Skip to content

Chapter 86

Chapter 86

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

zuwan wannan Zaid ɗin yanayin ki ya sauya” Rabi ta sunkuyar da kanta tana kallon yatsun hannunta, amma ba ta ce komai ba. “Menene yake faruwa?. Ko bakya sonsa kamar yanda Hafiza tace?” Rabi ta yi saurin girgiza kanta tana faɗin. “A'a, ba haka ba ne. Ina sonsa, kawai de wata matsalar ce da ban” Jidda ta gyaɗa kanta tana dafa kafaɗarta. “Na gane, to Allah ya kawo miki mafita, ke de kawai ki yi addu'a... Kin ji?” Sai ta gyaɗa kanta kawai. Jidda ta ƙara dafa kafaɗarta, sannan ta miƙe ta koma gadonta. Rhoda dake kwance a gefen gadon Rabi ta yi murmushi ta na gyara kwanciyarta. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriter's ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *22* ~~~ *Keep on letting your love shine...* *** RAJA POV. Zaune yake a falon kakansu wanda mutanen gidan ke kiransa da Baba, Baba Munzali da kuma Kawu Abdullahi ne tare da Baban. Kawu Abdullahi ne ya masa tambayoyi kan yanayin yanda rayuwarsa take a can garin Abuja da ya faɗa musu ya na da zama, sun masa tambayoyi sosai, kafin suka tambayeshi alaƙarsu da Rabi'a. “Na gamu da ita ne a hanyar makarantar da take zuwa aikatau, kuma daga haka ne muka soma soyyaya, har muka fahimci juna, giftawar wannan iftila'in ne ya kawo mana tsaiku” Kawu Abdullahi ya gyaɗa kansa a sanda Zaid ɗin ya kai ƙarshe a maganganunsa. “Ke nan ka san abun da ya faru da ita?” Kansa a ƙasa ya gyaɗa shi. “Na sani Kawu, dan ni ne ma da kaina na yi jinyarta a asibitin da aka kwanatar da ita” Baba Munzali ne yace. “Kuma kai yanzu kana santa a hakan?” “Sosai ma kuwa Baba, ina san aurenta a yanda take, abun da ya faru da ita ƙaddara ce,wadda ta wuce fata, kuma san aurenta da nake ne ya sa na biyota har nan...” Ko kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai, wayar Zaid ɗin ta yi ringing alamun shigowar kira. “A min afuwa...” “Ba damuwa za ka iya ɗaga kiranka” Kawu Abdullahi ya amsa masa. Kansa ya gyaɗa ya na ɗaga kiran. “Ok” Kawai yace sannan ya katse kiran, cikin WhatsApp ya shiga, ya buɗe chat ɗin wani contact, a inda aka turo masa wani vedio, buɗe vedion ya yi, kafin a hankali ya matsa ya miƙawa Kawu Abdullahi wayar. “Ka duba ka ga” Kawu Abdullahi ya karɓa cike da mamaki, kafin ya danna play, vedion ya buɗe, sannan hoton Habiba dake garƙame a cell ɗin 'yan sanda ya bayyana, fuskarta ta ji duka ba na wasa ba, muryarta ce ta shiga fitowa raɗau daga cikin wayar. Hakan ya sa Kawu ya karkata fuskar waya zuwa ga su Baba dan su ma su gani. “...Ni ce na yi wa Maryam asirin da ya sa Ɗan Lami ya saketa, kuma ni ce na yi mata asirin da ya sakata jinya, har ta kai ga mutuwa, har ila yau ni na saka Ɗan Lami ya karɓo min Rabi daga wajen 'yan uwan Maryam. Har ta dawowa wuri na da zama, kuma... Kuma ni ce na yi wa Rabin asirin da zai sa idolan wani namiji ya kalleta zai ji sha'awarta, har aka samu wasu suka mata fyaɗe!...” Daga haka vedion ya tsaya cak, alamun dai ya ƙare ne. Cike da mamaki ko wannensu ya kalli Zaid ɗin dake durƙushe gabansu. “Kun gane ta?” Ya tambaya ya na kallonsu, don ya ga kamar ba su fahimci zancen da ake ba. Baki buɗe Kawu Abdullahi yace. “Na ganeta. Habiba ce... Abokiyar zaman Maryam” Zaid ya gyaɗa kansa. “Ƙwarai ita ce... A lokacin