Chapter 28
Chapter 28
ta gyaɗa kanta tana tuna zancen da suka yi jiya, sanda ta tambayeta a ina ta ji rauni. “To ai na faɗa miki cewar ya cillar da wallet ɗinsa... Na ganshi ɗazu, kuma na bashi kayarsa, shi ne ya fitar kuɗin ciki gaba ɗaya ya bani, ya ce na yi kuɗin mota...” Ta ƙarshe tana miƙa mata kuɗin. Bakin Anti Saratu buɗe ta karɓi kuɗin, ita da kanta ta shiga lissafawa. “Rabi!... Dubu hamsin da uku ne fa?” Anti Saratun ta faɗa ido waje, ita kanta Rabin sai da ta yi mamaki, duk da dama tasan kuɗin ba kaɗan ba ne. “To da huɗu ne ma, tun da kin ga har kifin dubu na siyo” Ta faɗi ta na miƙewa tsaye, tare sa nufar jakarta, ta fiddo da kifin dake duƙunƙune cikin leda, ta dawo ta zauna kusa da Anti Saratun ta miƙa mata. “Rabi... Ko dai ya na ciki ne ?” Ta tambaya a sigar zolaya, Rabi ta yi murmushi tana hango rashin tabbatuwar hakan, don ko da wasa ba ta hango hakkan ba, babu ma ta yanda za ayi hakan ta faru, dan akwai banbanci tsakaninta da shi, wani irin banbancin da take ganin tazararsa kamar, ta Mutum da lokacin mutuwarsa, dan mutum bai san lokacin da zai mutu ba. Haka ita ma ba ta san adadin tazarar dake tsakaninta da shi ba. Kuma ita ta na ganin wata ƙila shi ma yana mata kallon wadda take kama da shi ne, ko kuma yarinyar dake buƙatar temako, ba ta san shi ba, ba ta san ya rayuwarsa take ba, amma tana da tabbaci kan shi ba sa'anta ba ne, akwai tazara me tarin yawa tsakaninta da shi. Abun da ba ta sani ba shi ne, wannaan tazarar da take gani ta kusa zama kusa, wata iriyar kusa da za ta bata mugun mamaki. Amma kuma kafin faruwar kusan, sai wasu ƙaddarori sun gifta a tskani. Ita ta buɗe musu ledar kifin,suka ci tare, tana tambayar Anti Saratun; kan yaya za su yi da kuɗin?. “Abun da zai faru kawai zan aje miki su a wurina, idan kina buƙata sai kimin magana, ni kuma na baki...” Rabi ta yi dariya tana kai wani kifin bakinta, yau tana cikin farin ciki, wanda ba za ta iya cewa ga dalilinsa ba. RAJA POV. Tsaye yake a gaban mutumin da ke amsa sunan ALHAJI BALA. Yayin da shi ma Alhaji Balan ke kallonsa. Fuskar Alhaji Balan na ɗauke da murmushin alfahari, dan sosai yake alfahari da Raja, though wannan shi ne karo na farko da suka fara haɗuwa, amma ayyukan da yake dominsa suna isowa kunnuwansa. Yayin da shi Rajan yake kallonsa da wani gutun murmushi, salihar fuskarsa na wani irin haske da ba ka ce na miye ba, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Alhaji Bala ƙasa-ƙasa. Daga shi sai Rabbil izzati suka san abinda yake tsarawa a cikin kansa. Suna tsaye ne a katafaren falon gidan Alhaji Balan, wanda ke ɗauke da maka-makan set ɗin kayan da kallo ɗaya za ka musu ka shaida tsadarsu. Rajan na sanye cikin wani green khaki trouser, sai baƙar crew neck sweater, ƙafafunsa sanye cikin canvas baƙaƙe. Alhj Bala ya ɗaga hannunsa na dama, tare da bubbuga kafaɗar Raja, yana ƙara faɗaɗa murmushin kan fuskarsa. “Zauna mana ZAKI!” ZAKI?!, Bai yi ƙarya ba, dan ya na amsa wannan sunan a wata duniya, wata duniya can da ban, wanda ta zama sanadiyyar kasancewarsa a wannan rayuwar. A hankali ya juya ya kalli Rhoda dake tsaye a bayansa, sanye cikin irin kayan dake jikinsa, kalabar attachment ɗin dake kanta ta sauƙo har kan kafaɗunta. Da ido ya mata alama da