Skip to content

Chapter 78

Chapter 78

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ta na dudduba fuskarta ta ɗan hasken dake layin. “Rabi ina kika shiga haka?... Kusan kullum sai Fu'ad ya je nemanki makarantar da kike aiki, amma haka zai dawo yace min ba a sameki ba, har police station ya kai ƙara, amma babu wani bayani” Rabi ta ɗan yi murmushi ta na share hawayenta, a ƙalla de tana da wani wanda ya damu da ita a duniya, Allah ya sa har yanzu akwai wani wanda yake santa har zuciyarsa, kuma ta san da ma duk wannan tsawon kwanakin da ta shafe bata gidan babu wanda zai nemeta bayan Saratun. “Ƙaddara ce ta zaunar da ni a can, ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a kaina, irin abun da mahaifinmu yake shi ne aka aikata min, mutum biyar Anti Saratu, su biyar suka haikemin!” Saratu ta ƙara fashewa da kuka ta na rufe bakinta, tare da girgiza kanta. “Ki dena kuka Anti Saratu, ya wuce fa, Allah ya hukunta cewar dole sau hakannta faru da ni, kuma ga shi ya farun!” “Yanzu ina za ki je?” “Gidan kawu Habu zan tafi” Ta faɗa don ta san babu inda za ta iya zuwa a yanzu da ya wuce can ɗin. Anti Saratu ta gyaɗa kanta tana saka hannu a aljihun doguwar rigar jikinta, sannan ta zaro kuɗi wurin dubu goma ta kamo hannun Rabin ta danƙa mata. “Ga shi, ban sani ba ko za su amfane ki” Rabi ta karