Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,191 words 0 views Progress saved
Download Book

da rannan Habiba ke sanar mata da cewa Babansu ya siyar da shi. Don wasu daga cikin kadarorin mahaifiyarta da aka raba gado aka bata, 'yan uwan mahaifyarta suka danƙa su a hannun Ɗan Lami, sauran kuma suna wurin dangin nata. “Ke!, me ki ke a nan ?! Bar nan dallah!” Muryar ɗaya daga cikin masu gadin makarantar ta katseta a tsawace. Shikenan kuma, da ma ta jima da sanin cewa shi talaka ba a bakin komai yake ba. Ba shi da wata kima ko dajara a idon mutane. Ba ta ce masa komai ba, ta juya ta fara tafiya. Ko jikin store ɗin da ta sabba zama ba ta kai ba aka kaɗa ƙararrawar tashi. Hakan yasa ta fasa zuwa store ɗin, kai tsaye ta yi hanyar fita daga makaranatar. Tun da an tashi to ita ma babu abun da za ta zauna ta yi. Tana tafiya ta na kwatanta yanda wasan da Yaya ya bata labarin za'ayi zai kasance, yace mata yau akwai wasa tsakanin arsenal da fc Barcelona. Shi yasa take ta kwatanta yanda wasan zai kansace. Ba tare da ta an kara ba wani me mota ya iyo kanta, ƙiris ya rage bai kaɗeta ba, amma duk da haka sai da ta faɗi. RAJA POV. A yau suka sauƙa a garin Abuja, bayan duk wasu maganganu da suka yi da Garuje, sai yau Allah ya hukunta tahowar tasu. Duk da ba shi kaɗai ya taho ba, ya taho ne tare da duka yaransa, Rhoda, Alandi, Zuzu da Jagwado. Dan su ɗin na amana ne, ba zai iya zuwa ko ina ba tare da su ba. _🎶.....It's something that i never, ever, ever had _ _I have never needed somebody🎶_ _But i wannan spend sleepless nights, and sleepy days with you.._ _With you, with you, you make me speechless...🎶_ A hankali waƙar sleepless nights ta Armaan Malik ke tashi a cikin motar tasa ƙirar Jeep. Raja ne ke tuƙa motar, yayin da Rhoda ke zaune a gefensa, Alandi, Zuzu da Jagwado na gidan baya. Rajan na sanye cikin wani blue jeans, da farar shirt dake ƙasan baƙar denim jacket ɗin da ya ɗora a saman rigar. Kuma sak kalar kayan dake jikin Rhoda ne. Don ita ce ta zame masa kamar abokiyar tagwaitakar tasa, abu ne mawuyaci su saka kaya da ban da ban. Kaya kala ɗaya suke sakawa, size ne kawai ke banbanta. Shi da Rhodan ne ke bin waƙar, Raja na yi yana murmushi, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Kuma a lokacin abun ya faru. A lokacin ƙaddarar da ke jiransa a garin Abuja ta auku, wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura. Kan motar ya juya dan shiga layin gidan da ya kama a KAURA DISTRICT.Wata yarinya ce tafe a gefen hanya, ba ya ce ya iya ganin fuskarta ba. Sai ganin wucewar wata baƙar mota ya yi da gudu, wadda ta so ta kaɗe yarinyar, duk da bata kaɗetan ba, sai ta kaɗata gefen hanya. Ba shiri ya taka birki. A firgice ya fice da ga motar, su Rhoda suka bishi da kallo su ma suna fitowar. Da gudu ya yi inda yarinyar take, sannan ba tare da jiran komai ba, ya kama hannun yarinyar ya ɗaga ta. “Sannu kin ji” Ya faɗa yana san kallon fuskarta, kuma sai aka yi sa'a ta ɗago da fuskar tata ta kalleshi. A lokaci guda zuciyarsa ta yi wani irin tsalle a ma'ajinta. Kamar zata fito daga bakinsa. Ba komai ne ya jawo hakan ba, face wata fuska da ya gani, fuskar sak irin ta mahaifiyarsa, fuskar sak irin ta ƙaninsa Aliyu, sannan fuskar sak irinta ce a tare da shi. Amma