Skip to content

Chapter 44

Chapter 44

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

ta nufi ɗakinta, tunani da yawa birgit a ranta, wanka ta yi, ta sauya kaya zuwa wani distressed jeans, da wata peach long sleeves tees, ta saka sliders ɗinta ta fito, kanta ko ɗankwali babu, sai band ɗin da ta saka a tsakiyarsa. A parlo ta zauna tana kallo, har zuwa lokacin da me aikin ta gama aikinta. “Ranki ya daɗe ni zan wuce”. Mishal ta janyo idonta daga kan Tv ta kalleta. “Ina za ki je?” Matar ta ɗan sosa ƙeya tana faɗin. “Gidan Anna zan koma, ai da ma nan ɗin shara kawai nake zuwa na yi” Mishal ta gyara zamanta. “Wacece Anna kuma?” Mamaki ya kama matar me suna Rahila, ta ya za ta auri ɗan mata, kuma tace ba ta santa ba. “Ita ce babar me gidan naki” Babarsa?, kenan ya na da 'yan uwa, to duk yanda aka yi ya san da zaman wannan ɗan uwan nasa. Kuma kafin ta ƙara cewa komai, aka ƙwanƙwasa ƙofar falo, ita ce ta bada izini, me gadin gidan Ilu ya shigo, hannunsa riƙe da ledojin abincin da aka kawo daga restaurant ɗin da suka saba kawowa Kuliya abinci. Har cikin falon ya shigo, ya aje mata abincin a gabanta, sannan ta sallame shi. “Ki zauna mu ci abinci, sai ki wuce” Ba musu Rahila ta amince, ta zauna har Mishal ta miƙo mata abincin, ita kuma Mishal ɗin ta miƙe, ta shiga neman Ayra, har ta samota a kitchen, ba ta fita ba sai da ta bi kitchen ɗin da kallo, babu komai a ciki sai coffee maker da kuma stove, sai kayan shayi. Ko da ta buɗe firdge ma duka kayan gwangwami ne a ciki. Ba tare da ta taɓa komai ba, ta fito ta dawo falo ta shiga cin abincinta tana bawa Ayra. Rahila sai satar kallonta take, wato kowa da kalar yarintarsa, ita kuma wannan kalar tata kenan. Sai ƙarfe 09:00 dai-dai Kuliya ya kamo hanyar barin headquarter, kuma kai tsaye gidan Anna ya nufa. “Ɗazu Rahila take faɗa min cewar yarinyar tana da kirki, dan bata barta ta dawo ba ma sai da suka ci abinci” Cewar Annan, bayan ya isa gidan. Girar Kuliya ta haɗe guri guda, alamun kokwanto. “Wacece Rahila?” Anna ta yi 'yar dariya. “Me aikina” “Oh na gane” Kafin kuma ya sake cewa komai, Siyama wadda ta dawo gidan Anna a yau da safe ta bayyana a falon, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, dan sai a yanzu ma maganar da ya saurara tsakaninta da yayarta ta faɗo masa a rai. Anna ma binta da kallo ta yi, tana mamakin irin halin Siyaman, zuwa yanzu ya kamata a ce ta cire Kuliyan a ranta, tun da ta riga da ta ji cewar ya yi aure, amma duk da haka ba ta haƙura ba, neman wata hanyar da za ta cusa kanta gareshi ma take. Cike da so da ƙauna Siyama ke kallon Kuliya, don ba za ta iya kwatanta yanda zuciyarta ke fama da ciwon sansa ba, a koda yaushe cikin raunata zuciyarta yake, amma hakan ba ya hana sansa ƙara ninkuwa a zuciyar tata, a duk sanda zai yi wani abu don ya bata haushi, to a lokacin yake ƙara burgeta. Kanta a ƙasa ta kama hanyar shiga kitchen, ba wai dan akwai abun da za ta yi a can ɗin ba, sai dan kawai ta shiga kitchen ɗin ta laɓe, ko za ta samu damar sauraron muryar sahibin ranta. Kuliya ya kamo hannun Anna ya matse, a sanda ya tabbatar da Siyama ta bar falon, jin hakan yasa Anna ta tattara gaba ɗaya hankalinta kansa. Ya ɗaga kafaɗarsa, sannan