Chapter 81
Chapter 81
kasa ganin gaskiya?. Wani abun farin cikin ma shi ne; da bata faɗa masa cewar shi ɗan uwanta ba ne, wannan shi ne kaɗai arziƙin da aka yi. Ta raya hakan a ranta, don ita ta manta da maganar da ta faɗa masa a sibiti. Haka suka yi kiɗansu suka yi rawarsu, amma ba ta ƙara cewa kanzil ba, har suka babbata haƙuri, kawu Abdullahi ne yace ta shirya zuwa gobe zai kaita a mata gwaje-gwaje, sai a lokacin ta yi magana, ta sanar masa da cewar duk wasu gwaje-gwaje da suka dace babu wanda ba a mata ba, amma yace shi bai yarda ba, kawai ta shirya zai kaita a sake mata wasu, ba ta ƙara masa musu ba tace to, sannan ta miƙe ta koma cikin gidan. Kai tsaye ɓaangaren kakarsu ta yi, inda ta san 'yan matan gidan suna tare a can, dan a dai-dai lokaci irin wannan a can suke taruwa. Kuma kamar yanda ta ayyana a ran nata sun taru a can ɗin. 'Yan mata shida ne sa'o'inta a gidan, Momi, Nafisa, Fati, Jidda, Kulsum da Kairiyya, su na ganinta su ka yi shiru, kowa ya zuba mata ido ya na kallo, dan kaf cikinsu babu wanda ya san da zuwanta, a sanda ta shigo garin ma suna islamiyya. Gaba ki ɗayansu so suke su ganeta, kammaninta na musu kama da na wata da suka sani, kallon ƙurillar da ta ga suna mata ya sa tace. “Ya da kallo haka 'yanmatan Waliki family?” Kusan a tare suka fashe da dariya suka iyo kanta. A dai-dai wannan lokacin kakarsu ta fito daga ɗakinta ta na ɗingisa ƙafa, kujera ta samu zauna ta na kallonsu. “Rabi'a?, wai yaushe ma kika zo garin?” Cewar Kulsum ta na dariya. Rabi ta zauna a kujera ta na faɗin. “Ɗazu da yamma, kuna islamiyya lokacin” “Wayyo Allah, wallahi na ji daɗin zuwanki, kusan shekara biyar fa rabonmu da ke” Cewar Fati ta na matsawa kusa da ita. “Ke Allah ya yi da ke kina nan za ayi bikin Nafisa” Kairiyya ta faɗa, baki buɗe cike da mamaki Rabi ta kalli Nafisan da ta kawar da kanta, saboda Hajiya kakarsu dake wurin. “Wai dan Allah?” “Wallahi kuwa, nan da wata ɗaya da sati ɗaya” Jidda ta amsa mata. “Ke Rabi a ina kika ji wannan raunin na fuskarki?” Momi ta tambayeta, Rabi ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta na hagu, sai da ta haɗiye wani abu sannan tace. “Haɗari ne... Kai ni yanzu ku ba ni labari, ya ake ciki ?” Daga haka suka shiga hira a kan batun bikin, suna bawa Rabin labarin yanda suka tsara bikin, da yanda zai kasance, har kusan ƙarfe goma suna can, dan abincin dare ma tare suka ci. Kasancewar 'yan matan su duka ɗakinsu ɗaya, ya sa ita ma ta kwana a cikinau, dan dana tun can tare auke kwana, gadon Rabin ma na da yana nan, kuma yanzun ma a kansa ta kwana. *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.* RAJA POV. _🎶It was just two lovers..._ _Sitting in the car, listening to blonde_ _Falling for each other_ _Pink and orange sky_ _Feeling super childish_ _No donald glover🎶..._ Waƙar dake tashi kenan a cikin sifukun gidan, wanda Raja ya ƙure volume. Tsaye yake daga gaban mirror, ya na taje sumar kansa, sanye yake cikin wata ash shadda, a hankali bakinsa ya ci gaba da biya waƙar Golden hour ɗin dake tashi a falo. “I was all alone... With the love of my life... She's got glitter for skin... My radiant beam in the night... I don't need no light to see