Chapter 57
Chapter 57
take, ta rasa inda za ta sa ranta, ita a tunaninta shi mq Zaid ɗin mutuwa ya yi. Kwanan Zaid ɗaya a aibiti kafin ya farfaɗo, kuma yabna farfaɗowar babu wanda ya samu kusa da shi sai Rhoda, haka ya ƙanƙameta suka rera kuka me isarsu, kafin ya ɗauketa suka dawo gidansu. Haka suka ci gaba da rayuwa, sai dai ba kamar yanda suka saba a da ba, kamar yanda Maman Rhoda ta bar musu kuɗinta da kayan ƙosai da kokonta, haka suka ci gaba da yin sana'ar, kuma a ɓangare guda suna zuwa makaranta, Zaid ne ya ci gaba da riƙe su har zuwa lokacin da shi ya kammala makaranta. Duk da Rhoda ce ke soya ƙosan, dan shi ya koma maƙiyin ganin wuta. Amma kuma ba ya bafinta ita kaɗai, duk inda za ka ganta to shi ma za ka ganshi. Da haka ya yi applying wata University a nan cikin garin kano, don ba zai iya yin nisa da Rhoda ba. Da haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu, yau da daɗi gobe babu. A lokacin da Zaid ya kammala karatunsa, sai ya shiga neman aikin DSS, aikin da ya sha burin yi tsawon rayuwarsa, aikin da yake kwana yake tashi da shi a zuciyarsa, aikin da suke da burin yinsa tun suna yara shi da ɗan uwansa. Cikin ikon Allah ya samu, hakan tasa ya ɗauki Rhoda suka koma Abuja, kuma ita ma bayan ta gama makaranta sai ta ce tana san ta shiga aikin DSS ɗin, Zaid be hanata ba, sai ma shige mata gaba da ya yi har ta samu. Shekerar Rhoda biyu da fara aiki, aka basu wani assignment me haɗari, wani assignment me ɗauke da sumatsi, wani assignment wanda ya shafi rayuwar ko wannensu, wani assignment wanda ya taho da guguwar ƙaddararsu, wani assignment wanda zai zama sanadiyyar faruwar wata ƙaddara, wadda za ta iya tarwatsa komai, sannan ta shirya wasu lamuran. Assignment ne a kan wani me kuɗi wanda ake zarginsa da yin safarar makamai da kuma miyagun ƙwayoyi, Alhj Bala, wanda a lokacin yake zaune a garin Abuja. Daga Zaid har Rhoda babu wanda ya yi musu wurin karɓar aikin, don za su jefi tsuntsaye biyu ne da dutsi ɗaya. Dole ta sa suka dawo garin Kano, don suna buƙatar bi ta hannun Garuje, babban yaron Alhj Balan, ƙarfi da ya ji suka koma 'yan daba, shi Zaid har da sauya suna zuwa RAJA. Sannan sun yi yarjejeniya da Rhoda kan idan sun kawo ƙarahen aikin za ta musulunta, babu yanda be yi da ita ba kan ta musulunta tun tana ƙarama, amma taƙi, sai yanzu ta yarda da hakan, shi ya sa Zaid ya zage damtse, don ya samu ya kawo karshen aikin ta ko wani hali, saboda ya na so ƙanwarsa ta samu rabauta, tun da Allah be sa Maman Rhoda ta samu rabon ba. Kuma sun nemo wasu 'yan dabar kan titi guda uku, dan aikin nasu ya tafi dai-dai, Alandi, Zuzu da Jagwado, Zaid ya temaki rayuwarsu sosai, kafin ya ɗauke su aiki. Kuma a lokacin ne suka haɗu da Uchechi. ____________________ _Salmanians!... Ku ce kallon kitse mukewa rogo, ashe Raja ba ɗan ba ba ne, kai amma wanga bawan Allah an yi ɗan reni_ _Kada fa ku manta da sirrin zuciyar Zaid da ya bayyana ya fito fili, shin kuna ga Rabi za ta amince da shi?