Chapter 19
Chapter 19
bar gida ta iyo nan. Kalisa ta taɓe baki. “Wallahi ni kuma na ga haukarki... wa ya faɗa miki cewar ana wani biya boka ko malam yanzu?... To ba'a haka, zagewa za ki yi ki nemi 'yancinki da kanki, da masifa da komai zaki ƙwatawa kanki 'yanci” “Ki na ga idan na bi wannan hanyar zan samu kansa ?” “Da gudu ma kuwa” Hajjara ta yi murmushi. “To yanzu miye abun yi?....” Daga haka Kalisan ta shiga tsara mata duk abubuwan da za ta yi, da hanyoyin da zata bi dan samun kan mijinta da kuma mallake gidanta. Ba tare da sanin cewa hanyoyin ba za su amfaneta da komai ba, sakamakon ɗaya bayan ɗaya hanyoyin za su ruguje, kuma rugujewar tasu za ta taho ne tare da ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta nan da 'yan kwanaki masu zuwa. Ƙaddarar da za ta wargaza komai, ta kuma saita wasu abubuwa. *Dambuwa road, Maiduguri...* MISHAL POV. Zaune take a tsakiyar 'yan uwanta na gidan Antinta Nimra, hira suke suna cin abinci, dan bayan an sauƙo daga idi su kai tsaye gida suka dawo. Kowa cikin kwalliyarsa mai kyau, wasu sanye da manyan kaya wasu kuma kayansu ne na al'ada a jikinsu. Mishal ɗin kuma sanye take da wata dark green cargo jumpsuit, daga ƙasanta ta saka farar shirt. Dan duk kayan sallahr da aka ɗinka mata cewa ta yi sun mata yawa. Shi yasa ta aje su da zummar idan sun koma abuja za ta bawa yayarta Adawiyya. Kuma da ma ita ba wani san manyan kaya take ba, ta fi so tai ta saka ƙananan kaya. A plate ɗaya suke cin abincin tare da kwaise, Arman da Daala. “Aki mu fita yawo mana idan anjima” Cewar Kwaise wadda take 'ya a wurin ƙanin Nimra tana kai loma, Arman ya gyaɗa kansa. “To ina za muje ?” Mishal ta tambaya. “Muje Gumalti, daga can sai mu wuce gidan zoo” Kwaisen ta faɗa tana kallon Arman dake zare wani zare daga kan Narjis, 'yar iqra ƙanwarsa dake zaune kan cinyarsa. “Shikenan, yarinya sai ta tanadi kuɗin da za ta kashe, an jima za mu fita!...” Arman ya faɗa da ɗan ƙarfi, dan sauran 'yan uwan nasa su ji. “Ni dai ba wani kuɗi da zan fitar, ina aljihunka” Cewar Iqra. “Alƙur'an ba ki isa ba, ga mijinki ai, sai ya biya miki” Iqra ta juya ta kalli mijinta Adam da suke cin abinci tare. “Rabu da shi Babe, sai mun kashe sama da abun da zai kashe” Adam ɗin ya faɗi cikin sigar zolaya. “Aki, za mu tsaya a hanya na sai fara ” Cewar Ijaz, yayin da yake cusa abinci a bakinsa. “Hello! Ban da ni za'a je?!” Wannan muryar ta faɗi daga bakin ƙofar falon, gaban Mishal ya yi tsalle ya hau kan mountain ever rest sannan ya diro ƙasa. Kallon fuskarsa kawai babban tashin hankalinta ne a duniya, kasancewar a duk sanda za ta kalli fuskarsa ma sai wannan lokacin ya haska a cikin kanta. Bata da tsoro, amma shi tana tsoronsa, ba ma shi kaɗai ba, duk wani abu da ya dangance shi tsoro yake bata. Ta zabura za ta miƙe tun kan ma ya ƙarasa shigowa cikin falon, Arman ya yi sauri ya riƙe hannunta yana mayar da ita ta zauna. Sannan ya juya ya kalli Yazid ɗin da ya shigo falon. “Yazid fita!” Arman ɗin ya furta a dake... Cikin kakkausan amonsa irin nasu na sojoji, babu alamun wasa ko kaɗan a fuskarsa, ya dake ya koma ainahinsa na soja. Sai da kowa ya jiyo ya kalli