Chapter 23
Chapter 23
sa hannusa a aljihunsa ya zaro handkerchief, sannan ya ɗaure hannun yarinyar. Ya lura da ita ma tun ɗazun kallonsa take, sannan irin mamakin da ke kan fuskarsa shi ne sak a kan tata fuskar. “Babu inda kika ji ciwo?” Wannan salihar muryar tasa ta tambaya, yayin da take kallonta da gray drunken eyes ɗinsa. Ya lura da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta gyaɗa masa kai. Shi ma sai ya gyaɗa mata nasa kan, sannan ya miƙe a hankali, idonsa a kanta, yayin da ita take zaune a dandariyar ƙasa. Juyawa ya yi a hankali sannan ya nufi motarsu da ke tsallake, Rhoda da Zuzu da su ma suke kallon abun mamaki suka bi bayansa, kuma da haka suka iso gidan. Waɗanan lumsassun idanuwan nasa ya ƙara lumshewa, fuskarta na dawowa a idonsa. Sai kawai ya shafi sumar kansa dake cikin askin high fade. Sannan ya ɗaga kafaɗarsa. Shi ya kasa ganewa, me yasa hakan ke faruwa da shi ?, wacece wannan yarinyar ?, menene LABARINTA ?, me yasa take kama da shi, Momma da Aliyunsa?. A hankali ya buɗe rabin idon nasa kamar kullum, ya kamata a ce ya kawar da wannan tunanin, don ba abun da ya kawo shi Abuja ba kenan, ya zo ne domin cimma wani ƙudirinsa, ya zo ne domin ya kawo ƙarshen wani abu. Dan haka dole ya jingine komai, ya fuskanci abun da ke tunkararsa, Allah ya ƙaddara haɗuwar wannan yarinyar da shi ne dan kawai tasa ya tuna rayuwarsa ta baya, kuma ya tuna ɗin, dan haka komai ya ƙare, ya ƙare daga nan. Abun da bai sani ba shine; yanzu komai zai soma, yanzu ƙaddarar ta soma, ba ayi komai ba ma. Ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta nan da 'yan wasu kwanaki na dab!, da faruwa, wata ƙaddara da za ta tarwartsa komai, sannan ta saita wasu lamura. *Unguwar Madallah, Suleja , Niger State* *08:30pm* RABI'A POV. Zaune take a ɗakinsu, yayin da take jera kayanta a cikin ghana most go ɗinta. Gani ta yi kayan nata sun jima ba tare da ta duba su ba, shi yasa yau ɗin ta fitar da su, dan ta sauya musu ma'aji. Hannunta na dama ta kalla, wanda ke ɗaure sa handkerchief ɗin da wannan mutumin na ɗazu ya ɗaura mata. Wannan mutumin?!, Wannan mutumin da ta ji macen da suke tare, me kaya irin nasa ta kira shi da RAJA!. Wannan mutumin mai kama da Ummanta. Tunaninsa ya tuna mata da wallet ɗinsa da ta tsinta a ɗazun. Don bayan ya miƙe ya shige motarsa sun bar wurin, ta shiga yunƙurin miƙewe, kuma miƙewar da za ta yi idonta ya kai kan wallet ɗin da take da tabbacin tasa ce. Hakan yasa ta tsugunna ta sa hannu ta ɗauka, kuma ba ta buɗe a lokacin ba, sai kawai ta juya ta ci gaba da tafiyar ta. Waige-waige ta shiga yi a kan katifar Saratu, dan tana zaune ne a bakin katifar, ƙasan hijabin da ta fita da shi yau ta samo wallet ɗin. A hankali ta ɗauketa, sannan ta jujjuyata, kafin ta saka hannu ta buɗeta, a dai-dai inda ake saka hoto, ta ga hoton mutum biyu masu kama ɗaya, kuma hatta da kayan jikinsu iri ɗaya ne. Ba dan dariyar da ɗaya ya yi ba, da babu abun da zai hana tace duka mutum ɗaya ne, zaune suke a ƙasa, daya ya dafa ɗaya. Yau ta fara ganinsa, amma duk da haka sai da ta gano shi a cikin su biyun, saboda rabin idanuwasa da suke a lumshe, sannan akwai tsotsiyar karen da ta ga a