Chapter 22
Chapter 22
Momman ta basu a yammacin ranar, tace da su; su siyi wani abun idan sun je islamiyya. Awara ya sai musu da ita, sannan suka dawo cikin ɗakin da aka kwantar da ita. Suna kallon gawar suna cin awarar. Kuma bayan sun gama suka ci gaba da zama a ɗakin, har zuwa lokacin da dare ya tsala. Aliyu ne ya samu ya yi bacci, shi kuwa Zaid kwana ya yi yana gadin su su duka biyun. Washe gari Zaid ɗin ne da kansa ya bazama cikin asibitin, kafin ya nemo inda mahaifiyarsu ta yi aiki a da. Ya faɗawa abokan aikin nata rasuwarta. Kuma su ne suka zo suka yi Duk wani abu na sutura. Har aka mata sallah, kafin aka binneta a maƙabartar asibitin. Har kowa ya watse da ga maƙabarar, Zaid da Aliyu na tsugunne a kan kabarin. A wannan karon shi ma Zaid ɗin sai da ya yi kuka. Kukan rashin sanin madafar da za su dafa a yanzu, mutuwa irin wadda mahaifiyarsu ta yi akwai raɗaɗi. “Yanzu a nan zamu kwana?” Aliyu ya tambayi Zaid ɗin, a sanda suka dawo gidansu. Wanda wuta ta gama ƙonawa, ko ina ya yi baƙi, babu abinda ya rage sai rufin gidan. “Bamu da inda ya wuce nan... Aliyu” Zaid ɗin ya faɗi yana ƙoƙarin sama musu inda za su zauna. Har ya gama kwashe kayan da wuta ta bari Aliyun na binsa da kallo. Zaid ɗin da kansa ya share ko ina, ya fitar da tokar abinda ya rage, sannan da ƙyar a cikin kayan ya samu wani bargo wanda bai ƙone ba. Asalin bargon a kan gadon Mommansu take shimfiɗawa. Sai guntuwar katifar Zaid ɗin da ita ma kaɗan ne ta ƙone. Sai wasu kwanuka irin na silver wanda suka yi baƙi. Kuma a cikin tarkacen kayan, Zaid ya samo wani hotonsu guda ɗaya da rage. Zaid ya fita can banɗakin gidan na waje, ya duba randar cikinsa ya ga akwai ruwa, ya zuba a cikin bokitin da ya samu a banɗakin, sannan ya koma ya kira Aliyu kan ya zo ya yi wanka. “Zaid wani kaya za mu sa?” Aliyun ya tambaya a sanda ya fito daga banɗakin, bayan ya yi wanka. “Babu Aliyu, ba mu da wasu sauran kaya, komai kana ganin yanda ya ƙone, wutar nan bata bar mana komai ba sai ran mu” “To ni yunwa nake ji!” Aliyu ya faɗa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. Zaid ya yi shiru yana tunanin ta inda zai samawa ƙaninsa abinci, bai san ta ina zai fara ba, ba shi ma da wata dabarar sanin inda zai samu ko da kuɗin sai masa abincin ne. Shi ba ya ta kansa, ta ƙaninsa da ƙaddara ta bar masa yake. “Ka zauna, bari na je gidansu Naufal na roƙar mana Mamansu, ƙila ta bamu ko da sauran ne” ya ƙarshe yana ɗaga kafaɗaraa ta dama. Aliyunya gyaɗa kansa a hankali, a yayin da yake zama a bakin baƙar katifarsu. Zaid ya fita daga gidan ya shiga gidan dake maƙotansu. Matar gidan ya fara gaisarwa, ta amsa shi da 'yar fara'ar da yake da tabbacin ba ta kai zuci ba. “Ashe kuma mamarku ta rasu?” Maman Naufal ɗin ta tambaya a sigar gulma, kan Zaid a ƙasa ya gyaɗa mata, don da ma shi yaro ne mai ladabi, ba kamar Aliyun ba. “To Allah ji ƙanta!” “Amin... Da ma Aliyu ne yake jin yunwa, kuma wutar ba ta bar mana komai ba, shi ne na ce ko za mu samu wani abun, da zan bashi ya ci...” Ya ƙarashe maganar, zuciyarsa na masa tuƙuƙi, wai yau su ne suke roƙon abinci, su ɗin da abinci sai dai