Chapter 21
Chapter 21
a taƙaice, duk kuwa da yasani ɗin. MISHAL POV. Shekaran jiya suka dawo daga Maiduguri. Kuma a jiya ne Abubakar ya kaita aka cire mata braces ɗin dake haƙwaranta. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba a sanda aka rabata da su, don Allah ya sani, ba ta san su, ga shi dai ita ta ce a saka mata su, amma daga baya sai suka gundureta. Zaune take a comound ɗin gidan, suna hira ita da Shatu, yayin da Daala ke zaune a gabanta. Akasarinta hirar tasu a kan Maiduguri ne. Daga can saman benin gidan kuwa, Hajjara ce ke leƙowa ta window tana kallon Mishal ɗin. Cike da tsana da kuma alwashi. Ta ɗaukawa kanta alƙawarin ganin bayan Mishal, ba za ta huta ba sai ta ga tabbatuwar hakan. Ko da za ta ƙarar da duka abun da ta mallaka ne sai ta aikata hakan. Abun da ba ta sani ba shi ne; ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta ta kusa afkuwa, kuma tun kafin abun da ta tsara ya kai ga gaci komai yake wargajewa. *Unguwar Rafin Cinnaka, Suleja, Niger state* “Yanzu miye abun yi ?” Muryar Habiba ta tambaya, yayin da take zaune a falon gidan yayarta hajiya Inno. Hajjiya Inno ta yi murmushi. “Yanzu abun da ya kamata shi ne kawai ki kawo wani abun, a kai masa a matsayin kafin alƙalami... A fara aiki a kan Saratun, na faɗa miki aikinsa ba ƙaramin ci yake ba... Da zarar ya yi aikin ina mai tabbatar miki da ko sati ba za'a yi ba za ki ga samari sun fara sintiri a ƙofar gidanki...” Habiba ta ɗan yi dariya. “Haka nake san ji, dan Wallahi har ga Allah na gaji da ganinta a gidan nan haka... Ita ma idan ta ɗan samu ta yi auren nan ai yafi ko?” “Hakane” “To sai batun Mama, yarinyar nan so take ta fara fin ƙarfina, wai rannan dan na mata magana kan ta ɗan yafita min wani abu sai ta hauni da faɗa?!” “Mtswwww!, Wallahi kuwa Habiba da kin bada mata, har ita ta isa dan ub*nta ?, Idon ki za ki murje ki nuna nata cewar ke ce uw*rta, ba ita ta haifeki ba!” Habiba tace“Hummm!” cikin taɓe baki. “Gaakiya ba zan iya takurata ba, dan baki san yanda nake san Mama ba ne, sam ba na so ranta ya ɓaci Wallahi, ke dai kawai kawo wata shawarar” Cike da mamaki Inno take kallonta. Can kuma sai ta taɓe baki tace. “To ai ita ma nata lamarin mai sauƙi ne, sai amata na kasuwar samarin, alhajan nan na abuja su yi ta kai kawo a kanta, sannan a rufe mata baki, duk sanda za ki mata maganar kuɗi ta miƙo miki kawai...” Habiba ta saka dariya har da shewa, tana jin wani abu na washewa daga ranta. “Wallahi Yaya Inno abun ne da yawa, kin ga na Zainab ma abun yaƙi daɗi, kar ki ga yanda bawan Allahn nan ke gasa mata aya a hannu” Inno ta kuma yin dariya. “Shi ma nata mai sauƙi ne... Habiba idan fa da kuɗin ki shikenan, duk wata matsala taki ta kau, in dai za ki bada shikenan...” Ta sauƙe ajiyar zuciya. “Sai kuma na wannan sheg*yar yarinyar, kinbga fa duk dan na tagayyara rayuwarta na sa Ɗan Lami ya dawo da ita nan garin, toh!, ta taggayar ɗin, amma ni ba haka na so ba....Na fi so ta ƙare da cikin sh*ge, shi ne fa yasa ma na aikata akatau, amma dai har yanzu shiru ki ke ji...” Dariyar da Inno ta saka ce ta sata yin shiru. “Wai ni Habiba yaushe kika yi sanyi ne ?, ina Habibar da na sani ta da ?, wai duk kin yi