Arman ɗin, sannan kuma suka kalli Mishal da jikinta ke ɓari, sai ɓuya take a bayan Arman. “Ai ba.....” “Ka juya na ce!” Arman ɗin ya faɗi ya na aje Narjis kusa da Mishal ɗin da numfashinta ya fara yin sama. “Ok...” Ya faɗa yana juyawa, babu wani alamun nadama ko kunya a tare da shi, dan ya ci bulis, duk da bai mata komai ba a lokacin, kuma a ganinsa ko da ya mata wani abun babu abinda zai faru, tun da shi na gida ne. “Ki nustu Mishal, ya tafi, ba ya nan...” Adam ke faɗi yana san kwantar da ciwon nata, kasancewarsa likita. Idanuwanta sun fara yin sama, ga yanda numfashinta ke fita wani iri. Abubakar da Arman na gefenta suna mata fifita. A hankali-a hanakli hayyacinta ya dawo jikinta, sai sauƙe ajiyar zuciya take a kai-akai. “Kin sha maganinki yau ?” Arman ya tambaya. Kanta ta girgiza masa, shi kuma sai ya gyaɗa mata kai, tare da juyawa ya kalli Kwaise. “Duba ɗakinta ki ɗauko min jakarta...” Kwaise ta miƙe tana faɗin to. Hanin Mishal ɗin ta dawo hayyacinta yasa kowa ya koma ya zauna, Mushal ta cure gu ɗaya tana saka babban ɗan yatsanta na dama a baki, tare da fara shan hannun a sace. Dan bata san wani ya gani. Ko Abubakkar da sha hanata shan hannun, amma ba ta iya denawa, duk da takan jima bata sha ɗin ba, amma duk sanda zai faɗo mata a rai sai ta sha. “Wai ke Baby har yanzu baki san cewa kin girama ba?... Da ma har yanzu kina shan hannu ?”. Da sauri ta cire hannun na ta ta na turo baki, tare da juyawa Arman ɗin kai. Arman ya yi dariya. “Abubakar me yasa baka kaita an cire mata wannan braces ɗin ba ?” Cewar Arman ɗin ya na duban Abubakar. Abubakar da ke magana da Adam a kan ciwon Mishal ya ɗago ya kalle shi. “Sai mun koma za mu je a cire mata, dan na ga gap ɗin sun haɗe...” “Na kwaise kuwa har yanzu ba su haɗe ba” Cewar Ijaz. “Ai ba'a wani jima da saka mata ba shi ya sa, na Mishal ɗin fa ya kai shekara biyar, kawaise kuwa ai ko shekara uku bai yi ba” Arman ya ba shi amsa. Haka hirarrakinsu suka ci gaba da wanzuwa, har zuwa sanda Kwaise ta dawo riƙe da jakar maganin Mishal, Arman da kansa ya bata. Sannan suka ci gaba da hirar, har zuwa yamma, kowa ya sake kwalliya suka fita zaga gari da yawon gidan 'yan uwa. RABI'A POV. A yau ne aka dawo makaranta, don haka ita ma ta shirya da wuri, ta kama hanyar makarantar, Kuma bayan ta je ta gama aikinta, sai ta shiga shawagin duba Mishal, amma haka ta gama shawagin nata ba tare da ta ganta ba. Wata ƙila ba ta dawo ba, haka ta faɗawa kanta tana juyawa da ga tsayuwar da ta yi a ƙofar ajin su Mishal ɗin. Daga nan kuma ta wuce ɓangaren ta wuce ɓangaren sport na makarantar, ta tsaya a wurin da ake buga ball. Tana kallon yaran da ke cikin raga suna ta buga ball ɗin. Ƙafarta har ƙai-ƙai take mata, dan ji take kamar ta shiga cikinsu su buga tare da ita. Gani take kamar ba dai-dai suke wasan ba. Kamar idan ta shiga cikinsu za ta iya yin abinda ya fi wanda su suke yi. _“Yaya Baby, ba haka ake ba.....ki tsaya na nuna miki yanda ake...”_ Tunawa ta yi da wani lokaci da ya wuce a can baya, lokacin da suke buga ball ita da Baby a garden ɗin gidansu na da. Gidan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112