ta ya hakan za ta faru ?, ya aka yi yarinyar ke kama da su ?, wacece yarinyar ma ?, daga ina take ?. Kusan ƙamewar muntuna shida Rabi ta yi, a sanda ta kalli fuskar matashin da ya temaka ya ɗago da ita bayan kifawar da ta yi. Mamaki ne bayyane a fuskarta ita ma, kamar yanda yake kwance a tasa fuskar. Za ta iya rantsewa da Allah ta ga gilmawar mamakin a cikin idanuwansa. Ba ƙaramar kaɗuwa ba ta yi ita ma, ba dan kada ta yiwa kanta ƙarya ba, da sai ta ce wannan ya fi kama da mahaifiyarta fiye da ita. Dan ya fita farin fata, saboda ita ba wata fara ba ce sosai, ta ɗan kwaso baƙin Abbansu. Amma Ummansu fara ce sosai, kuma farinta sak irin na wannan bawan Allan ne, kusan rabin idanuwansa a lumshe suke, sannan ya kafeta da ƙwayarsu wadda ta kasance gray color. Ta sani cewa ko cikin 'yan uwanta na haɗejia babu mai kaka da wannan, duk da ba za'a rasa ba, amma dai wannan ba daga can yake ba, to kenan waye shi ?, daga ina yake ?, me yake a nan ?, kuma me yasa yake kama da Ummansu ?, don sai dai ta dangana kamar tasa da ta Ummansu ba tata ba. Mafarin komai kenan😎. *DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja* KULIYA POV. “Aliyu, this will be your next assignment, ina so ka yi ƙoƙarin yinsa cikin taka tsan-tsan da kula, ka sani kuma nima na sani, a halin yanzu akwai masu farautar rayuwarka... Dan haka ka kula, coz this was the most dengerous assignment ever. Dan haka sai ka kula....” Chidera Kinsily ke koro masa wannan jawabin, yayin da yake miƙa masa wani file. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi file ɗin. File ɗin da zai kai rayuwarsa zuwa wani mataki, file ɗin da zai sauya rayuwarsa, file ɗin dake ɗauke da matakin farko na sauyawar ƙaddararsa. Ƙaddarar da za ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu lamuran. Chidera ya ci gaba da faɗin. “Case ne a kan wasu manya-manyan 'yan ta'adda da suka yi wa garin Abuja tsinke a yau ɗin nan... Ba ma so abun ya tafi da nisa, wannan file ɗin ɗauke yake da bayanin kowannensu, don haka kasan abun yi... Sannan idan kana so za ka iya neman temakon abokin Abubakar” Kuskure mafi girma kenan da ya zama sanadiyyar faruwar wannan ƙaddarar. Wata ƙaddara mai cike da tarin abubuwa, masu daɗi da akasinsu. A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce. “Zan san abun yi sir” Kuskure na biyu kenan, wani babban kuskure da zai yi nadamarsa da farko, sannan daga baya ya dawo ya yi farin cikin ɗaukarsa. * “Shigo!” Muryar Abubakar ta faɗi daga cikin office ɗin. Bayan da aka buga ƙofar office ɗin nasa. Kuliya ya murɗa ƙofar office ɗin, sannan ya shiga ciki. A hankali Abubakar ya ɗago da kansa ya kalle shi. Kamar kullum sanye yake cikin baƙar suit, sai dai babu suit ɗin, waist coat ce kawai a saman baƙar oxford shirt ɗin dake jikinsa. Hannunsa na dama riƙe da file ɗin dake ɗauke da ƙaddararsu. Ƙaddarar da za ta sauya LABARINSU. “Sabon assignment ne, idan babu abun da za ka yi, sai ka taya ni...” Wannan dakkakiyar Muryar tasa ta faɗa. Kuskure na uku kenan. Abubakar ya yi murmushi yana aje ipad ɗin hannunsa. “Babu damuwa Dude, ai duk assignment ɗinka nawa ne... akan miye ?” Kuskure na huɗu kenan. “Ban sani ba, dan ban duba ba” Ya amsa shi

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112