ƙasan haƙorinsa. Iko sai Allah, kenan ba ma shi kaɗai ba ne, to amma umma ta faɗa mata cewar abokiyar tagwaitakar ta wato mai sunanta Rabi'a ta rasu, kuma ta rasu, bayan rasuwarta ma aka ce su ma yaran da ta haifa sun rasu. To su waye waɗanan ?, me yasa suke kama da Ummanta da kuma ita, dan ganin ɗaya ɗan uwan nasa yasa ta ƙara ganin kamarta a cikin fuskokinsu, duk da a lokacin yarinta aka musu hoton. A hankali hannunta ya ci gaba da buɗa wallet ɗin, akwai kuɗaɗe a ciki, sai atm cards. Bakinta ta taɓe, sannan ta rufe wallet ɗin, wata ƙila Allah zai sa su ƙara haɗuwa, sai ta samu damar ba shi kayansa. Aje wallet ɗin ta yi a gefe, sannan ta ci gaba da shirya kayan nata. Kuma a cikin kayan ne, hannuta ya ɗauko wata jersey, jerseyn ta Bacerlona ce. Kuma tata ce. Nan take idanuwanta suka hango mata lokacin da aka samu rigar. _“Yaya Baby, Umma ta dawo”_ _Muryarta ta faɗi, a sanda take kallon Umman tasu da ta dawo daga asibiti, sannan a lokaci guda ta faɗa jikin mamar tata ta rungumeta._ _“Umma sannu da dawowa”_ _Baby ta faɗi a sanda ta leƙo daga ɗakinta. Umman tasu ta kalleta tana amsawa._ _“Yayar mamarta kin san me Umma ta kawo miki ?”_ _Umman ta faɗi a sanda take zama a kan sofa, cike da ɗauki Adawiyya ta girgiza mata kai alamun a'a._ _“Jersayn Becelona!...”_ _Umman ya faɗa tana fiddo da jersyn daga jakarta da ta saba fita da ita. Adawiyya ta daka tsalle ta rungume Umman tana murmushi._ _“Thanks Umma”_ Jin wata ƙwalla na shirin taruwa mata a ido yasa ta yi saurin cilla rigar cikin kayanta, a mafiya yawan lokuta rayuwarta ta baya ba ta faɗo mata sai a sanda ta ga wasu kayanta na da. A da ba ta da jerseyn sakawa da ta wuce wannan, dan Barcelona shi ne favourite team ɗinta. Ba ta da burin da ya wuce idan ta girma ta fara biluga ball, har ta kai ga wata rana Barcelona su ce za su siyeta, ta tafi can ta je tana buga musu ball. Jama'a da dama sun sha mata kallon banza a kan ball ɗin da take da burin yi, kuma ba kowa ba ne illa al'umarta, hausawa 'yan arewa, kamar dai sauran mata, ita ma haka ake fatan ta darƙushe baiwarta ta ja bakinta ta yi shiru. Saboda ana ganin ba za ta iya ba, a matsayinta na mace, mutane na ganin zaman gida ne ya dace da ita, ita kanta ta san da hakan, amma kuma aure ba shi zai hanata cimma burinta ba, tana san ta zama wata aba a fannin buga ball. Wata rana ita ma a saka sunanta a jerin ƙwararru, kuma duk wanda zai kira sunan nata dole sai ya kira arewa, domin nanne tushenta, nan ne asalinta. An sha cewa ba ta da hankali, dan kawai tana san zama 'yar ball, a ganin mutanen arewa ball wasan maza ne, mace ba za ta iya ba. A da Ummanta ta saka mata a ranta cewa za ta iya, ta ba ta duk wani goyon baya kan ta yi, amma kuma yanzu komai ya tsaya, komai ya wargaje tare da rasuwar Umman. *DSS (Department of State Service) Headquarter, Maitama Evenue, Abuja* KULIYA POV. Cikin takunsa mai ƙarfi yake tafiya, kansa a sama, babu ruwansa da kallon kowa, ciki kuwa harda waɗanda ke gaida shi, kuma suma da alama basu damu ba, don idan da sabo sun saba. Shi kullum haka yake rayuwarsa, babu ruwansa da kowa a wurin, idan har kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112