Chapter 65
Chapter 65
shi a wurin 'yan makarantarsu tana faɗin ga mijinta nan. “Waye yake san maganar da ni” Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, dai-dai da lokacin da Mishal ta ɗaga tata kafaɗar ta dama, don kawai neman tsokana, ita ta rasa me yake ji a wannan ɗaga kafaɗar, mutum ya yi ta wani ɗaga kafaɗa?, shi ba tsuntsun ba, kuma ta lura da wancan ɗan uwan nasa ma ya na ɗaga kafaɗar. Cike da mamaki Kuliya yake kallon Mishal, wato shi take kwaikwayo?, don ta na ga ya na ɗaga kafaɗa shi ne ita ma za ta yi?. Kuma ita ma ta lura da kamar fushi yake shirin yi, don haka ta yi saurin cewa. “Waye yake son maganar da ni?” Maganar tata ta tuna masa da batun da ya zo mata, sai ya share batun ɗaga kafaɗa yace. “Yayarki Nimra” Sai ta juya ta kashe wutar gas ɗin, sannan ta juyo ta kalle shi. “Wayar tana ina ?” Da hannunsa ya nuna mata falo, don shi gajiya yake da wannan surutan, ita ma kuma ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta raɓa shi ta fice tana dariya ƙasa-ƙasa. Ƙamshin da stew ɗin ke yi ya ci gaba da shiga hancin Kuliya, don haka ya cewa kansa de yau ya kamata ace ya ɗanɗana abincin nata, sai ya shiga bubbuɗa pots ɗin da ta yi girkin da su, farar shinkafa ce sai wannan stew ɗin dake ta tashin ƙamshi, ga kuma coslow a gefe. Tsakani da Allah abincin ya burgeshi kamar sauran abincinta, ga kuma yunwar da yake ji, saboda rabonsa da abinci tun safe, ya kai hannu ya ɗauki plate, ya zuba abincin iya yanda ya san zai iya cinyewa. Sannan ya fara ci, bai taɓa zaton ƙaramar yarinya kamar Mishal za ta iya yin girki haka ba, a da duk ɗaukan zancen girkin nata yake a matsayin shirme, amma yanzu da ya ɗan-ɗana sai ya ji kamar irin wannan abincin yake buƙata a kullum domin ci. Mishal na fita ta hangi wayar tasa aje a kan coffe table, da sauri ta ƙarasa wurin ta ɗauki wayar, gaisawa suka yi, kafin Nimran ta tambayeta yanayin zaman nasu, kana ta ƙara mata da nasiha, ita kuma Mishal ɗin babu abun da ta tambayeta sama da Daala, don ita kaɗai ta yi kewa. Sai da suka gama wayar, sannan ta tashi ta nufi kitchen ɗin, zuciyarta ɗaya ta tura ƙofar kitchen ɗin, kuma abu na farko da idonta ya fara gane mata shi ne. Kuliya tsaye a kusa da stove, hannunsa na hagu riƙe da plate, wanda yake cike da shinkafa da miyar da ta dafa, harda coslow a gefe, hannunsa na dama kuma riƙe da cokali, ya kai shi setin bakinsa ya na shirin kai loma. Ba ƙaramar dariya ya bata ba, mutumin da a kullum yake gudun cin abincinta, yau shi ne ta kama ya na cin abincinta a ɓoye, amma sai ta riƙe dariyar, ba tare da ta ce masa komai ba, ta tsaya a kusa da shi, ta sauƙe tukunyar stew ɗin daga kan stove. Kuliya ya ci gaba da binta da kallo, ya zaci za ta ce wani abun, amma sai ya ji ta yi shiru, har ta gama kwashe abincin duka, ta zubawa Ayra, sannan ta ɗauki nata ta zauna a kan kujerar island. Ganin ya kasa ƙarasa cinye abincin nasa ya sa Mishal faɗin. “Ka zauna ka ƙarasa ci” Kuliya ya ɗan sosa ƙeyarsa, sannan ido ba kunya ya ƙaraso ya zauna a tsallakenta ya na ci gaba da cin abincin. Ita dai Mishal sai ƙunshe dariyarta take, duk da daga can ƙasan zuciyarta akwai wani abu ɗan ƙanƙani me kama da damuwa, kuma abun ya samo asali ne saboda rashin zuwan Adawiyya makaranta!, abu ne wanda tun bayan da suka ɗinke bai taɓa faruwa ba, ko a da can ba ta ganinta tana fashi bare yanzu, amma har can ƙasan zuciyarta take fatan kada Allah ya sa wani abu mara kyau ne ya faruwa da Adawiyyan. *Washe gari...