Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ta bi bayanta da harara. “Wallahi na tsani yarinyar nan, dan Allah Umma ki koreta ta koma inda ta fito” Habiba ta yi dariya. “Baki da hankali Mama, ai idan na barta haka ban amsa sunan Habiba ba, so nake sai ta tagayyara tukunna, ba na so ta koma wurin dangin uwarta ta ji daɗi, dan kinsan ai 'yan uwan uwar tata suna da kuɗi, so nake sai ta gama lalacewa, so samu ma ta haɗa da cikin she*e, sannan zan sa Ɗan Lami ya koreta daga gidanan, tunda dama ni ce na saka shi ya kawota!” Mama ta tintsire da dariya, Fatima na na tayata. Rabi na fita kai tsaye bakin titi ta nufa, a hanya ta tsaya tana kallon wasu yara dake buga wasan ƙwallo. Ba yau ta saba ganinsu suna ƙwallon ba, kusan kullum a lokaci irin wannan suna buga ƙwallo, a wasu lokutan ma ba su ne suke yi ba, manya ne ke yi a filin, kasancewar ana azumi shi yasa manyan basa bugawa. Tsaiwarta ta gyara tana ci gaba da kallonsu, ƙwallo na ɗaya daga cikin burukanta na duniya, ƙwallo mafarkin rayuwarta ce, a da bata da wani fata sai na ta zama shahararriyar 'yar ƙwallo. Sanda Ummanta na raye burin nata ya ɗauko hanyar cika, dan akwai wata football academy da Umman nata ta sakata, kuma kullum tana zuwa yin training, sai dai bayan rasuwar Umman tata komai ya sauya. Komai ya ruguje, ciki kuwa harda burinta na zama 'yar wasan ball, dan a nan gidan makaranta ma ba'a barta ta je ba, ta ina za'a barta ta wani samu damar tarining. A gidan kakaninta kuwa cewa suke ai ƙwallo ba wasan mata ba ce, dan haka ita ƙwallo ba ta dace da ita ba, ko a sanda Umman na raye babu yanda ba'a kai ruwa rana ba a kan wannan ball ɗin. Ganin tsaiwar ba zata kaita ba hasa ta kwashi ƙafafunta ta yi gaba. *FHA 2 lugbe, abuja* *11:00am* Wasu baƙaƙen motoci ne har guda biyu suka yi parking a gaban wani gida cikin layin. Yanayin gudun motocin ne kaɗai zai tabbatar maka da ba lafiya ba. Ƙofar gaba ta ɗaya daga cikin motocin ta buɗe, wani matashi ya fito a fusace, yanayin yanda yake fitar da iska daga hancinsa ne kaɗai zai tabbatar maka da cewar a fusace yake. Sauran ƙofofin suka buɗe, sannan ɗaya bayan ɗaya mutanen ciki suka firfito, yanayin shigarsu ne kaɗai zai shaida maka matsayinsu. Duka sanye suke da baƙaƙen kaya, sannan a jikin kowannensu akwai bullet proof jacket, wadda a jikinta aka rubuta DSS. Na farkon da ya fito ne kaɗai babu bullet proof jacket ɗin a jikinsa. Kuma shi ne a kan gaba wajen shiga cikin gidan, a harabar gidan suka tsaya. Matashin sai safa a marwa yake, kamar wanda aka ɗorawa maganar duniya. Ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ya taho kusa da shi, hannunsa riƙe da bullet proof jacket, a tsorace yace. “Sir baka saka wannan ba...” Wani irin kallo da ya masa ne yasa bai ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa ba. Hakan yasa jami'in ja da baya, ya matsa kusa da mace ɗayan dake cikinsu, dan kaf wurin maza ne, ita kaɗai ce mace. “Ki masa magana” Kanta ta gyaɗa, sannan ta sofare bingarta ƙirar pistol a aljihun wandonta na baya. Ta sa hannu ta karɓi rigar, ta matsa kusa da shi. “KULIYA kana buƙatar wannan......” Sai da ya fitar da wani huci na takaici, sannan ya miƙo hannunsa ya fisgi rigar ba tare da ya kalleta ba, rigar ya saka yana ta hura hanci. Sannan ya yi alama da kawo masa abun magana. “Ta ko ina gidanan a kewaye yake da jami'an