Chapter 45
Chapter 45
a ran Aliyu, sau tari yakan keɓe kansa ya sha ƙuncin kewar yayan nasa. Da haka har ya kwashe shekaru biyar tare da su Anna, a cikin wannan shekaru biyar da suka shuɗe, Allah ya yi wa mijin Anna rasuwa, sakamakon jinyarsa ta ciwon ƙoda da ya kasa sakun sauƙinta. Haka Anna ta ƙara rungumar Aliyu a matsayin wanda ya rage mata, ta manta da cewar shi ba ɗanta ba ne, ta manta da cewar ba ita ta haifeshi ba, ganin bayan mijinta da 'yar uwarta ba ta da kowa, kuma ga shi mijinta ya rasu, sai ƙanwar tata da kuma shi Aliyun. Lura da Anna ta fara yi da yanayin damuwar da Kuliya ke ciki ne ya sa ta ritsa shi da tambayoyi, har ta samu nasara a kansa, ya bayyana mata abun da ke cin ransa. Da haka ta masa alƙawarin za ta je har Kano tare da shi don su duba ɗan uwansa. Sai de me?!. A sanda suka isa Kano suka je gidansu Aliyu na da, basu iske kowa a cikin gidan ba, hakan ya sa Aliyu da kansa ya shiga gidansu Naufal ya tambayi Maman Naufal ɗin, shin ta san inda ɗan uwansa yake?, kuma Maman Naufal ɗin ce ta sanar masa da cewar ai rana ɗaya suka tashi suka ga babu Zaid ya gudu. Jiki a saɓule cikin tashin hankali da sallalami Anna ta dawo Abuja da Aliyu, kuma tun daga lokacin yanayinsa na shiga ƙunci ya ƙaru fiye da da. Babu yanda Annan ba ta yi da shi ba, kan ya dawo yanda yake amma ya ƙi. Har ta haƙura ta zubawa sarataura Allah ido. Bayan da Kuliya ya kammala secondary, Anna ta ƙuƙuta ta sa ma masa gurbin karatun diploma a wata makaranta dake cikin garin Abuja. Bayan ya kammala diplomar ne ya shiga fafutukar neman aikin da suka taso cikin burin yinsa shi da ɗan uwasan, aikin da Momma ta ƙarfafa musu gwiwa a kai, tun suna ƙananu suka yi wa kansu alƙawarin yin aikin DSS!. Sai da ya gama shan wahalar neman aikin, kafin Allah ya sa wani ɗan uwan mijin Anna ya kawo masa offern aikin DSS ɗin. Da an ce mutum na da hannaye shida, da Kuliya ba zai yarda ba, amma a sanda aka ba shi offern zai iya cewa ya ga hannayensa sun nunku daga biyu zuwa shida wajen karɓar takardun, ya yi matuƙar farin ciki da samun aikin. Kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga aiki gadan-gadan, bayan da aka musu training, ƙwarewarsa kan aikin da kuma gaskiya da maida hankali ne yasa shi samun nasarori da dama, tare da samun ƙarin girma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. *Present day...* RAJA POV. _🎶...We're not in love..._ _We share on stories_ _Just something in your eyes..._ _Dont be afraid..._ _The shadows know me_ _Let's leave the world behind...🎶_ Waƙar da yake saurare kenan, ta cikin headphones ɗin dake saƙale a kunnensa. Jingine yake jikin gate, idonsa a kan ƙofar gate ɗin makarantar tasu. Ya na kallon sanda ƙafafunta suka fito daga cikin gate ɗin, kuma zai iya rantsewa kan abu na farko da ta fara kalla daga fitowar tata shi ne. Ya ga sanda ta yi wani siririn murmushi, shi ma kuma martanin murmushin ya mata, sannan ya miƙe a kan ƙafafunsa, ya fara takowa zuwa inda take tsaye, wato ƙofar makarantar. Hannunsa ya kai ya tura headphones ɗin ƙeyarsa. Tare da ɗan ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Mu je ba?” Tana wannan sirirn murmushin ta fara