Skip to content

Chapter 87

Chapter 87

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

yake ba, hatta da baccin dare ba ta samu ta yi, ko na rana ma a firgice take yinsa, duk da ba wai haɗuwa suka yi ba, dan tun bayan zuwansa ba su haɗu ba, kawai de ta na jin tsoron abun da zai je ya zo. Ilai kuwa, yau suna zaune sai ga kiran Baban ya risketa, kan ta zo ya na san ganinta, kuma ta na zuwa suka tarbeta da maganar auren Zaid, shi ne ta musu shiru ta kasa cewa komai, to me za ta ce wai?, tace musu shi ɗin da suka ƙwallafa rai a kai ba mutumin kirki ba ne?, ko ta yi wa kanta ƙarya tace bata san aurensa?. Haƙiƙa ta ga farin ciki a idon kakansu, ta ga farin ciki a idon Hajiya, kuma ta ga farin ciki a idon kowa na gidan, don kwana uku kenan da zuwan Zaid ɗin, amma kamar yau ya zo, sai nan-nan suke da shi. Ta tabbatar da idan har ta nuna ƙin amincewarta da auren nan, babu wanda zai ƙara kulata, babu wanda ma zai ƙara yin alfahari da ita a gidan. Kuma ita kanta ta san cewa tan na son Zaid, amma halinsa ne kwata-kwata ba ta so, mutum fa?! Mutum ta ga ya kashe a gabanta, ran mutum ta ga ya ɗauka kamar wani kiyashi. Sai de kuma duk da haka babu komai, za ta jure komai a kan ahalalinta, wata ƙila ita ƙaddararta ce ta zo a haka, Allah ya riga ya tsara cewar har ta koma gareshi ba za ta taɓa jin daɗin rayuwa ba, ko wani jin daɗinta na duniya ƙayadajje ne. Kanta ta ƙara sun kuyarwa kamar ɗazu, ta kasa furta komai, hakan ya sa Baba fahimtar inda ta dosa, tana san auren, amma wata ƙila kunya ce ta hanata furta hakan. “Na gane.... Ki je ki fara shirye-shirye, dan nan da sati huɗu kema za'a ɗaura aurenki tare da na 'yar uwarki Nafisa!” *Bayan sati huɗu...* *Wakili Family House, Unguwar Jama'are, Haɗejia* Ta ko wani ɓangare na gidan a cike yake maƙil da jama'a, ko ina ka kalla jama'a ne fal, kowa sai kai kawo yake ana ta hidimar biki, domin kuwa yanzu-yanzu aka dawo daga ɗaurin auren jikoki uku na gidan, hakan ya sa gidan ya cika fal da jama'a. Saboda wannan aure gidan har sabon fenti aka sake masa, babba da yaro na wannan ahali na cikin farin ciki. Daga can ɓangaren samarin gidan kuwa, Zaid ne tare da samarin gidan, jiko da 'ya'ya, wasu ma bai sansu ba a cikin wata ɗayan, sai yau yake ganawa da su, kuma a yau din ne yake ƙara tabbatar da girma da kuma yawa irin na ahalin nasu. Daga can gefen kuwa Jagwado, Alandi da Zuzu ne sanye cikin manyan kaya, kai ka rantse da Allah na gari ne, yanda suka haɗe cikin manyan kaya sai zare idanu suke, kowa ya zo sai ya tambaya su waye su? Zaid ne yake amsawa da abokansa ne. Allah ya sani, ba ƙaramin farin ciki yake ciki ba yau, a yau din nan ya mallaki Ammata a matsayin matarsa, a yau ɗin nan ya zama cikakken mutum, shi kansa ya kasa yarda, wai shi da ya saba rayuwa shi kaɗai, shi ne yau ya wayi gari ya ganshi kewaye da tarin ahali masu matuƙar ƙaunarsa, banda matar da suka ɗauka suka ba shi, har auren gata suka masa, dan kuwa babu wata wahala da aka barshi ya yi a auren, Baba da su Kawu Abdullahi su ne suka ɗauke masa komai. Lokacin da ya koma Abuja ya siyi