Skip to content

Chapter 68

Chapter 68

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ke cikin wannan raunnaniyar zuciyar tasa, a hankali ya lumshe idonsa, hakan ya sa ita ma Mishal ɗin lumshe nata idon. “Hafsat!” Ya kira sunan nata a hankali. “Umm... um... umm” Ta amsa idon nata a lumshe, hannunta na dama dake cikin nasa ya ɗora a saitin zuciyarsa, kusan a tare suka buɗe idanuwansu. “Kin ji yanda take bugawa ba?... Da ko wani bugu da take ta na bugawa ne da sunanki, da kowani bugu da take tana bugawa ne da sanki, Hafsat... I... Love... Youuuu!” Ba shiri Mishal ta matse gaban rigarsa da hannunta dake kan setin zuciyarsa, saboda yanda kalaman suka saka jikinta rawa. Ba ta za ta ba ta ji hannun Kuliya ya kewaye waist ɗinta ta baya, sannan ya matso da ita jikinsa sosai, hakan ya sa ta buɗe idonta ba shiri. “Answer me Hafsat, did you love me?!” Ya tambaya ya na goga lips ɗinsa a kan nata, hakan ya sa Mishal ɗago ɗayan hannun nata, tare da ƙara matse gaban rigarsa. Sakan ɗay... Biyu... Uku... *Washe gari...* *07:10 AM.* Mishal ta rufe lunchbox ɗinta, bayan da ta gama jera abincinta a ciki, sanye take da complete uniform ɗinta, ta juya za ta fita daga kitchen ɗin idonta ya sauƙa a kan flask ɗin abincin Kuliya. Kuliya?!, Sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, nan take abun da ya faru a jiya ya dawo mata. A jiyan bayan shuɗewar sakan uku, muryarsa ta katse shirun dake wanzuwa a falon. “Na ba ki daga yanzu zuwa gobe da safe, ki yi tunani a kai” Abun da yace kenan, kafin ya saketa a hankali, ya ɗauki plate ɗin da ya ci abinci ya nufi kitchen, hakan ya bata damar faɗawa ɗakinta da gudu, ta sakawa ƙofar sakata. har gari ya waye ta na saƙawa da kuncewa. Ko da safe da ta tashi ayyukanta ta shiga yi cikin gaggawa, don so take ta yi sauri ta kammala abun da za ta yi don ta bar gidan kafin ya fito, hakan da ta tuna ne ya sa ta zabura za ta bar kitchen ɗin, sai dai kuma fatan ta bai cika ba, don a dai-dai lokacin ƙofar kitchen ɗin ta iyo ciki, Kuliya ya shigo, kamar kullum sanye cikin baƙaƙen kaya. Kallonta yake cikin wata iriyar siga da Mishal ba ta san ta inda za ta mata fasarra ba, hancinta ta ja, sakamakon murar da ta kamata a jiya, ta haɗiyi yawu da ƙyar. Numfashinta ya kusa ɗaukewa a sanda ya tsaya a gabanta. “Har kin shirya?” Ya tambaya ya na kallon hancinta da ya yi jajir, da alama dai mura take. “Eh” Ta amsa masa cikin muryar me mura. “Ba ki da lafiya?” Ya tambaya ya na duban yanayinta, da sauri ta girgiza masa kai, sai kuma ta gyaɗa kan nata tana shaƙar ƙamshin turarensa da duk murar da take ba ta hanata jinsa ba. Wani sauti ta ji me kama da na murmushi, hakan ya sa ta kalli fuskarsa da sauri, kuma sai ta ga da gaske ne, Kuliya ne yake mata murmushi, wani abu sabo, wani abu da za ta cewa ba ta taɓa ganinsa a zahiri ba. Kuma murmushin da ya yi sai ya ƙara bayyana mata kamarsa da Adawiyya, haka zalika murmushin nasa ya ƙara bayyana kamar da suke da ɗan uwansa... Tunaninta ya katse a sanda ta ji sauƙar tafin hannunsa a kan fatar wuyanta, wannan sanyin ya shiga bi ta jijiyon jikinta, hakan ya sa ta ɗan ɗauke numfashinta na wasu sakkani, kafin ta dawo da shi ta na jansa da sauri-sauri. “Har da zazzaɓi kenan?” Ya tambaya ya na dawo da hannun nasa