tafiya, yayin da shi ma ya jera tare da ita, be san me ya sa ba, amma bayan son sanin asalinsa ta dalilinta, yana san samun kusanci da ita, sai dai ba ya jin abun kamar yanda Rhoda ke faɗi ne, da ta ce wai ya na santa ne, shi sam bai ga hakan ba, kawai dai ya na jin son wannan haɗuwar da suke, don idan weekend ya zo ba ya jin daɗi, shi da za'a bi ta tasa ma da an dena yin weekend ɗin. Sai kuma ya yi wa kansa da kansa murmushi. Da ya hango tarin ɗaliban da ba sa son zuwa makaranta, wasu ma ba su da lokacin hutu sai wannan weekend ɗin, wata ƙila idan suka ji wannan batun nasa sai sun naɗa masa na jaki. “Yau ina Rhoda?” Muryar Rabi'a ta faɗi bayan wani lokaci. Kamar me neman Rhodan, sai da ya waiga bayansa ya kalli ƙofar Estate ɗinsu, sannan ya juyo da kansa yana kallon hanya. “Yau ba ta zo tsurkun ba” “Ku kaɗai kuke rayuwa a gidan naku ne?” Sai da ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da. “Eh, amma akwai wasu abokai na guda uku, mu 'yan Kano ne, aiki ne ya kawo mu Abuja, kuma da zarar mun gama za mu koma” Sai ta gyaɗa kanta. A sanda take ƙara tabbatarwa da kanta duk yanda aka yi bai san da zaman mijin Mishal ba, amma sai dai idan matsala suka samu, har ta kaisu ga rabuwa, ko kuma dai sun rabu ne ba tare da sani ba, ma'ana ko ɗaya ne ya ɓacewa ɗaya. To ita yanzu mamaki da ruɗanin sai suka zame mata biyu, tana san sanin wace alaƙace tsakaninta da su, tana kuma son sanin abinda ya raba waɗanan 'yan uwan biyu, amma ba ta san ta inda za ta fara ba. Kawai sai ta tare shi tace masa ta ga ɗan uwansa?, to idan kuma da ma ya san da zaman ɗan uwan nasa fa?,ya kammata ta fara sanin abun da ke tsakaninsu tukkuna, ta na buƙatar sanin farkon LABARINSU, kafin ta san wani mataki ya kamata ta ɗauka a kan lamarin. “Ke fa?, tare da wa kike rayuwa?” Wannan innocent muryar tasa ta faɗa, a sanda suka tsaya a bakin titi, ta kalli hanya sannan tace. “Ni da yayata da kuma Ummanmu, kafin Allah ya yi wa yayartawa rasuwa, daga bisani kuma Mamata ma ta rasu, sai kuma na dawo da zama a gidan babana, akwai matar babana da yaranta huɗu, Anti Saratu, Mama, Fatima da Mahmud... Sai kuma shi baban nawa” “Shi ne yasa kike aikatau a nan?” Ya tambaya kansa tsaye, kuma ya lura da ta haɗiyewa wani abu, kafin wannan siriryar muryar tata tace. “A'a, ba babana ba ne, matar babana ce” Raja ya gyaɗa kansa ya na ƙara tabbatarwa kansa da abun da zuciyarsa ke zargi a kan yarinyar. Ba tare da ya sake ce mata komai ba, ya tsayar mata mota kamar kullum, ta shiga sannan suka yi sallama. Sai da suka yi nisa, sannan ya juya ya koma layinsu. Da Rhoda ya fara haɗuwa a bakin ƙofa, ta jingina da jikin ƙofar part ɗinsu tana kallonsa, fuskarta ɗauke da murmushi. Ransa ya haɗe ya na ɗauke kai, ya yi kamar be ganta ba. Sai da ya zo wucewa ta gefenta, sannan ta ɗaga hannunta tare da saka masa wani fito me ƙarfi, har da wani tafa hannu, hakan yasa ya tsaya yana kallonta. “Idan na ce you fall in love, sai ka ce ba haka ba, amma ga shi nan kullum sai ka karakata har bakin titi, idan ana cikin weekend sai ka riƙa ɓata rai, dude ko ka yarda... Ko kar ka yarda, ka... Faɗa.. can
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112