, sai ta yi ta amai, ga kasala, ga kuma rashin san cin abinci da ba ta yi. Sallah ita ce abu na farko da ta fara yi, kafin ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama gyara gidan, ta ɗora girki, tana gama girkin ta faɗa wanka. Bayan ta fito daga wanka ta saka wani baƙin leggings, da wata baƙar long sleeve high neck shirt, ta ɗora kimonohnta a kan kayan, sannan ta kawo wani baƙin baby hijjab ta saka. Ba ta yi kwalliya ba, dan da ma ita ba gwanar kwalliyar ba ce. Mai kawai ta shafa a jikinta, sannan ta ɗauki backpack ɗint ta saka kayan sport ɗinta a ciki.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112