* *Brickhall School, Kaura District, Game Village, Abuja.* RAJA POV. Cike da mamaki principal ɗin makarantar yake kallon mutumin dake zaune a tsallaken teburinsa, kamar ba shi ba ne jiya ya zo ya na tambaya a kan Rabi'a, yau kuma sai ga shi ya dawo da wani yanayi da ban, saɓanin wanda ya zo da shi jiya, stil kuma ya na sake tambayarsa a kan Rabi'an. “Ka yi shiru, ko akwai matsala ne?” Rajan ya tambaya, ganin yanda mutumin yake kallonsa, principal ya girgiza kansa. “Ba haka ba ne, kawai dai yau kwana biyu kenan bat ta zo ba!” Wani irin shiru ne ya ratsa office ɗin, kuma a cikin shirun, banda bugu cikin sauri babu abun da zuciyar Raja ke yi, wannan abun da yake ji a jikinsa ya fi ƙarfin tsoro, ji yake kamar ma ya haukace ne, me ya sa Rabi'an ba ta zuwa?, saboda shi ne?, amma me ya sa?, ko wani abu ne ya sameta?. Da waɗanan tambayoyin fal a ransa ya bar office ɗin. “Yayana!” Ya ji an kira sunan a bayansa, amma bai tsaya ba, saboda halin da yake ciki ba zai barshi ya tantance da shi ake ko ba da shi ake ba. “Ɗan uwa!” Aka kuma kiran sunan, hakan ya sa ya tsaya sannan ya juyo, wannan yarinyar ce, wadda ta ce masa ya na kama da cousin ɗinta. “Dama a nan kake ?” Mishal ta tambaya a sanda take isowa gabansa, mamaki fal kanta, na son sanin me ya zo yi a makarantarsu. “Na... Na zo neman wani ne” Sai ta gyaɗa kanta. “Ka same shi?” Ta tambaya, sai ya girgiza kansa. “A'a, ban same shi ba” Ya faɗi yabna ɗaga kafaɗarsa ta dama, Mishal ta jinjina girman Allah a cikin ranta, sak Kuliya,duk da akawai 'yan banbance banbancea tsakaninsu. “Faɗamin sunansa, na san kowa a makarantar nan, zan nemo maka shi” Duk da halin da yake ciki sai da ya ɗan murmusa. “Ba lalle ki san shi ba. Zan koma, na gode ƙanwata, ki kula da kanki!” Haka kawai ya samu bakinsa da furta sunan, kuma bai jira cewarta ba, ya juya ya ci gaba da tafiya. Mishal ta ci gaba da kallon bayansa, abubuwa da dama na mata kai kawo a cikin kai, tana son ta san me ya sa Anti Adawiyya ba ta zuwa, kuma ta na son sanin me ya sa Kuliya babya tare da ɗan uwansa, tabna son ta san me ya sa su duka suka zo makarantarsu, don ta san ko Kuliyan ma jiya ba wurinta ya zo ba. *No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja.* Siyama da Karima Yayarta da kuma yaran Kariman ne zaune a falo suna karin kummalo. Kowacce a cikinsu jikinta ɗauke yake da rauni, raunin da suka samu a zuwansu gidan Kuliya. “Salamu Alaikum!” Suka ji sallamar Anna, a yayin da take turo ƙofar falon, da sauri Karima ta miƙe tsaye, hakan ya sa Siyama ma ta miƙe, saboda sun san ba su da gaskiya. Ɗaya bayan ɗaya yaran Kariman su uku suka riƙa gaida Anna, ta na amsa musu. “Abdul ku je ɗakinku ku ƙarasa karin a can” Babban ɗan nata ya amsata ya na haɗa kan ƙannensa wuri ɗaya, tare da ɗiban kayan abincin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112