Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

haka ba... Tazarar awa ɗaya ne tsakanina da shi a haihuwa, kuma bayan wannan tazarar ba mu sake samun wata tazara ba... A ko da yaushe muna tare” Cike da tausayawa Malam Ila ya girgiza kansa. “Ka ga abun da za ayi shi ne; zuwa gobe sai muje mu duba shi ko?” Cike da zumuɗu Zaid ya ɗagaa kafaɗarsa. “Allah ya kaimu goben, na gode Malam Ila, Allah ya saka maka da alkairi...” Washegari da sassafe Zaid ya dira a ƙofar shagon Malam Ila, ko fitowa ma bai yi ba, haka ya zauna ya na jiran fitowar Malam ilan. Sanye yake da wani farin yadi, wanda Malam Ila da kansa ya bashi, don yace ba ya san ganinsa da wannan uniform ɗin. Kana ganin kayan za ka san cewa ba nasa ba ne, saboda yanda kayan ya masa yawa. Ya na zaune a wurin har Malam Ila ya fito, babu yanda be yi da Malam Ila kan su wuce gidan marayun katsaye ba. Amma Malam Ilan ya dage kan sai ya sai masa abinci ya ci tukunna. Hakan kuwa aka yi, sai da ya sai masa abincin ya ci ya yi taf, sannan suka kama hanyar gidan marayun. “Bawan Allah, Lafiya kuwa na ga kamar gidan marayun nan a kulle, kuma na... Na ga kamar ma gobara aka yi!” Cewar Malam Ila a kiɗime, hankalinsa ya yi wata mummunar tashi, bayan da suka iso gidan marayun, suka ga gate ɗinsa a kulle, kuma ko daga bakin gate din za ka gane cewa an yi gobara a wurin. Mutumin da Malam Ila ya tambaya ya kalle su. “Kwana huɗu kenan da wuta ta kama a gidan, kuma babu wanda ya fita da ransa daga gidan!...” Iyaka abinda Zaid ya iya fahimta kenan a zancen nasa, bai san sanda ya yanke jiki ya faɗi ba. Kwanansa uku a asibiti kafin ya farfaɗo, kuma da ya tashi farfaɗowar ma ba a hayyacinsa ya farka ba. Abubuwa ya riƙa yi kamar wanda ya samu taɓun ƙwaƙwalwa, sai zantuka yake barkatai, an kasa gane kansa. Ganin abun ba na ƙare ba ne ya sa Malam Ila ɗauke shi daga asibitin, don ya ga abun ba na asibiti ba ne. Tashin farko gidansa ya kai shi, amma matarsa tace fafur ba za ta karɓi tsinttaciyar mage ba. “Wa to kai ga ka juju ko?, Ub*n yaye-yaye, to Wallahi ba za ta saɓu ba!, a ina zan saka wannan gardin ƙaton?, A gida ɗaki ɗayan?, Ga ka, ga ni, ga 'ya'yana, to Wallahi Malam da sake!” “Haba Gambo, be kamata kike faɗin haka ba, yaron nan na faɗa miki cewar maraya ne, idan ba ki manta ba; babarsa ce ta ba ni kuɗin da na miki yankan sunan Audu...” “Wallahi ba ka isa ba, wato dan kawai uwarsa ta ba ka kuɗi ka sai mana ragon suna, sai na karɓi ɗanta ko ?, na rantse maka da Allah wannan yaron ba zai zauna min a gida ba!” Duk da Zaid ba ya hayyacinsa sosai, amma yana iya tuna yanda matar kewa mijinta masifa da bala'i, ya na iya tuna yanda ta haƙiƙance kan ba zai zauna da ita ba. Tun bayan da ya fuskanci cewa Aliyun da ya rage masa ya bar duniya, rayuwarsa ta shiga halin ƙaƙa na ka yi. Ya ji gaba ɗaya ya gaji da duniyar, babu abun da ya fi buƙata sama da mutuwar shi ma, ya ji cewar yana son ya mutu kamar Momma da Aliyu, tun da da ma su ne kaɗai gareshi, to ga shi ya rabu da su, to ina zai sa kansa?. Ba dan Malam Ila ya so ba, sai dan babu yanda zai iya, ya