Chapter 77
Chapter 77
da babu yanda Rhodan ba ta yi da ita ba kan ta fara cin abincin da ta zo da shi, amma fir ta ƙi. Haka ta yi ta jera sallollin bayan da Rhoda ta sanar da ita kwanakin da ta kwashe a asibitin. Kuma duk da sallallin da ta ruƙa jerawa, ba ta samu ta idar duka ba, ta dai samu ta yi da yawa, haka ta zauna tana hutawa, kafin Rhodan ta bata abincin ta ci, sannan likita ya zo ya dubata, har ma yace zuwa gobe zai ba su sallama. Kuma tare suka kwana da Rhodan har zuwa safiyar yau. Abu na farko da ta fara yi bayan ta tashi shi ne ci gaba da biyan sallollinta, sai in ta gaji ne za ta zauna ta huta, duk da a zaune take sallahr, kuma likitan ma bai basu sallamar ba sai da yamma. Shi ne Rhodan ta kira shi don ya zo ya dawo da ita gida. Ƙofar motar ta buɗe da niyyar fita, har ta sa ƙafarta ɗaya a waje sai ta fasa fita ta juyo ta kalleshi. Shi ma kuma ita ɗin yake kallo. “Dan Allah, kada ka ƙara kusanta tata, kada ka ƙara nema na, kada ƙara bin ko da hanyar da kasan za mu haɗu ce, wannan roƙona ne gareka...” Kuma ta na kaiwa nan ta fice daga motar. Raja ya yi murmushi ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, wai kada ya ƙara nemanta, ai abun da ba ta sani ba shi ne; shi da ita kuwa yanzu suka fara haɗuwa, don ba zai rabu da ita haka ba, dole zai san yanda ya yi ya aureta. Sai da ya gama shawaginsa a duniyar tunani, kafin ya tayar da motar ya juya ya bar unguwar. Da sallama a bakinta, Rabi ta shiga gidansu, duk da akwai duhun dare, ta na iya ganin komai dake wakana a tsakar gidan, saboda hasken wutar lantarkin dake ci a tsakar gidan. Zaune a kan babbar tabarma Habiba ce, Fatima, da kuma Mahmud, sai Babansu daga can gefe ya na sauraren radio, daga Habiban har Ɗan Lamin miƙewa su ka yi suna kallonta. A dai-dai lokacin Saratu dake zaune a ɗaki ta fito da gudu, jin wata murya me kama da ta Rabi, hasken ƙwan lantarki nan, ya haska mata fuskar Rabi tar, kusan sati huɗu kenan rabon da ta saka 'yar uwar tata a idonta, kuma duk tsawon wannan lokacin ita kaɗai ce take cikin damuwa a gidan, daga Ɗan Lami har Habiba babu wanda ya damu. Ta na iya ga wata kallar rama da Rabin ta yi, ga kuma wani rauni da take iya gani a gefen fuskar Rabin. “Gantallaliya an dawo?” Kalaman Habiba kenan, hakan ya sa da maɗaukakin mamaki Rabi ta kalleta, wato matar nan ba ta san Allah, ita take turata aikatau, kuma a hanyar dawowarta gida daga wurin aikatau ɗin aka saceta, har kusan sati huɗu ba ta gida, amma da abun da za ta fara tarbarta da shi kenan?. “Gantali?, haka aka ce miki gantali na tafi?” Ta tanbaya ƙwalla na ciko idonta. “Yo in ba gantali kika tafi ba a gidan uw*r wa kike tsawon wannan lokacin?!” “Gidan uw*r da kika aike ni na je, ko ba ki ji ba?, na ce gidan uw*r da kika aike ni na je!” A wannan lokacin kam Rabi ta je ƙarshe, ba za ta iya jure ko wani cin kashi ba, a yanda take jinta ba za ta iya ɗaukar ko wani ciwon kai ba, bayan wanda take tare da shi, haba!, abun ai ya yi yawa, ya kamata ace an barta haka, ko ita ma ta huta. Ba wulaƙancin Habiba