sanyi kin zubar da makaman yaƙinki ?, yo in ba haka ba ai wannan ba wata matsala ba ce, ke dai zo ki ji” Ta ƙarashe tana matsawa kusa da Habiban, Habiba ta miƙa mata kunne. A take Habiba ta saka shewa tana tafa hannu, bayan da ta gama sauraron abinda Innon ta raɗa mata. “Ai kuwa ko miliyan nawa zan sadaukar a kan wannan aikin, in dai har... Zan ga bayan jinin Maryam a duniyar nan!” ______________ _Wai Siyama ce take san Kuliya😂... Wani ya bata shawarar kada ta fara tafiyar dare ba maraki, ah to, kar ta ce ba mu gaya mata ba_ _Shin wata ƙaddara ce wannan ke shirin faruwa ?_ _Ya za ta kaya tsakanin RAJA da RABI'A ?_ _Kun ji alƙawarin Hajjara a kan MISHAL?_ _Sannan ga Habiba ma a nata ɓangaren, me kuke ganin tana shiryawa ?_ _Kamar fa an bawa Kuliya assignment ɗin da zai sauya rayuwarsa, sannan Chidera ya ce 'yan dabar yau suka sauƙa a garin abuja....Kada ku ce min su RAJA ne😨...._ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #Taurariwriters °°°°°°°°°°°°°°°°°° *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *06* ~~~ *The wrong one will find you in peace and leave you in pieces. The right one will find you in pieces and lead you to peace.* *** *Shekara ta 2000* *Kano.....* A hankali Zaid ya juya ya kalli ƙaninsa Aliyu, wanda har zuwa lokacin yake ta risgar kuka. awa biyar kenan da aka kashe wutar da ta kama a gidansu. Wutar da ba ta bar musu komai ba, ciki kuwa harda mahaifiyarsu. Kuma har zuwa lokacin, suna sanye da wannan uniform ɗin islamiyyar, yayin da ƙonnaniyar gawarbmahaifiyarsu ke rufe a gabansu. Zaune suke a ɗakin da aka ajeta bayan da aka samu aka kawota asibiti, kuma tun kafin su kawo asibitin jama'ar da suka ɗaukota ke faɗin ai ta cika. Shi ma kansa Zaid ɗin so yake ya yi kukan, amma ya kasa. Bai san ina za su je ba, bai san ina za su koma ba, bai san kowa nasu ba, kuma Momman nasu ko ƙawa ba ta da ita, bare su ce za su je wurinta. Hatta da asalinsu basu sani ba, bayan ce musu da ta yi ita 'yar haɗejia ce, ba ta ƙara ce musu komai a kan asalinsu ba. “Aliyu....” A hankali nitsataiyar muryarsa me cike da kamewa ta kira sunan, yayin da lumaassun idanuwasa masu ɗauke da gray ƙwaya suke kallon Aliyu. Aliyun ya juyo ya kalli yayansa. Kuma har a lokacin kuka yake. Lokacin ƙarfe takwais na dare da ɗorariya, jama'ar da suka kawo su asibitin ma tafiyarsu suka yi bayan an tabbatar musu da rasuwarta. “Ba mu yi sallar magrib ba... Ga isha ta kawo kai” Da ƙyar sautin muryar tasa ke fita, don mai sauraro ma zai iya tsintar ɗacin da muryar tasa ke ɗauke da shi, ba zai ce ya gama mallakar hankalinsa ba, amma ya san cewa duk wanda ya mutu ba ya dawowa. Ya san cewa yanzu su da ganin Mommansu wata ƙila sai a lahira, sun zama marayu, yanzu su marayu ne waɗanda basu da kowa sai junansu. Babu wanda zai taya su kukan rashin da suka yi. Ba tare da Aliyun yace komai ba ya miƙe tsaye, shi ma Zaid ɗin miƙewar ya yi, ya dafa kafaɗarsa suka fara tafiya zuwa waje. Kuma har lokacin Aliyun na kuka, shi kuma Zaid ɗin sai rarrashinsa yake. A masallacin asibitin suka yi sallah. Sannan suka fita wajen asibitin. Dan Zaid ɗin ya tuna da ɗari biyun da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112