da na rasa Rabi'a, na sa aka kamata, don ta mana bayanin inda take, a memakon mu samo bayani kan inda Rabi'a take, sai muka samu wannan bayanin” Baba ya share ƙwalla ya na kallon jikansa, jini ba ƙarya ba, hatta da yanayin maganarsa irin na mahaifiyarsa ne, shi yanzu ba shi da wani fata godewa Allah, da kuma neman yafiyar Allah, kan zunubansa na baya. “Matso nan jikana” Zaid ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na matsawa kusa da Baban da ya kira shi, kansa ya shafa ya na faɗin. “Allah ya mamka albarka, Allah ya ji ƙan mahaifiyarku.... Kuma ni da kaina na baka auren Rabi'a, ba za'a ɗau wani dogon lokaci ba, akwai bikin ɗaya daga cikin ƙannen naka da za ayi nan da sati huɗu, dan haka in Allah ya yarje mana tare za ayi da naku!” Wani abu ne ya shiga ratsawa tun daga kan Zaid har zuwa ƙafafunsa, farin ciki ya buɗe ƙofar zuciyarsa ya rufta, ƙaunar 'yan uwansa ta ƙara kama shi, a hankali ya kwanta a jikin kakansa ya na nemawa Momma da Aliyu rahamar Allah. * “Bros” Cewar Zakar ya na duban Zaid, wanda ke cire takalman kafarsa bayan da ya dawo daga wurin su Baba. Zaid ya amsa ya na cire takalman ƙafarsa. Tare da shigowa ɗan madai-dai cin falon samarin, ya zauna a kan kujera yana dubansu. “Ya ake ciki ne?” Sani ya tambaya. Zaid ya yi murmushi. “Baba ne ya bani aure...” Zakar ya aje mug ɗin hannunsa ya na zaro ido. “Ikon Allah... Wai da gaske?” Zaid ya yi murmushi ya na shafa kansa. “Da gaske ne mana, kuma kun san wani abun farin cikin ma?, tare da na ɗayar ƙanwar tawa za ayi!” “Wai auren Nafisa?” Auwal ya tambaya ya na zaro ido. “Ban san sunanta ba. Kawai de yace auren nan da wata ɗaya ne” “Gaskiya muna taya ka murna, amma ai kana nan har zuwa lokacin bikin?” Cewar Yunus. Zaid ya girgiza kansa. “Akwai wani aikin da ban ƙarasa ba a Abuja. So dole zan koma, amma biki saura sati biyu zan dawo” “Ni fa ɗan uwa, ina san wannan ƙanwar taka da kuka zo tare!” Zaid ya yi shiru ya na kallon Zakar dake wannan batu. “Rhoda?” Ya tambaya dan tabbatarwa. Zakar ya gyaɗa kai. “Of course ita, ina santa, and i mean it” “She is not musulim, ka bari ta musulunta tukunna” “Wai har sai ka jira?. To tun da me ya sa bata musulunta ba ?” Auwal ya ta baya ya na gyara zama. “Akwai abun da muke jira kafin faruwar hakan, amma ina da tabbacin lokacin shigarta musulunci ya kusa” “To Allah ya tabbatar, amma dan Allah kar ka bari a yanka ni, dan Wallahi ina santa” Zaid ya yi dariya ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Idan an yi auren Abuja za ka bita?” “Abuja kuma?” Zakar ya tanbaya ya na kallonsa. Zaid ya gyaɗa kansa. “Ƙwarai Abuja, ma aikaciyar DSS ce” “Jar uba! Kace ƙanwar taka me zafi ce” Zaid ya ɓata fuska, ya na kallon Yunus. “Ban san irin wannan abun Yunus” “Allah baka haƙuri, wasa ne” “Rabu da shi sirikina, zan maka maganinsa” Zakar ya faɗi yana hararar Yunus. “Har mun zama surukai kenan?” Zaid ya tambaya. “Eh mana, na ga dai kai ma ƙanwarmu zaka aura, ni ma kuma ka ga zaka bani ƙanwarka, mun zama surukai” Gaba ɗayansu suka sa dariya. RABI'A POV. “Kin yi shiru?” Cewar Baba ya na kallonta, ɗagowa ta yi yo da kanta ta kalleshi, yayin da take zaune a ƙasa daga gefensa. Allah ya sani tun bayan zuwan Zaid gidan nan hankalinta ba a kwance

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112