yace. “Anna... Yau na ga wata me kama da Mommana, me kama da Zaid ɗina, kuma me kama da ni!” Wani irin shiru ne ya ratsa falon, yayin da babu ƙarar abun da ke tashi sai na tv dake a kunne, sai kuma ƙarar acn dake fita a hankali, kuma da a ce Kuliya ya kasa kunne sosai, da ya ji sautin bugun zuciyar Anna, yanda take kallonsa kawai shi ne zai shaida masa kalar tashin hankali da mamakin da take ciki. Siyama dake kitchen ta ɗora hannunta a kan bakinta, yayin da zuciyarta ke tambayarta; shin da ma Kuliya na da wasu 'yan uwan bayan Anna?, ita dai haka ta taso ta ganshi a gidan Anna, kuma ce mata aka yi maraya ne da Annan ta samoshi a tsohon gidan marayun da ta taɓa aiki. *Shekarata 2000* Aliyu ne zaune kan wani benci da ke Garden ɗin gidan marayun da aka kaishi, matar da ya saba da ita cikin kwana uku kacal me suna Rahama na aikin share garden ɗin, jifa-jifa Rahaman da tace ya riƙa kiranta da Annan ke masa hira. Sai dai shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ba ya kanta, hankalinsa ya karkarta kan ɗan uwansa da ya shafe kwana uku ba tare da shi ba. Babu kowa a garden ɗin, daga Annan sai shi, saboda gaba ɗaya yaran gidan na ajin ɗaukar karatun Alkur'ani. Wata iriyar ƙara da ta cika wurin ce ta sa Anna da Aliyu firgita, a kiɗime suka dubi ginin wurin. Wanda ke taci da wuta. Wata kalar ƙara haɗe da salati Anna ta saki, tunawar da ta yi kowa na gidan na cikin ginin, babu kowa a waje sai ita da. Wannan ɗan marayan Allahn. A dugunzume ta ja hannun yaron suka yi waje, sannan ta shiga neman ɗauke, har aka samu wanda ya kira 'yan kwana-kwana, aka zo aka kashe wutar, amma babu wanda ya tsira a cikin gidan, tun daga kan yaran gidan har ma'aikatan. Ba Anna kaɗai ba, hatta da Aliyu da bai jima da zuwa gidan ba sai da abun ya taɓashi, haka gwamnati da sauran masu faɗa a ji suka riƙa sintiri a gidan marayun, kafin daga bisani aka rufe shi. Tun bayan faruwar lamarin Anna ta ɗauki Aliyu suka koma gidan wata ƙawarta a nan garin Kano, kasancewar da ma da ta zo garin a nan ta sauƙa. Bayan da ta gama haɗa kuɗaɗenta na mota ta ɗauki Aliyu suka koma mahaifarta Abuja, inda mijinta da 'yan uwanta suke. Da ma can nemawa mijinta kuɗin da za'a masa tiyata ne ya sa ta zo garin kano neman aiki, har Allah yasa ta samu a wannan gidan marayun. Kai tsaye gidan mijinta ta wuce da Aliyu, kuma da isarsu ta zauna ta masa bayanin inda ta samu Aliyu, be musa mata ba, haka ya amince da zaman Aliyun tare da su, ya tiƙe Aliyu kamar ɗan da ya haifa, kasancewar Allah bai taɓa basu haihuwa ba. Haka Aliyu ya ci gaba da zama a gidan Anna. Wadda ita ce ke kula da kaf nauyin gidan nata, kasantuwar shi mijin nata ba shi da lafiya, har makaranta ta saka shi, bayan da ta samu aikin dafa abinci a wani restaurant, da albashin da suke bata take kula da kaf matsalosalun gidanta. Anna ita ce wadda ta ƙarawa Aliyu sunan Bhici a gaban sunansa na makaranta, kasacewar mijinta hifaffen garin Bhicin jahar Kano ne. Shi kuma mijin nata shi ne yake kiran sa Kuliya, saboda yace halayensa kaf irin na wani ƙaninsa ne da ya rasu, kuma sunan kanin nasa Kuliya!. Har zuwa lokacin Zaid na maƙale

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112