Skip to content

Chapter 64

Chapter 64

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

wanda ya yarda” Har yanzu dai wannan shiriritar na nan, kuma kafin yace a'a, har ta kama hannunsa ta shiga jansa, sai ya riƙe kalamansa ya shiga bin bayanta. “Kai shashashu! Na ce muku an min aure kun musa ko? To ga ku ga mijinawa, sai ku tambayeshi ku ji!” Abun da ta faɗi kenan a class ɗin nasu cikin ɗaga murya, kasancewar lokacin break ne, kowa na harkar gabansa, ido ya dawo kansu gaba ɗaya, sai kallon kallo ake, wasu na mawa mijin Mishal ɗin kallon sani, don ya na musu kama da wannan me sharar, sai masu masa kallon sani, saboda kullum idan an tashi suna ganinsa tsaye a tsallaken makarantarsu, wasu kuwa ma basu san shi ba. *No. 213, Naf belly, Asokoro, Abuja.* “Wallahi Aliyu ba ni da masaniya kan abun da su Karima suka aikata!” Anna ke faɗin hakan cikin hawaye, bayan da Kuliya ya zo ya na sanar da ita haukan da Karima da kuma Siyama suka je gidansa suka aikatawa Mishal. Kuliya ya kamo hannayenta ya riƙe. Bayan ya bar Brickhall kai tsaye gidan Annan ya nufo. “Na sani Anna. Na san ba za ki aikasu su yi wa matata haka ba, amma ina son na sanar da ke da ki jawa kowaccensu kunne, kan kada su ƙara taka ƙafarsu cikin gidana, jiya ma girmanki da darajarki suka ci, ba dan haka ba Wallahi ba zan barsu ba” Anna ta share hawaye. “Ba komai Aliyu, tashi ka tafi aikinka, zuwa yanzu na san ka makara, ka je kawai, ni na san matakin da zan ɗauka!” Ya karkatar da kansa gefe. “Ba za ki dena kukan ba?” Anna ta ɗan yi murmushi tana share wani hawayen. “Na dena, ka je kawai” “Shikenan” Ya faɗi ya na miƙewa, har ya fice Anna na kallonsa, ta san abun da za ta yi. Don ta zubawa su Karima ido suna ta haukansu ba wai don ba za ta iya taka musu birki ba ne, ba ta san cewa haukar tasu ta ƙamari ba, amma ba komai, Allah ya kaimu gobe, za ta yinwa tufkar hanci. *Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja.* Da gudu wata nurse ta fito daga wani ɗaki da aka kwantar da wata mara lafiya da ta baƙunci asibitin nasu a safiyar yau, hannunta na dama ɗore a bakinta, a ƙoƙarinta na tare kukan dake son cin ƙarfinta, ta jingina da jikin bango tana kallon ƙofar ɗakin, a hankali ta zame zuwa ƙasa, kukan da take ta yunƙurin riƙewa ya fito da ƙarfinsa. Tun da uwarta ta kawota duniya ba ta taɓa ganin tashin hankali irin wanda ta gani yau ba, ta na jin labarin fyaɗe, amma ba ta taɓa ganin wanda aka yi wa fyaɗe ba sai yau, an ce mata idan ta fara aiki sai ta gamu da abun da zai sa ta kuka, a wancan lokacin da aka faɗa mata dariya ta yi, don ita ba ta hango yiyuwar hakan ba, sai a yau ta yarda da abun da aka faɗa mata, kuka take sosai har ta na dafe ƙirjinta. Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, likitan da suka shiga tare da shi ya fito ya na sharar ƙwalla, kafin ya kalli nurse ɗin, shi kansa da ya kwashi tsawon shekaru ya na aikin bai taɓa ganin abu makamancin wanda ya gani yau ba, bare ita da ta ke sabuwa a aikin. “Ke Sakina! lafiyar ki kuwa?” Wata ƙawarta ta tamabaya, a sanda ta biyo corridorn ta ga ƙawar tata zaune a ƙasa tana kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa, juyawa ta yi ta kalli likitan, shi ma duk