Chapter 49
Chapter 49
kike?” Raja ya tambaya. “Bacerlona” “Aaa!, ki ce ke tamu ce, mu 'yan PSG ne (Paris Saint Germain)” Cewar Rhoda. Daga haka kuma sai hirar tasu ta koma ta ball, har suka iso bakin titi hirar ba ta ƙare ba, sosai Raja ya yi mamaki jin yanda Rabi'an tasan abubuwa da dama game da ball, kuma ya yi mamakin jin yanda tace musu ta na son buga ball, dama ce kawai ba ta samu ba. Su suka tsaida mata mota ta shiga, sannan suka juyo,suna tafe suna 'yar hira. Kamar daga sama suka ji wata murya na faɗin. “Hello!” Hakan yasa suka kalli inda sautin muryar ya fito. Wata yarinya ce tsaye a gabansu, sanye cikin uniform ɗin makarantar Brickhall, a ƙiyasin shekaru ba za ta wuce 17 ba. “Hy” Rhoda ta amsa mata, yayin da idanuwan Raja ke kallonta ƙasa-ƙasa. “Ko zan iya sanin sunanka Bro?” Mamaki ya kama Raja, to me za ta yi da sunansa?, tukunna ma waye ce ita?. “No, kada ka damu fa, ni ba 'yar yankan kai ba ce...” Maganar tata ta bawa Raja dariya, hakan yasa suka murmusa a tareshi da Rhoda, ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama. “Sunana Raja, ke kuma fa?” “I'm Mishal” Mishal ta faɗi tana gyara zaman jakarta dake goye a bayanta. “Me yasa kike son sanin sunana?” Sai kuma ta yi shiru, da ma gajiya ta yi da jiran zuwan Kuliya, hakan yasa kawai ta fito ta fara tafiya da ƙafarta, kuma a kan hanyar ta ci karo da wannan me kama da Kuliyan, shi ne ta tsaya don ta samu ta masa magana, wata ƙila za ta tabbatarwa da kanta abun da take san sani. “Akwai wani yaya na da yake min kama da kai that's all” Ta zaɓi da ta masa wannan ƙaryar, don a ganinta wata ƙila ita za ta fi bada ma'ana, saboda babu yanda za'a yi ta faɗa musu cewar da mijinta yake kama, don ba ma lalle su yardar da cewar ita ɗin matar aure ba ce, to taya ma za'ayi su yarda?. Ba ƙaramin duka maganarta ta yi wa Raja ba, wai meke shirin faruwa da shi ne?, farko Rabi'a, yanzu kuma wannan yarinyar na faɗa masa cewar akwai wani ɗan uwanta me kama da shi, sai dai kuma shi yasan basu da wasu 'yan uwa na kusa. Da ace ma Rabi'a ce za ta faɗi hakan sai ya yarda, amma shi yasan cewa su ba su haɗa jini da shuwa arab ba, saboda daga gani wannan yarinyar jinin shuwa arab ce, haka zalika kuma yasan cewa duk wanda ya mutu babya dawowa, Allah ya riga ya amshi rayuwar Aliyunsa, hakan tasa ya dangana, ita ma Rabi'an abun da ya sa yake bibiyarta ba komai ha ne face son sanin wani abu game da danginsa. “Ya alaƙarku take da yayan naki ?” Rhoda ta tambayi Mishal, dan babu labarin Raja da ba ta sani ba. “Uwa ɗaya uba ɗaya” Ta amsa tana kallon fuskar Raja, yanda ya yi da fuskar tasa kaɗai yasa ta tabbatar da abin da take zargi, tabbas babu makawa, duk yanda aka yi wannan ɗan uwan Kuliya ne, amma me ya shiga tsakinsu har suka rabu haka?, tana buƙatar sani. “Ni zan wuce, Bro and Sis sai an jima” Da kallo suka bi bayanta har ta fara tafiya. “Yarinyar nan akwai shirirta” Rhoda ta faɗi tana 'yar dariya. Raja da ya gama tabbatarwa da wannan yarinyar ba a kan Aliyunsa take magan ba ya mata murmushi kawai, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, kafin ya ci gaba da tafiya, hakan yasa ita ma bin bayansa. Mishal