goshinta. “Zan bawa Ibrahim (Drivernta) maganin mura ya kawo miki” Da sauri ta gyaɗa masa kai tana jan hanci. “Ban manta ba... Mecece amsata?” Ta kalli fuskarsa, amma sai ta kasa cewa komai, bakinta ya mata nauyi, kamar wanda ta haɗiyi dutse. A hankali Kuliya ya ƙara matsawa kusa da ita, sannan ya saka hannunsa na dama ya kewaye ƙuginta, ya haɗeta da jikinsa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, hakan ya sa Mishal rintse ido tana kawar da kanta, hannunsa na hagu ya sa ya kamo haɓatar ya juyo da fuskarta. “Look at me!” Sai ta buɗe idon nata tana kallon fuskarsa. “Did you love me?” Saboda abun da Mishal take ji ba ta san sanda ta shiga gyaɗa masa kanta da sauri ba kuma ta gyaɗa ya fi sau biyar. “Kin tabbatar?” “E... Eh!” Kalaman sun yi wa Kuliya daɗi, hakan ya sa ya yi wani irin murmushi da sai da ya bayyana haƙoransa, kafin ta ɗauke hannunsa daga kan haɓarta, ya dawo da shi gefen fuskarta, yana shafawa a hankali. “I love you Teddy Bear!” Ya na kaiwa ƙarshen maganar, ya raba leɓensa biyu, sannan ya sa nata na ƙasa a tsakiya, kafin ya haɗe bakinsa da nata gaba ɗaya. Abun da ya yi ya sa Mishal ɗaga ƙafarta sama, sannan ta dunƙule hannayenta a kan ƙirjinsa. Ba ta san ma me yake faruwa ba, ba ta san me ake yi a duniyar ba, ba ta san me yake wakana a kitchen ɗin ba, abu ɗaya ta sani, shi ne ita ce riƙe a hannun Kuliya, yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da gefen fuskartsa na dama, bakinsa kuma cikin nata, ya na aika mata da wani laffiyayyen kiss. A lokacin ne aka ƙwanƙwasa ƙofar falon ta can compound, sannan muryar Ibrahim ta biyo baya. “Ranki ya daɗe lokaci na ƙurewa, ki fito kar mu makara!”.😁 #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *17* ~~~ *Time moves slower when you miss somebody.* *** *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja* RAJA POV. Yau zaune yake a tsakar gidan, ya na kallon yanda iska ke busawa ta na kaɗa bishiyoyin farfajiyar gidan, a zahiri kenan, amma a baɗini sam ba su yake kallo ba, tunaninsa na can wata uwa duniya, yayin da shi kuma yake wannan duniyar, sati uku kenan rabonsa da farin ciki, sati uku kenan rabonsa da walwala, sati uku kenan rabon da wani abu na fara'a ya gifta a fuskarsa, sati uku kenan da shigar yaruwarsa cikin yanayin tashin hankali da zullumi, sati uku kenan da komai na rayuwarsa ya yi juyin waina a tanda, kuma a cikin wannan satin ukun ne rayuwarsa ta shiga kwale-kwalen katako, wanda ke tangal-tangal a cikin kogin da ke cike da yunwatattun kadogi, a cikin sati ukun nan komai ya cakuɗe masa. Kuma duk hakan ya samo asali ne ta sana diyyar ɓatan Rabi'a, don zuwa yanzu ya na da tabbacin Rabi'ar ba kawai makarantar ta dena zuwa ba, ɓata ta yi, amma abun tambayar a nan shi ne, ina ta je?, ta na ina ?, shin ta na hannu na gari?, ko a'a, idan ya yi zurfi a tunani irin wannan sai kansa ya kulle, kamar wata ƙofar da aka garƙame da makulli. “Raja!” Ya ji muryar Jagwado na kiran sunansa, amma sai ya ƙi juyawa bare ya amsa. “Raja!” A wannan karon muryar Alandi ce ta yi kiran, kuma a yanzun ma bai amsa ba. Kusan a tare suka zauna a kusa da shi, Zuzu a ɓangaren dama, Alandi a kusa da Zuzu ɗin, Rhoda ta zauna a gefensa na

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112