kaɗai ba, na kowa ma ba za ta ƙara ɗauka ba. Habiba ta shiga tafa hannuwa cikin sallallami. “Rabi? Ni kike zagi? Ki ce dadiron naki rashin kunya ya koyar da ke?” “Ni ba karuwa ba ce. Wannan gantallaliyar 'yar taki da ta bar gidan ub*nta ta bi namiji ita ce karuwa!. Ya isheki haka Habiba, na gaji, ba zan ƙara ɗaukan wani walaƙancinki ba, ya isheni haka!” “Ɗan Lami ai ka na ji ko?, To ka koreta daga gidan nan, dan ba zan iya zama da ita ta na halin 'ya'yan akuya ba. Ban da rashin kunyar da ta koyo kuma!” Kamar da aka kunna inji haka Ɗan Lami ya hau zagin Rabi, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, Rabi kuwa ta na tsaye a gabansu ƙyam, babu wani alamar tsoro ko rauni tare da ita, to wani dare ne jemage bai gani ba?, ai na mutuwarsa ne kawai ya rage. Abu da ya yi ƙamari Ɗan Lami ya rarumo muciya ya yi kan Rabi da ita. “Kar ka soma Abba!” Ta dakatar da shi a dake, hakan ya sa Ɗan Lamin ya tsaya daga shirin dukanta da yake, doj da ma duk borin kunya yake, ya na yi ne dan ya burge Habiba, saboda akwai maganar kuɗi tsakaninsu. “Kar ka soma duka na. Wani laifi ma na maka da na cancanci duka huh?, yau sati na uku ina kwance a asibiti, an samu wasu marasa imani sun haikemin, kuma ba komai ne ya ja min hakan ba face ayyukanka, ayyukanka marasa kyau da ka saba yi, zina da kake yi da 'ya'yan mutane ita ce yau ta faɗo kaina, bayan ta faɗa kan ɗaya 'yar taka, kai babu ruwanka da rayuwarmu, shagalinka kake san ranka...” A take Ɗan Lami ya ji jikinsa ya yi sanyi, dan duk abin da ta faɗi gaskiya ne, babu abu ɗaya da ta faɗi wanda yake ba dai-dai ba, sai dai kuma waɗanan kuɗaɗen da yake hangowa ba za su su sa ya ji maganar tata ba. “Ki fice ki bar min gidana, kada ki sake dawowa gidan nan!” Zuciya ta ciyo Rabi, hakan ya sa ta juya ta fice daga gidan, da gudu Saratu ta bi bayanta tana kiranta, ko hijabi babu a jikinta haka ta fita. Habiba ta samu wuri ta zauna, kamar ta tashi sama dan murna, dan kuwa duk abun da take so ya tabbata, rayuwar Rabi ta lalace, tun da har ta furta da bakinta cewar wasu sun mata fyaɗe, sai a yanzu ne burinta ya cika, sai a yanzu ne duk fafutukar da ta yi ta yi tun bayan auren Maryam ta kawo ƙarshe. _“Wallahi sai na ga bayanki ke da yaranki, ba zan huta ba sai na ɗai-ɗaita rayuwarki Maryam!”_ Haka ta taɓa faɗawa Maryam ɗin, a wani lokaci can baya, kuma ga shi ta yi ɗin, ta aikata duk abun da ta ci buri, ita ce fa Habiba, babu wani wanda ya isa ya shiga gabanta. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *20* ~~~ *Let your wings be soft enough to carry her, until she remembers how to fly again...* *** RABI'A POV. “Rabi!... Rabi!” Kiran da Anti Saratu ke mata ne ya sa ta tsaya da tafiyar da take a fusace, ta juya tana kallon Anti Saratun, wadda fuskarta ta yi gaje-gaje da hawaye. “Rabi” Ta furta a raunane ta na rungume Rabin, tare da fashewa da kuka, har mutanen dake wucewa ta lungun suna kallon su, duk dauriyar Rabin sai da ta zubar da hawaye, Anti Saratu ta saketa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112