ɗauki Zaid ya mayar da shi gidansu na da, amma kullum sai ya kawo masa abinci da ruwan rubutun da yake karɓo masa a gun wani malami mai almajirai da yasa a yi masa, don ya temaka masa wurin dangana da halin da ya shiga ciki. Safe, rana, dare, ba ya taɓa tsallakewa, har takai ga Zaid ɗin ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya, amma yanayinsa da ɗabi'unsa duka sun sauya, ba ya son yawan magana, ba ya son fita, ba ya son shiga jama'a. Ya koma rayuwar ƙunci. Ƙarshe ma ya yanke shawarar barin gidan. Rana tsaka Malam Ila ya shigo gidan kawo masa abinci amma ya nemeshi sama ko ƙasa babu alamarsa. Ya ɓata ɓat! Kamar almara. Ranar da ya gudu cikin garin kano kawai ya bazama, ya kwana a titi, kafin da safe ya ci gaba da yawatawa. Har Allah ya kawo shi rumfar wata inyamura me ƙosai, sunanta Ebere, tana da marainiyar yarinyarta Rhoda, da mijinta ya mutu ya bar mata. Ganinta da Zaid na farko Allah ya saka mata tausayinsa, hakan yasa ta kira shi. “Menene sunan ka ?” Ta tambaya cikin gurɓattaciyar hausarta. “Zaid” Zaid ya amsa mata kansa a ƙasa. “Kai maraya ne ?” Sai ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Ni maraya ne, ba ni da kowa” Maman Rhoda ta waiga ta kalli 'yarta Rhoda dake zaune a raufar ta na wasa. “Za ka zauna da mu?” Zaid ya ɗago da kansa ya kalli matar, sannan ya kalli 'yarta, a take ya ga sun rikiɗa a idonsa sun koma masa Momma da Aliyu. Ba jayyaya ta amince mata, a ranar tare suka wuni a rumfar saida ƙosan nata, bayan dare ya yi ta ɗauke shi da Rhoda 'yarta suka tafi gidanta. Gidan ba wani babba ba ne, amma nata ne, kuma mallakinta, ɗaki ɗaya ta bashi tace masa ya yi zamansa, daga yau shi ma ɗanta ne, kuma ba ta hana shi yin addininsa ba, zai iya ci gaba. Tun daga wannan ranar Zaid ya yi sabin ahali, ga su dai ba musulmai ba, amma sun nuna masa karamci da hallacin da ya kamata a ce 'yan uwansa musulmai ne suka nuna masa. Maman Rhoda ta mayar da shi kamar babban ɗanta, Rhoda kuma ta ɗauke shi a matsayin wa, sai suka koma kamar 'yan biyu, duk da shi Zaid ɗin ya fita shekaru, amma hatta da kaya iri ɗaya suke. Maman Rhoda ta saka Zaid a makaranatar su Rhoda, sannan ta biya masa kuɗin shekarun da zai yi har ya gama makaranatar kamar yadda ta yi wa Rhodan ita ma, don tace akwai mutuwa, ba ta son ta mutu ta barsu cikin wani hali. Kullum da safe Maman Rhoda za ta haɗa kayan ƙosanta. Kuma tare da su Zaid ɗin take tafiya, idan suka je suka aje mata kayanta a rumfar da ta saba yi, sai su wuce makaranta idan a cikin sati ne. Bayan sun taso kuma kai tsaye can rumfar tata za su wuce, ba su suke dawowa ba sai rana, idan sun dawo da rana za su zauna su huta, idan suna da wani aikin yi su yi, idan kuma ba su da shi sai su hau aikin haɗa ƙosan yamma. Yamma na yi za su ƙara komawa, ba sa dawowa sai wajajen sha ɗaya, wani lokacin ma Rhoda tun a can take fara bacci, sai dai Zaid ya goyota su dawo gida. Zaid ya sake da su sosai, ya na rayuwa cikin farin ciki, dan Maman Rhoda ba ta rage shi da komai ba, ko azumi ne zai

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112