Chapter 1
Chapter 1
*LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* بسم الله الرحمن الرحيم *01* ~~~ *Unguwar Madalla, Suleja, Niger state* *06:00am* “RABI'A!, nasan cewa bayan na mutu za ki koma gidan mahaifinki.... ADAWIYYA ina da tabbacin bayan kin koma cikin 'yan uwanki da zama za ki sha wahala, na san cewa za ki shiga taskun rayuwa kala-kala, na san cewa Habiba ba ta sona, bare kuma 'ya'yana, na san cewa ba za ta taɓa barinki ki huta ba..... Amma ki riƙe addu'a, ki riƙe addu'a a ko wani irin yanayi kika tsinci kanki. Ki yi haƙuri, domin na san cewa ƙaddarorinki yanzu suka fara. Yanzu LABARINKI zai soma.........” Zubar ruwan da ya cika bokitin da ta saka a famfo ne ya jawo hankalinta daga duniyar tunanin da ta faɗa. Kanta ta ɗan ɗaga sama ta kalli sararin samaniya, har yanzu garin akwai sauran duhun asuba, yanayin gashi kuma yanayin garin akwai zafi, kasancewar ana tsakiyar kwanki goma na ƙarshen watan azumi ne, dan bai fi saura kwana huɗu sallah ba. Kanta ta sauƙe ƙasa ta kalli bokitin da ya cika har ruwan ciki na zuba, ta tsugunna zata janye bokitin, wata murya ta daka mata tsawa cikin faɗin. “Ub*n me kike ne wai Rabi?!, Tun ɗazu bokitin ya cika har yana zuba amma ba za ki ɗauke ba?,Saboda baƙin halli da kika gada a wurin uw*r ki ko?, to ki ci gaba da tsayuwa a wurin, idan ƙarar ruwan nan ya tada min yara sai na ci uw*r ki Wallahi!....”. Rabi ta ɗago da kanta ta kalli inda matar ke tsaye, hasken wutar nepar dake haske tsakar gidan ya haska mata fuskar matar tar, matar babanta ce, Habiba, matar da akodayaushe burinta ta ga ta lalata mata rayuwa. Kuma bata tsaya iyaka nan ba, har cikin garin Abuja take turata aikatau, yau shekarunta biyar a gidan, tun bayan rasuwar mahaifiyarta, mahaifinta ya je har garinsu mahaifiyarta ya ɗaukota, ya dawo da ita cikin gidansa, gidan da ita zata iya kiransa da kurkuku. Domin ko da da sakan ɗaya bata taɓa jin daɗin zaman gidan ba. Babu wanda take jin daɗin zama da shi a gidan sai Saratu, 'yar Habiban ta biyu, a wasu lokutan ma idan Habiban na mata faɗa har baki take sakawa. Tun a shekararta ta farko a gidan ta fara ganin uƙuba irin ta matar uba, da ta saba jin hakan a labarai, labarin yanda matan uba kan ƙuntatawa 'ya'yan mazanjensu, ko da wasa bata taɓa hasaso cewa rayuwarta zata fuskanci abu makamancin wannan ba. Sai gata tsundum cikin wannan hali. Kuma ƙalubalen nata ya fara ne tun daga sanda ta nemi da Babanta ya maida ta makaranta, yace ai ta gama karatu, shi bq zai iya wahalar da kansa wurin sakata a makaranta ba. Ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba a lokacin, dan Allah ya sani tana san karatu, kuma burin mahaifiyarta ne ta yi karatu. Bayan wannan sai ta koma baiwa kuma jakar aikin gidan, 'ya'yan Habiba ko tsinke basa ɗaukewa a gidan sai de ita ta yi. Duka wannan bai ishi Habiba ta gama da rayuwarta ba sai da ta fara turata aikatau. Kullum iƙirari take kan cewar ba zata ciyar da ita a banza ba, tun da ub*nta bashi da aikin yi, ita take riƙe da gidan, kuma kusan hakan ne, dan Mahaifin nasu ba shi da wani aikin yi, kasancewar an koreshi a wurin aikinsa. Babu abinda yake sai zaman baza, zuciyarsa ta riga ta gama mutuwa, babu abinda yake sai caca da bin matan banza. Haka Habiban za ta saka shi a gaba