wani kyakkyawan madai-daicin gida, wanda yake da niyyar aje Rabi'a a ciki, ya na shirin siyan kayan furnitures Kawu Abdullah ya dakatar da shi da faɗin su ne za su yiwa 'yarsu kayan ɗaki, kuma hakan aka yi, don a jiya aka cika gidan da kayan furnitures da kuma na kitchen, da ma duk wani abu na buƙatar gida. Kuma hatta da sadaki Baba ne ya biya masa, shi kansa ba zai iya misalta kalar farin cikin da yake ciki ba, babu abun da zai ce sai godewa Allah, domin kuwa ita ma Rhoda ya na gab da aurar da ita, saboda sun riga da sun ɗinke da Zakar, hujjojjin dake hannunsa kawai ya rage ya miƙa, da zarar ya miƙa su za'a kama Alhaji Bala, kuma kamar yanda suka yi da Rhoda daga zarar an kama Alhaji Bala za ta musulunta. Sannan sun yi magana da Kawu Abdullah kan daga zarar Rhoda ta musulunta za ayi aurensu da Zakar ɗin. Don haka farin cikin da yake ciki ba me misaltuwa ba ne, baki ya yi kaɗan ya faɗeshi, sai dai kawai ya ci gaba da godewa Allah. RABI'A POV. Daga ɓangaren Ammatan Raja kuwa, duma suna can nasu ɗakin ana wa amaren kwalliya, cikin wata ɗayan ba ƙaramar rama ta yi ba, don har mutanen gidan sun fara zargin ko auren ne ba ta so, amma ta nuna musu ba haka ba ne. A can ƙarƙashin zuciyarta kuwa tunanninnika ne birgit ta ko ina, ita kanta a yanzu ba za ta iya cewa ga takamemen abun da yake damunta ba, amma ta san cewa ba ta jin daɗi, duniyar ba ta mata daɗi sam. Don har zargin wannan auren take, tun bayan rabuwarta da Zaid a Abuja ba su ƙara magana ba, hasali ma rabonta da shi tun ranan da za su islamiyya ta hangeshi shi da su Yunus suna hira, bayan nan ba ta ƙara saka shi a idonta ba, idan za ta ce ga abun da ya ramar da ita to har da kewarsa ma za ta iya shigowa ciki, ta na son ganinsa, ko da faɗa ne ma su ɗan yi, amma wannan zaman nesan ba ya mata daɗi. “Kai! Amma fa kin yi kyau Rabi'a” Cewar Rhoda, a sanda aka gama ɗaura mata ɗankwalin farin leshin da suka yi ankonsa ita da Nafisa, kanta ta kalla a mudubi. Tabbas ta yi kyau, dan hatta da wannan tabon yankan na gefe fuskarta an ɓoye shi da hoda, kwalliyar ta bal'in hawa fuskarta. Hannunta ta kai kan ƙashin wuyan da ta yi a kwanankin, ta ɗan ja guntin tsaki ta na jan wayarta. “Kai ku yi sauri ku fito ga masu ɗaukar hoto nan sun zo” Cewar Jidda, a yayin da take shigowa ɗakin da gudunta, ta ci uwar kwalliya kai kace ita ma amaryar ce. “Dan Allah Ummi ki yi sauri ki gama min” Momi ta faɗa a sigar magiya, ta na kallon me kwalliyar. “To” Me kwalliya ta amsa, a gefe guda kuma Rhoda da Rabi ne suke ɗaukar hoto a waya, daga can kuma Kairiyya ce takewa Nafisa da Kulsum hoto a waya. Haka suka gama shiriritarsu kafin suka fita. Dangi da jama'ar da aka gayyata haka suka riƙa zuba musu ruwan hotuna ana ta Allah sanya da alkairi. Da yamma kuwa walima aka haɗa musu, amma ba su yi dinner ba, dan Baba yace ba za'a yi ba, duk da suna son yi haka suka haƙura saboda babu yanda za su yi. *10:30 PM.* “Ke wai ina za ki kai ni ne?” Rabi ta tambaya tana kallon Jidda dake ta janta tun ɗazu, tafe suke a harabar

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112