su yi sadakarsa, wai aka ce rayuwa juyi-juyi. “Eh, akwai wani guntu, amma iyaka na cin mutum ɗaya ne” Kitchen ta shiga, sannan ta fito hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano, ta miƙa masa ya sa hannu ya karɓa yana miƙewa tsaye. “Na ce kuma wai ku baku da wasu 'yan uwa ?” Tun ba yau ba da ma yasan halin matar, kuma halinta na san jin ƙwaƙwaf yasa Mommansu ba ta shiri da ita. Sai kawai ya girgiza mata kai, yana ɗaga kafaɗarasa ta dama. “Bamu da kowa” Sai ta jinjina kai tana gaskata abun da mutane kan faɗa a kan Rabi'ar, na cewa wataƙila cikin shege ta je ta yi a garinsu, shi ne ta gudo nan ta zo ta kafa sabuwar rayuwa. (Kai jama'a, duniya ina za ki da mu?!, Baiwar Allah ta rasu, maimakon ai mata addu'a, sai dai a ci gaba da cin namanta. Wanda kuma hakan sam ba dai-dai ba ne). “Ga wata jallof ɗin taliya, ka ta shi ka ci” Zaid ya faɗi a sanda ya dawo gidan, Aliyu da ke kwance a kan katifar ya miƙe zaune, sannan ya kai hannu ya karɓi 'yar robar. Kafaɗarsa ya ɗaga yana kallon taliyar. Abincin duka bai fi loma biyar ba, kuma ko shi Aliyun kaɗai ba ya jin abincin zai isheshi, bare ace shi ma ya zauna ya ci. “Kai ba za ka ci ba?” “Ba na jin yunwa” A sanda ya kai ƙarshen maganar cikinsa, a lokacin ya wani irin ƙulle, saboda yunwar. Amma sai ya dake ya ɗaga kafaɗarsa, sannan ya ce. “Bari na je na watsa ruwa” Kuma daga haka ya fice daga ɗakin. Wankan ya je ya yi, ya dawo ya tarar da Aliyu ya raba taliyar biyu, ya ci rabi sannan ya bar masa rabi. “Me yasa ba ka cin ye ba?,ko ba daɗi ?” Ya jero masa tambayoyin yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, tare da juya rigar uniform ɗin islamiyyarsa dai-dai. “A'a, akwai daɗi mana, na ga kai ma ba ka ci ba, ka daure ka ci wannan ɗin” Wata ƙwalla ta taru a idon Zaid. A hankali ya zauna kusa da ɗan uwan nasa yana kallonsa. Wannan karon kusan a tare suka ɗaga kafaɗunsu na dama. “Aliyu... Yanzu babu Momma, da ga ni sai kai... Babu wani mai temakon mu sai Allah... Yanzu rayuwa za ta mana wahala, ban san ya za mu ci gaba da rayuwa ba, Aliyu ban san ma mecece rayuwar ba, kawai dai nasan akwai ƙalubale, kuma shi ne abinda za mu tunkara a yanzu!...” Shi kansa ba ya ce waɗanan kalama nasa ba ne, bai san da ga ina suke zuwa ba, jin su kawai yake suna fita daga bakinsa. Bai taɓa sanin ya iya su ba ma. Haka kawai ya ji wani nauyin kula da ƙaninsa ya hau kansa, ya na jin zai iya komai dan ganin ya sa ƙaninsa farin ciki, yana jin zai iya sadaukar da komai don ɗaukar nauyin ƙanin nasa... *Present day......* *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja* RAJA POV. A hankali ya zauna a bakin gadon ɗakin da yake a matsayin nasa. Yanzun nan suka gama zaga gidan, dan ganin abinda za su buƙata. Har yanzu abinda ya faru ɗazu ya ƙi sakin ransa, gani yake kamar mafarki yake, abun akwai ɗaure kai. “Raja me ke faru wai ?” Muryar Rhoda ta katse musu kallon-kallon da suke a ɗazun. Kuma maganar tata ce ta sa ya kalli hannun yarinyar dake zubar jini. Ba tare da ya amsawa Rhodan da ta tsaya tana kallon ikon Allah ba, ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112