Skip to content

Chapter 107

Chapter 107

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

zaune kan darduma. Ba ta san me take ba,amma bisa ga dukkan alamu ba sallah take ba. Sai ta shiga cikin ɗakin tare da nufar inda take. “Ƙanwata!” Ta kira sunanta tana dafa kafaɗarta, firgiyar da da Mishal ɗin ta yi ya ankarar da Rabi cewar tunani take. “Kin idar da sallahr?” Mishal ta gyaɗa mata kai. “Mishal! A yanzu Aliyu ba ya buƙatar kukanki ko damuwa, addu'a kawai za ki masa, da yardar Allah zai tashi!” Wata siriryar ƙwalla ce ta biyo kuncin Mishal. “Anti Adawiyya idan na tuna maraicina sai na ji kamar zan fasa ƙara. Ba ni da kowa fa, Aliyu shi kaɗai ne ya rage min, bayan shi ban da kowa. Idan ya mutu kuma ya zan yi?!” Da sauri Rabi ta girgiza mata kai. “Insha-Allah zai warke, zai tashi kin ji?” Ta faɗi tana jan Mishal zuwa jikinta. Kafin ta saketa a hankali tana share nata ƙwalla. “Mu je mu ci abinci...” Mishal ta girgiza kanta. Rabi ta zare mata ido tana faɗin. “A gidana ba'a min musu, dan haka salin-alin ki tashi mu je mu ci abinci” Duk da halin da Mishal ke ciki be hanata yin murmushi ba. Tashin ta yi suka fita, a falon suka zauna a kan carpet suka fara cin abincin. Ko rabi ba su yi ba, Rabi ta ji amai na taso mata. Dan haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta da gudu. “Lafiya?” Mishal da Rhoda suka faɗi a tare suna miƙewa tare da bin bayanta da kallo. “Zauna ki ci gaba da cin abincin, ni zan je na dubata” Cewar Rhoda. Ba dan Mishal ta so ba, haka ta zauna tana ta kallon ƙofar ɗakin Rabin. “Sannu! Sannu kin ji... Sannu!” Rhoda ke ta jerawa Rabi sannu, wadda ke ta amayar da taliyar da ta samu shiga cikin. Bakinta ta wanke tana jingina da bango, bayan da ta gama aman. “Baki da lafiya ne?” Rabi ta girgiza kai tana dafe cikinta. “To sannu” Falon suka dawo, inda Rabi tace ita fa ta ƙoshi, dan haka su su ƙarasa cin abincisu. Babu yadda Rhoda ba ta yi da ita ba kan ta daure ta ƙara abincin, amma tace ita ta ƙoshi. Haka suka ƙyaleta su ma suka ci gaba, da ƙyar Mishal ta iya cin abincin da yawa. Kafin Rabi ta ɗauke trayn ta kai shi kitchen, ta fito tana faɗin. “Sai mu kwanta ko?” Rhoda ta miƙe tana faɗin. “No, ku de ku je ku kwanta a ɗaki, ni a nan zan kwana!” Rabi ta girgiza kanta. “A'a... Ke ma zuwa za ki yi mu kwanta, gadon fa babba ne, zai ɗaukemu mu uku” “Ok, mu je” Da haka suka koma ɗakin, gadon kuwa tas ya ɗaukesu su ukun, har da sauran space. Rabi da Rhoda ne kawai suka yi bacci, ban da Mishal ɗin da ta kwana ido buɗe. Dan ba ta jin za ta iya baccin, hakan ya sa daren ya mata tsawo, fiye da sauran dararen da suka shuɗe a rayuwarta. *Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja* ZAID POV. Zaune yake a kan kujera ɗaya dake cikin ɗakin da Aliyu ke kwance. Ya kafe Aliyun da ido, kamar idan ya kira sunansa zau amsa. Hannunsa ya kai ya shafa sumarsa tun daga gaba zuwa baya. Sannan ya dawo da hannun nasa kan bakinsa. Aliyun dake kwance kan gadon marasa lafiya, ba ya iya numfashi sai da temakon na'urar numfashi. Ba ya jin zai iya ko da rintsawa. Dan gani yake kamar idan ya kumshe idonsa na minti ɗaya, Aliyu zai iya ɓacewa. Haka ya ci gaba da zama a wurin, har zuwa asuba. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *27* *END* ~~~ *“How sad to miss someone, who you know doesn't miss you...* *** *No.86, Garki 2, Abuja...* RABI POV. Tun da ta tashi sallahr asuba bata koma bacci ba. Amma da Mishal da ba ta samu bacci jiya da daddrae ba ta koma baccin. Sai Rhoda a bata farka ba. Gyaran gidan ta shiga yi. Bayan ta gama kuma ta ɗora girki, bayan nasu wanda za suci, har da na su Zaid ta girka, ta juye musu nasu a cikin was warmers masu kyau, ta saka a basket ta aje. Nasu kuna ta kai kan danning ta jera. Ɗakinta ta koma, ta je ta taso Mishal da Rhoda, tace musu su tashi su yi wanka. Ita kuma ta fice ta shiga ɗakin Zaid. A can ta yi wanka, ta ɗauki ɗaya daga cikin kayanta da suke can ta saka, ta fito. Sanda ta koma ɗakin nata, Mishal ce a banɗakin tana wanka, ita kuma Rhoda ta yi wanka tana shafa mai. “Rhoda kaya na kuwa zai miki?” Ta tambaya tana buɗe lokokinta. Rhoda ta juyo ta kalleta. “Ai ba zai iyu na saka kayanki ba ma, yau za mu shiga kotu, dan haka kayan aiki ya kamata na saka, so ba sai na sauya kaya ba,zan tafi da wannan, daga can kuma sai na wuce Kaura” Cike da gamsuwa Rabi ta rufe lokarta, bayan da ta ɗaukowa Mishal wata doguwar rigar atamafa da take da tabbacin za ta mata dai-dai, dan kansu ɗaya da wadda ta bata ta saka jiya. Zama ta yi a bakin gadonta,tana buɗewa wayarta dan kiran Zaid, sai de kuma wayar har ta yi ringing ta katse bai ɗaga ba. Sai kawai ta aje wayar, don ta san da ma balalle ya ɗaga ɗin ba. A lokacin Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta ɗaure da towel. “Ga kaya, sai ki sauya” Rabi'a ta faɗi tana mata nuni da doguwar rigar atamfar dake aje a kan gado, Mishal ta kalli kayan, sannan ta ƙaraso ta ɗauka, ta koma banɗakin dan sakawa. Cike da jin tausayinta Rabi ta girgiza kai, idanunwata ba ƙaramin kumbura suka yi ba, saboda tsabar kuka.Wayar Rhoda ce ta yi ringing, hakan ya sa ta ɗaga wayar tana fita waje, dan kiran daga headquarter su ne. Bayan wani lokaci, Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta sanye da doguwar rigar. Ba tare da ta saka komai a jikinta ba ta zauna a kusa da Rabi. Fuskar nan cike da damuwa, kana ganinta za ka san cewa tana cikin tashin hankali, idonta ya jeme, fuskar nan ta yi jajir. “Ga hijabi ki saka” Kallon hijabin ta yi, kafin ta karɓa tana miƙewa tsaye. “Mu je mu ci abincin to” Rabi ta faɗi tana dafata, bayan da ta gama saka hijabin. A falo suka haɗu da Rhoda, wadda ta gama wayar da ta tafi yi, daga nan suka wuce danning suka ci abinci. Kafin suka shirya fita daga gidan. *Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja.* KULIYA POV. Zaune yake daga bakin gadon marasa lafiyar dake dakin da aka kwantar da shi. Ya zuro ƙafafunsa ƙasan gadon. Jikinsa sanye da kayan marasa kafiya da ake bawa pertinent ɗin asibitin. Hannunsa na dama, sanye cikin arm sling. Daga gefen damansa kuma, Zaid ne zaune yake kallonsa ta gefen ido, dan jinsa yake kamar wani baƙo a gurinsa. A ɗazu bayan da ya dawo daga masallacin sallahr asuba, ya tarar da Aliyun ya buɗe idonsa, amma kuma yana kwance a kan gadon, hakan ya sa ko ɗakin ma bai ƙarasa shiga ba ya juya da sauri ya tafi

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112