tsaro, zai fi muku da ku miƙa wuyan ku cikin ruwan sanyi, idan kuma ba haka ba!.......” Ya kai ƙarshen maganar yana haɗe haƙwaran sama da na ƙasa cikin fusata, sai da ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba. “Idan ba ku miƙa kanku ba, sai na binne kowannenku da ransa, idan kuma kun musa, kada wanda ya fito a cikinku!....” Wani irin shiru ya ratsa wurin tsawon muntuna biyar, cikin gidan babu wani motsi kamar babu kowa, alhalin akwai mutum har biyar a cikin gidan. “Wallahi wannan mara mutuncin ne!....” Wani matashi ya faɗi daga cikin gidan, bayan ya sauƙe labulen ɗakin da suke ciki. A tsorace ya yi maganar, kuma daga yanda jikinsa ke rawa zaka fahimci hakan kalar tsoron da yake ji. Cikin halin ko in kula wani cikin mazan dake ɗakin yace. “Wai wa kake nufi?” “KULIYA!” Kusan a tare gabansu su duka ya buga, ciki kuwa harda wanda ya furta sunan, KULIYA!, wani suna ɗaya da yake firgita duk wani me laifi a garin abuja da kewatenta. Sunansa kawai kan sa cikin mai laifi ya ɗuri ruwa, KULIYA wani irin bahagwan mutum ne, wanda ba'a gane gabansa bare bayansa, ga saurin fushi da fusata, bashi da imani ko kaɗan. A razane suka miƙe tsaye gaba ɗaya, kuma ɗaya bayan ɗaya suka shiga leƙa windown dan tabbatar da abinda ɗayan nasu ya faɗa. “Yanzu miye abun yi ?” Ɗaya daga ciki ya tambaya, fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali. “Kawai mu miƙa wuya” “Kai baka da hankali, mu miƙa wuya fa?” “To mu ci gaba da zama har ya shigo ya harbe mu” Daga harabar gidan, Kuliya ya fiddo da bindigarsa wadda ke saƙale a bayansa, sannan ya nufi hanyar shiga cikin gidan gadan-gadan. “Kuliya!, what are you trying to do ?” Wannan macen cikin nasu ta faɗi tana bin baya sa. “Sharon, kar ki takuramin!” “Ba'a bamu umarni ba, dole sai mun jira umarni.....” Sharon bata rufe bakinta ba, Kuliya ya raɓata ya wuce cikin gidan. Cike da takaicinsa ta ɗaga kanta sama tana girgiza shi, har abada Aliyu ba zai taɓa sauyawa ba. Matasan nan na tsaye a cikin ɗakin, suna ta nemawa kansu mafita. Basu ankara ba suka ji an banko ƙofar ɗakin, kuma a cikin ƙasa da sakan sittin. Ƙarar harbin bindigar Kuliya ya cika gidan. Kafin aka samu wani harbin da ya fito ba daga bindigar tasa ba!. *Kano....* *11:30pm* Motoci biyu ne parker a wani filin Allah, wurin ba gida gaba da baya. Duka fitilun motocin a kunne suke, kasancewar babu wani haske a wurin bayan na motocin. Motocin na kallon juna ne, yayin da wasu mutane shida ke tsaye a tsakiyarsu. “Ku bamu saƙon” Muryar macen cikinsu ta faɗa, wasu gardayen maza ne guda uku a bayanta, alamun dai tare suke. Yayin da take fuskantar wani matashi, wanda shi kuma mutum ɗaya ne tsaye a bayansa. Matashin ya yi murmushi. “Ku bamu kuɗi tukunna....” Ya faɗi cikin rainin wayo. Sai macen ta yi murmushi, tana kawar da kitson kalabar attachment ɗin da ya sauƙo mata kan fuska. “Ka...bamu saƙon!” Ta maimaita masa abinda ta faɗi tun farko, sai ya kuma yin murmushi. “Ku kira ogan naku ya zo ya karɓa muku....” Daga cikin motar dake bayan su macen, mutum ɗaya ne zaune a gidan gaba, kansa a sama, yayin da bayansa ke jingine da jikin kujera. Waƙar lonely at the top dake tashi a cikin motar yake biyawa, yayin da idanuwansa ke a lumshe. “Zuwan RAJA nan ba zai mana daɗi ba, dan haka ka bamu saƙon,

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112