ta zauna, zaman ta yi a kan kujerar dake kusa da ita, sannan shi ma ya zauna a kusa da ita, dan kujerar me ɗaukar mutum biyu ce. Alhaji Bala ya kalli yaransa uku dake zaune a falon, sannan y ce. “Ku ba mu wuri, za mu gana...” Cike da girmamawa suka tashi suka fita, ya rage daga shi sai Raja da Rhoda. “Ita ma wannan yarinyar taka ya kamata a ce ta fita ko?, Dan maganar da za mu yi sirri ce!” Alhaji Bala ya faɗi yana kallon Rhoda, kamar me neman amsa a wurin Rhodan, ya juya ya kalleta, ita ma shi take kallo, kafin ya juya ya kalli Alhaji Bala. Ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, sannan wannan innocent voice ɗin nan nasa yace. “Na fahimta, amma ba za ta iya fita ba, she is my other half, komai zan yi sai na sanar da iya, ba na taɓa yin wani abu ba tare da saninta ba... So you can say what you want at her present” Alhaji Bala ya gyaɗa kansa, sannan ya gyara zaman malum-malum ɗin jikinsa, alamun dai maganar da za ta fito daga bakinsa babbace... Raja da Rhoda suka miƙe a tare, bayan da Alhaji Baka ya kawo ƙarshen maganarsa, hannu Alhj Bala ya miƙawa Raja suka gaisa. Daga haka suka yi sallama suka kama hanyar fita daga falon. Ƙofar falon ce ta buɗe, hakan yasa Raja da Rhoda tsayawa. Wani mata shi ne ya shigo, yana binsu da kallon ɗai-ɗai, daga Rajan har Rhodan sun san waye, USMAN!, ɗan Alhaji Bala na fari. Babu wanda ya kula shi, har suka raɓa shi suka fice. “Ya aka yi yanzu kuma ?” Alhaji Bala ya tambaya yana kallon Usman ɗin, Usman ya sosa ƙeyarsa yana kallon babansa. “Kuɗi nake buƙata” “Dama na sani, ka je, zan saka maka a account...” Ba ko godiya, haka ya gyaɗa kansa sannan ya juya ya bar falon. Ya na saka ƙafarsa a wajen ɓangaren mahaifinsa ya fiddo da wayarsa daga aljihu, ya aika wa abokinsa Bash kira. “Usee boyyyy!... So Sup? (To yaya ake ciki?)” Muryar Bash ɗin ta faɗa ta cikin wayar. Usman ya saki murmushi, har fuskarsa na haskawa ta cikin hasken fitulin dake haskawa a harabar gidan nasu, kasancewar lokacin dare ne. “An samu kuɗaɗen nan, a tanadar mana babes ɗin kawai, dan gobe akwai chilling” “Oboy!, that's my gee, kar ka damu, ka kwantar da hankalinka kamar kana jirgin sama mai ya ƙare, akwai zafafan 'yan mata, masu tafiya kyau na zuba, kai dai kawai sai na ganka goben” Daga haka wayar ta katse, sannan ya jefa wayar aljihunsa. Wannan shi ne halinsa, ainahin halinsa da kowa ya sanshi da shi, shaye-shaye, neman mata da kuma bin abokan banza, shi ya sa yake ɓarin kuɗi, kuma mahaifinsa ba ya hanashi kuɗin, a duk sanda zai tambaya sai an bashi. KULIYA POV. A hankali yake saka kayansa cikin ƙaramar jakarsa ta goyon baya. Yau aka sallame shi daga asibiti, don haka ya shirya tsaf, don barin asibitin. Ya riga ya tsara tarin abubuwan da zai gabatar a cikin kasan, ya riga ya tsara kaf, abubwan da zai gabatar bayan ya bar asibitin. Ba zai sararaba sai ya ga ƙarshen aikin da ke gabansa, shi matsalarsa ɗaya, fushin da Anna ke yi da shi, don tun bayan da ya kwanta jinyar kusan kwana huɗu kenan, amma ba ta zo ta duba shi ba. Tun ranar farko da ta zo ta gama masa wankin babban bargo ba ta ƙara dawowa ba. Sai kuma ita, itan da kamanin fuskarta suka manne a cikin tunaninsa, dai-dai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112