jikinsa ya yi sanyi, kansa a ƙasa kamar da aka ce shi ne ya aikata fyaɗen. Hannunta ta kai ta kamo ƙawar tata tana miƙarta, tare da share mata hawaye, amma Sakinan sai ta ƙwace fuskarta ta na komawa gefe. “Dan Allah Kausar ki bar ni na yi kuka. Bar ni na koka da abin da na gani. Kausar wasu mazan ba su da adalci, ba su da tausayi!” Ta ɗaga hannunta tana nuna mata ƙofar ɗakin. “Shi ga ki ga abun da suka yi wa wata yarinya. A shekaru dai na san yarinyar ba za ta wuce 19 ba, amma ki je ki duba ki ga yanda suka mata fyaɗe cike da rashin imani, mutum biyar Kausar, mutum biyar ko sama da haka ne suka haike mata!.Kuma ba su barta da wannan tambon ba, sai da suka ƙara mata da wasu raunuka a jikinta, gefen fuskarta da kuma kanta duk sun fasa mata, yanzu haka yarinyar ta shiga doguwar suma!” Ita kanta Kausar ɗin sai da gabanta ya buga da mugun ƙarfi, don za ta iya cewa wannan ɗin sabo abu ne da ya shigo asibitin nasu. “Me ya sa Kausar?. Me ya sa mu ba mu da 'yanci?, Kowa sai ya taka mu ya wuce yanda yake so. Me ya sa wasu mazan ba sa ganin mata da kimi?. Me yasa?... Sai zuwa yaushe ne za mu tsira?, sai zuwa yaushe?!”. *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja* RAJA POV. Zaune yake a ɗakinsa, ya yi tagumi da duka hannayensa biyu, abun duniya ya bi ya isheshi, musamman yau da ya ga Rabi'a ba ta zo ba, abun ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, shi fa burinsa shi ne ya samu ya ganta don ya mata bayani, zai gabatar mata da kansa a ainahin yanda yake, zai faɗa mata gaskiyar komai a kansa, amma yau haka ya ƙaraci tsayuwarsa a ƙofar gate ɗin ba tare da ya ga gilmawarta ba. Ƙofar ɗakin aka buɗe, sannan Rhoda ta shigo hannunta tiƙe da wayarsa. Kansa kawai ya ɗaga ya kalleta ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama. “Alhaji Bala ne yake ta waya. Yace ya na buƙatar kayansa cikin gaggawa” “Mtswwww!” Ya ja tsakin ya na kawar da kansa, shi ba ta Alhaji Bala yake ba, don matsalar Alhaji Bala sifili ce a wurinsa, babba kuma shirgegiyar matsla gareshi ita ce RABI'A!. Ganin hakan ya sa Rhoda zama kusa da shi, sannan ta dafa ƙafaɗarsa. “Na san halin damuwa da kake ciki, amma ya kamata ace ka sameta ku yi magana, ka faɗa mata gaskiya, wata ƙila ta saurare ka” Fuskarsa ya shafa da hannayensa. “Yau ba ta zo ba fa” Ya faɗi cikin wata murya me sanyi. “Wata ƙila ta zo, ta ɓoye ne kawai dan kada ka ganta” Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, ƙwarai, hakan za ta iya kasancewa, amma me ya sa shi bai yi tunanin hakan ba?. “Ki na ga zan iya shiga cikin makarantar?” “Me zai hana?” Sai ya gyaɗa kansa, ya na hangowa kansa mafita a cikin kalaman Rhoda. *No.181, Guzape, Abuja...* *07:00 PM.* MISHAL POV. Tsaye take a kitchen tana juya stew ɗin da take dafawa, duk da yau girkin a makare take yinsa, saboda makarar da ta yi wurin dawowa gida. Ba tare da ta san lokacin da ya shigo ba, ta ji muryarsa a bayanta. “Ana san magana da ke!” Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya na tsaye daga bakin ƙofa, kallonsa da ta yi a yanzu shi ya tuna mata da shirman da ta yi masa yau da safe a school ɗinsu, don haka ta yi ta nuna

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112