Skip to content

Chapter 92

Chapter 92

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

“Kawai de ina kewarta ne?” Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai. “Nanbda sati ɗaya ne fa Teddy Bear,saurin me kike?” Ta juya ta na ci gaba da aikinta tare da faɗin. “Na gaji da zuwa school ne... Kuma mun kusa mu fara exams” Lokar ta rufe, sannan ta juyo ta iso gareshi. “Next term za ku fara Neco da Waec right” “Ummm!” Ta amsa masa tana karɓar wayar hannunsa. “Lokacin danna waya ya ƙare, let's fall asleep” Murmushi ya yi ya ja kamo hannunta, tare da zaunar da ita akan gadon. Wayarsa dake haannunta ya karɓa ya na ajeta kan side drawer. Kwantar da ita ya yi a kan gadon, ya juya ya kashe wutar ɗakin, sannan shi ma ya kwanta ya na karata da jikinsa. “Abu Aswad?” Mishal ta kira sunan bayan wani lokaci. “Ummm!” Muryar Kuliya ta amsa ƙasa-ƙasa, alamun kamar ma ya fara bacci. “Yaya batun Anti Adawiyya?” Tar Kuliya ya buɗe idonsa cikin duhun ɗakin. Jin ta ambato masa sunanta, bayan da ya gama bincike ya gano komai a kanta, ciki kuwa har da fyaɗen da aka mata, sai de kuma baya so ya faɗa mata komai, dan baya so hankalinta ya tashi, shi ya sa bar wa cikinsa maganar, ba tare da ya faɗa mata komai ba. “Sharon tace zuwa gobe za a iya samo address ɗin gidansu, ki kwantar da hankalinki!” Ya faɗa mata dan ta kwantar da hankalinta, wata ƙwalla ce ta taru a idon Mishal, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta silalo. Sai jin damshi Kuliya ya yi a gaban rigarsa, kasancewar kanta na kan ƙirjinsa ne. Iska ya furzar daga bakinsa ya na ƙara ƙanƙameta. “Hafsat?” “Na'am!” Ta amsa a raunane. “Ni fa da kaina na ce miki zan gano miki inda take, babu abun da zai sameta” Hawayen ta goge da kanta tana gyaɗa kai. “Umhumm!” “I love you, maza ki yi baccin ki.....” “I hate you” Ta faɗi tana lumshe idonta. *No.86, Garki 2, Abuja...* *10:20 PM.* RABI'A POV. Tsaye take daga jikin dressing mirrorn ɗakinta, a hankali ta aje wayarta dake riƙe a hannunta, bayan da suka gama waya da Jidda. Juyowar da za ta yi ta ji an buɗe ƙofar ɗakin. Ba shiri zuciyarta ta doka tsallen albarka a ƙirjinta har sau biyu. Dan kuwa ko ba'a faɗa ba, ko ba ta kalla ba, ta san waye, hakan ya sa ba tare da ta ko kalli side ɗin ƙofar ba, ta juya ta ƙara fuskantar mirronrn. Allah ya sani, sam bata son su haɗu, ba ta son wani abu ya haɗasu, ta na jin kunyarsa da kuma kunyar kanta da ta yi masa mummunar fahimta, tana ta zarginsa game da abun da sam bai aikata ba, me ya sa zuciyarta ta yarda da abun da idanuwanta suka gani?, me ya sa har take zaton shi zai iya aikata wannan mummunar ta'asar?, kaiconta da ta kasance mace me matuƙar san kai. Satinsu ɗaya da aure, amma fur ba ta yarda su haɗu ko da wasa, kullum za ta yi girki ta aje masa nasa amma ko da kaɗan ba ta bari ya ganta. Ba za ta iya haɗa ido da shi ba, ta kalli tsabar idonsa tace shi makashi ne, tace za ma ta iya kaksheshi, duk da ba da gaske take ba, amma ai ta faɗa. Tunaninta ya katse a sanda ta ji tsayuwarsa a bayanta. Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa ta cikin mudubin dake gabanta. Zaid ya ci gaba da kallonta da lumsassun idanuwansa, tun bayan ranar da ya bayyana mata gaskiyar kasancewarsa ma'aikacin DSS suka shiga wasan 'yar ɓuya shi da ita, wata ƙila kunyarsa take ji, wata ƙila kuma ba ta yarda da abun da ya faɗa ba ne. Ko ma de me take tunani a kai, shi de be damu ba, damuwarsa ita ce rashin ganinta, nisantarsa da take ya fi sosa masa rai, shi be ƙi a kullum ya kasance da ita ba, ko da kuwa za su ci gaba da zaman doya damanja ne, dole ne ta sama musu mafita, dan shi kam gaskiya ya gaji da wannan tazarar da suke bawa juna. “Ammatan Raja!” Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, ko a da ma ya ake ƙarewa idan ta ji sunan?, bare yanzu da sunan ya samu ƙari a gaba, ‘Ammatan Raja!’ haka yake kiranta. Sai ta kasa amsawa, ta ci gaba da kallonsa ta cikin mirrorn. Raja ya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya yi taku ɗaya... Biyu.. Wanda ya ƙara kusanta shi da ita, sannan ya ɗaga hannayensa tare da zurasu ta ƙugunta, suka kewayo zuwa cikinta, kafin ya jata baya zuwa jikinsa, ya sunkuyo da kansa zuwa wuyanta. Ba shiri Rabi ta rintse idonta gam, wai me ya sa?, me ya sa duk yadda zai taɓa jikinta irin haka sai ta ji wani sauyi tare da ita,me ya sa?. “Na yi lefi ne?... Ko har yanzu ni makashi ne a idonki?” Ya tambaya muryar ta sa na fita a hankali, Rabi'a za ta iya cewa sai da kalaman suka gama shawagi a kan fatar wuyanta kafin suka isa zuwa ga kunnuwanta, a lokaci guda kuma sai ta ji jikinta ya ɗauki wani irin ɗumi, kamar wata wadda aka kara a jikin kyandir, ko wata ƙofa ta gashi a jikinta ta buɗe. Amma sai ta ture komai ta girgiza masa kai. Zaid ya saka hannayensa ya na juyowa da ita, ta fuskanceshi, ya sunkuyar da kansa dan samun damar haɗa ido da ita amma fur ta ƙi barin hakan ta faru, don nata idanuwan kulle su ta yi gam. “Idan de kika ci gaba da yin abun da kike ɗin nan zan ɗauka cewar har yanzu baki yarda da ni ba!” Da sauri Rabi'a ta buɗe idonta, dan kuwa gwara ta sha kunya da ace ya ɗauka cewar bata yarda da shi ba ne, a yanzu tana jin wani irin girma da kamarsa na ƙara hauhawa a cikin ranta, wani irin kwarjini yake mata, wanda ba za ta iya kwantanta kalarsa ba. “Trust me Diary... Wallahi gaskiya na faɗa...” Da sauri Rabi ta ɗago da hannunta ta rufe masa baki tana girgiza masa kai. “I trust you Raj. And I'm sorry” Cikin hanzari Zaid ya kai hannunsa ya kamo nata dake kan bakinsa, ya riƙe hannun nata ya na kallon fuskarta da ta fara jiƙewa da hawaye. “Babu buƙata Ammata, kuskuren fahimta ne” Rabi ta ja hanci. “Amma me ya sa to ni na kasa fahimtarka?. Ya kamata ace na fahimceka Raj... I'm sorry... I'm really really sorry...” Saurin rungumeta Zaid ya yi, hakan ya bata damar sakin kukan dake cin ranta, ta masa kuskure, abun da ta masa sam be kamataba, ta aikata babban kuskure. “Ka yi haƙuri please!” Kansa ya ci gaba da girgiza mata yana ƙara ƙanƙameta a cikin jikinsa. “Wallahi sam ba ki min kuskure ba. A ko da yaushe ni me miki uzuri ne ko da kin yi laifi, bare kuma ba ki aikata komai ba. Ba dan komai ya sa na ɓoye miki ba sai dan yanayin aiki, ina kan wani assignment ne yanzu haka” Rabi ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tana sakin wani kukan, ba ƙaramin ɗaɗi

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112