you... Shine... It's your golden hour...” Sai kuma ya yi shiru ya na kallon kansa a mirror, yayin da ya aje matajin hannunsa, bayan wani lokaci me tsayi yau shi ne sanye da manyan kaya, ya daga kafaɗarsa ya na murmushi, ya gyara wuyan rigar jikinsa, ya ƙara fesa turare a jikinsa, sannan ya finciki hularsa ya fito. “Huh?! Dude? Yau ina zuwa?” Cewar Rhoda kenan, yayin da ta fito daga kitchen, hannunta na dama riƙe da plate, Raja ya kama kumatunanta ya na ja. “Zance zan je” Rhoda ta shafa kumatunta da ya saki da hannunta na hagu. “Guys, ku shigo ku ga ikon God!” Kiran da ta ƙwalawa su Jagwado ne ya sa suka afko cikin gidan babu shiri. Kallon Rajan su ma suka tsaya suna yi, a karo na farko tun bayan saninsu da Rajan da kuma Rhoda, ba su taɓa ganinsu da mabanbantan kaya ba, a ko da yaushe kaya kala ya suke sawa, sai yau. “Allah de ya biya oga Raja, ina za ka fasa haka?” Alandi ya tambaya. “Zance zan je” “Kutumar dumadu, Kaga Oga Raja namu, Allah ya biya, gayu, oga fa ya rufta ramin ƙauna Allah Wallahi” Cewar Zuzu ya na wani ɗaɗɗaga hannu. Raja ya yi murmushi ya na girgiza kansa. “Wai Zuzu ban hanaku magana irin haka ba?” Zuzu ya shafa kansa ya na kallon ƙasa. “Sabo ne oga Raja, amma za mu dena da yardar me duka” ya faɗi muryarsa babu wani banbanci da ta ɗazun. “Ku fa?” Raja ya tambaya yana kallon sauran. “Aah, ai muma hakan take oga, ko ya kuka ce gayu?” Alandi ya faɗi ya na kallon su. “Haka ne” Jagwado ya amsa. “Na zo na raka ka?” Rhoda ta faɗi ta na aje plate ɗin hannunta, wanda ke ɗuke da alale. Raja ya maka mata harara. “Wa za ki bi?... Kama hanyar ki can joo!”. *Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.* Da gudu Fatima ta shigo gidan har tana bangaje Saratu da ta fito daga banɗaki. “Ke Fatima mi ye hakan?” Inaa, sam ba ta tsaya ba sai da ta dangana da ɗakin Habiba. “Ke dallah mi ye hakan za ki faɗo kaina?” Habiba ta tambaya ta na miƙewa. Fatima ta dafe ƙirji ta na zaro ido, hannunta ta ɗaga tana nunawa Habiban ƙofar ɗakin. “Wa... Wani na... na ga a waje... Kamarsu ɗaya da... Da Rabi!” Wani irin juyi kayan cikin Habiba suka yi, don a sanda fatiman ta ambaci kamar mutumin da ta gani da Rabi, ƙwaƙwalwarta ta hasko mata 'yan uwan Maryam na Haɗejia. To ko su ne suka zo kamata ?, wata ƙila Rabi ta sanar musu da duk irin abubuwan da ta mata, shi ne suka zo dan su kamata. Muƙut!, ta haɗiye yawu, tunawa da ta yi da labarin irin kuɗin baban Maryam ɗin da aka bata. Ba shiri gumi ya shiga tsatsafo mata, cikinta har wani ƙugi yake. Sallamar da Saratu ta ji a waje ya sa ta leƙa, kasancewar akwai hijabi a jikinta. Ita kanta sai da ta firgita, ganin wani mutum sak Rabi, tsaye a soron gidan nasu, amma sai ta ɓoye tsoronta ta amsa sallamar tasa. Ba tare da ta tambayeshi wa yake nema ba, ta masa lamini da ya shigo cikin gidan. Wata kujerar roba ta bashi, tace ya zauna a kai. Ya na zama a kan kujerar Habiba ta bankaɗo labulai ta fito, Fatima na biye da ita. Curko-curko suka yi daga bakin ƙofar ɗakin Habiban suna kallon ikon Allah. Saratu ce ta kawo masa ruwa, sannan ta zauna suka gaisa. “Am... Rabi'a nake nema” Wani irin ƙara cikin Habiba ya saki, da saida
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112