tana tsigeshi, kamar wani ɗan da ta haifa, amma ko tari ba ya iya mata, saboda yasan ba shi da gaskiya. Babu yanda Rabin za ta iya, haka ta yarda ta fara zuwa aikatau ɗin, da ko wani ƙalubale dake fuskantar rayuwarta, Kalaman mahaifiyarta na ƙarashe su ne ke yawo a kanta. A sanda take mata maganganun, gani take kamar zafin ciwo ne ke nuƙurƙusarta, gani take kamar kawai sambatun ciwo mahaifiyar tata take, dan waɗanan kalaman nata sune maganarta da ta ƙarshe, bata sake magana ba har ta koma ga ubangijinta. Sai a yanzun take ganin duk abunda take faɗa mata, duk abinda ta ce mata zasu faru gareta su take gani. Dan yanzu haka a wata makaranta dake cikin garin abuja take aikin goge-goge da share-share. Bata da wani buri a yanzu, bata da wani fata, bata da wani abin da take san cimmawa, dan a ganinta kamar rayuwartace ta zo ƙarahe, kamar LABARINTA ne ya ƙare, babu wani abu da ya yi saura. Ƙwara ma kawai ta zauna ta rungumi ƙaddararta da ta zo mata a haka, tun da Allah yasa a bautawa wasu rayuwarta za ta ƙare to ta amshi hakan...... Ƙarar turowa ƙofar gidan nasu ce tasa ta juyawa takalli ƙofar. Mama ce ta shigo, 'yar Habiban ta uku. Amma kuma ba wai hakan ne yasa Rabi mamaki ba, mamaki take na san sanin sanda Maman ta fita ta daga gidan. Ta san cewa jiya daddare tare suka kwanta, tun da ɗakinsu ɗaya, amma ko da asuba bata ganta ba, fitar tata a daren ba wani abun mamaki ba ne, dan ta saba kwana a waje ma, ta saba bin samarinta su tafi yawon banza. Sunan 'karuwa' da Habiba ta saba kiranta da shi ne ya dawo cikin kanta. Sai kawai ta juya ta ɗauki bokitin da ta juye ruwan cikinsa a randa, ta koma bakin famfo ta kunna famfon ta ci gaba da tsaiwa a wurin tana jiran ya cika. Dan Habiba na gama masifar tata ta koma ɗakinta. A rayuwar gidansu ta tabbatar da karin maganar nan da hausawa ke faɗin 'Laifi tudu ne, ka take naka ka hangi na wani', ita zata bada shaidar wannan, domin duk abinda Maman ke yi da sanin Habiba, dan idan ta samo kuɗi ko kayan kwaɗayin da samarinta kan bata Habiban take kawowa. Ita abun haushinta a nan shi ne; ganin cikin watan azumin Allah ta ala ma bata bar abinda ta saba ba. Sai ta girgiza kanta a fili tana kashe famfon da ruwansa ya cika bokitin gabanta. “Ub*an miye kike wani girgiza kai ?!” Maman ta tambaya cike da masifa, dan in dai ruwan bala'i ne, to kaf cikin yaran Habiba babu wanda ya gado shi kamar Maman, dan bata da mutunci, Rabi ta kalleta, sannan ta girgiza kanta. “Babu komai” Sai da ta ɗan tsaya na wasu sakanni tana aikawa Rabin harara, sannan ta juya kanta ta shige ɗakinsu. Rabi ta kuma jijjiga kanta a sanda ta juye bokiti na ƙarshe a cikin randar. Share gidan ta shiga, ta share tsakar gidan tas, kana ta shiga ɗakinsu, dan ɗaukan kayan da za ta sa, saboda wankan da za ta yi. Tana ɗage labulen da harar Mama ta fara cin karo, sannan ta bi ɗakin duka da kallo, Saratu ce zaune tana guga, sai Fatima ƙaramar ƙanwarsu tana kwance a kan katifarta, sai sharar bacci take. Bata cewa kowa komai ba, ta ƙarasa shiga cikin ɗakin tana nufar inda take aje jakarta ta Ghana must go. Zip ɗin jakar ta buɗe, idonta ya sauƙa a kan kayan da suke a saman jakar, kayanta ne, kayan da ta zo gidan da su tun shekaru biyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112