_ _Ku dai ku ci gaba da bi na sannu a hankali, dan ganin wata waina za mu toya a feji na gaba_ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *14* ~~~ _-*The key element to happiness is; Knowing that you deserve to be loved correctly for the wild and beautiful soul that you are*-_ *** Follow my Wattpad account 👇 https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends ~~~ RABI'A POV. Har ta kai gida ba ta cikin hayyacinta, ba ta sani ba ma ko ta haukace ne, haka ta riƙa yin abubuwa sukuku, har Anti Saratu ta lura da ita. Tana zaune a ɗaki ta takure wuri ɗaya, Anti Saratun ta shigo ta zauna kusa da ita ta na taɓata. Yanda ta zabura ya ankarar da Anti Saratun cewa tunani me zurfi ta faɗa. “Rabi?! Wai me yake damunki?” Rabi ta sauƙe ajiyar zuciya tana sunkuyar da kanta ƙasa, to wai ita me za ta ce ne?, ta faɗa mata cewar wannan Zaid ɗin da ta take yawa bata labarin suna mutunci ne ya yi faɗa da arniyar budurwarsa kanta, kuma ya furta cewa ita ce matar da zai aura nan gaba?, yin soyyayar sa da arniya ba laifi ba ne, dom ba haramun ba ne, amma yanda ya mari budurwar tasa, da yanda ya furta 'His wife to be' ɗin nan shi ne abun da ya tsaye mata a rai. “Ba za ki faɗa min ba ?” Rabi ta ƙara yin ƙasa da kanta, don ba ta san me za ta faɗa matan ba. “Rabi! Kin san cewa ba ma ɓoyewa juna komai, duk damuwata ke nake faɗawa, me ya sa ke ba za ki faɗa min taki damuwar ba? Idan har ba zan iya temeka miki ki fita daga cikin dakuwar ba, ni me iya tayaki baƙin ciki ce” Jin hakan ya sa zuciyarta tsinkewa, ba shiri hawaye ya sauƙo mata, hawayen da ta yi ta riƙe shi tun ɗazu don kar ya zubo, sai kawai ta kwantar da kanta a kafaɗar Anti Saratu. “Anti Saratu wai ina zan sa kai na ne?.Ya ake so na yi?.Yau Zaid ya yi faɗa da budurwarsa a kaina, kuma ya faɗa mata cewar ni zai aura ba ita ba. Da ma ina da wannan muhummancin?” Bisa ga mamakinta sai ta ji Anti Saratu na murmushi. “Kowani ɗan adam ya na da daraja da muhummanci Rabi, kuma kowa ya na da tasa darajar. Ina me miki albirishiri da kasancewarki ɗaya daga cikin masu wanna darajar, saboda kina da daraja fiye da lissafinki Rabi!” Rabi tasaki kuka me sauti. “Yanzu ya zan yi da Yaya?, idan na rabu da shi ban masa adalci ba” Wannan maganar tata ta tabbatarwa da Anti Saratu zarginta a kan Rabin tun lokacin da Zaid ɗin da take ba ta labarinsa ya fara ɗorata a taxi, daga Rabin har shi Zaid ɗin suna san junansu ne ba tare da sun sani ba. “Rabi ki na son Zaid?!” Tambayar ta saka Rabi fashewa da matsanancin kuka, ita ba ta san ya za ta yi da rayuwarta ba, ba ta ma san inda za ta sa kanta ba, ina za ta kai kanta da hakkin Yaya?, A gaskiya ta cuci kanta da har ta bari soyyayar Raja ta shiga ranta, haɗuwarta da shi kuskure ce, fara kula shi da ta yi ma kuskure ne, maganar da suka yi kuakure ce, komai ma tsakaninta da shi kuskure ne, a she da da take cewa tana son Yaya faɗi kawai take a baki, yanzu ta fara soyyaya, sai a yanzu ne ta faɗa ramin soyyaya, sai a yanzu ne ta saka ƙafarta a soyyayar, sai a yanzu ne ta fara jin shauƙin soyyaya, amma me ya sa ?, Me ya sa ƙaddarorinta suke zuwa a haka?, Me ya sa duk wani abu me kyau da ta samu sai ya guje mata, don
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112