na tafe tana saƙe-saƙe a ranta, tana son sanin abin da ke tsakanin waɗanan mutanen biyu masu kama ɗaya, sai de kuma suna da mabanbantan halaye, tsayuwar da ta yi da wannan Rajan ba ta fi ta minti biyar ba, amma ta gane banbancinsa da Kuliya, wannan yana da fara'a, yayin da Kuliya ba shi da ita, wannan yana da sakin fuska, fuskar Kuliya kam kullum a ɗaure take, sannan muryar wannan akwai sanyi da taushi, yayin da ta Kuliya ke cike da hargagi da faɗa, ko maganar arziƙi yake da mutum sai ya maka tsawa, bare kuma a ce ransa ya ɓaci. Sai kawai ta yi murmushi tana jinjinawa kanta, na sanin halayen Kuliyan a kwana huɗu kawai da suka yi tare, duk da ba wani zama suke sosai ba, haɗuwarsu ba ta wuce uku a rana, da safe kafin ta tafi makaranta, sai kuma idan ya zo ɗaukanta, sai da daddare idan ya dawo. Kuma kwana biyu ma ba sa haɗuwa da daddarren dan sai ta yi bacci yake dawowa. KULIYA POV. Cikin matsanancin gudu yake tuƙa motarsa, tunawa da ya yi ya bar 'yar mutane ta na jiransa, aikin da yake ne ya sha masa kai, har ya sa ya manta da lokacin tashinta daga makaranta, kuma tun a sanda ya fito daga headquarter ya riga ya yanke hukuncin cewa dole sai dai ya nema mata driver, don ayyukan dake gabansa sun fi ƙarfinsa, idan yau ya tuna a kan kari, gobe ba llalle ya sake tunawa ba. Amma idan ya sama mata drivern, aikin zai masa sauƙi, kuma ko ba komai shi ma zai huta, saboda a kullum sai ya dakatar da aikinsa yake iya samun zarafin zuwa ɗaukanta. Wata yarinya ya hanga a gefen titi, kamar ita kamar ba ita ba, gashin kanta da kuma farar fatarta da ya gani ne ya tabbatar da cewar ita ce, ya kamata ace ya mata magana kan fita babu ɗankwalin nan ma, don a matsayinta na matar aure hakan be dace da ita ba. Parking ya yi a kusa da ita, yanda ta tsaya tana kallon motar tasa ya sa ya gane cewa ita ma ta san cewar shi ne a cikin motar, to amma me take jira da taƙi zagayowa ta shigo?, ko jira take sai ya mata magana?. Kusan shuɗewar muntina goma suna a haka, ita tana tsaye, ta kafe motar da ido, shi kuma ya kasa mata magana ta shigo, ganin kamar tana shirin ɓata masa lokaci ne yasa ya zuge glass ɗin setinta ƙasa. Sannan ya kalleta. Sai da ya ɗaga ƙafaɗarsa kafin yace. “Za ki iya shigowa idan kin gama tsayuwar!” Mishal ta yi murmushi tana zagayowa, aka ce da ba ya ji, sarai ta gane shi, amma jira take ta ƙure masa miskilancin da yake ji da shi, duk da Anti Adawiyyanta ta ce kada ta na masa irin haka, amma ta lura da idan ba haka ta masa ba, ba zai dena mata wannan abun ba. *No.181, Guzape, Abuja....* *08:30pm* MISHAL POV. Zaune take a ɗakinta, assignment ɗin da aka basu take ta ƙoƙarin yi. Ƙofar ɗakin da aka turo yasa ta ɗa ga kanta ta kalleshi, don tasan daga ita sai shi ne kawai a gidan, kuma ta yi mamakin dawowarsa da wuri. Kamar yanda ta saba ganinsa, sanye yake cikin baƙaƙen kaya. Wai shi ba shi da wasu kaya sai baƙaƙe ne?, kullum sai ya yi ta saka baƙin kaya kamar me shirin zuwa jana'iza #AbuAswad Sai kawai ta yi dariya a sanda zuciyarta ta raya mata sunan, ABU ASWAD! sunan ya karɓe shi kuwa. A hankali Kuliya ya saki hannun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112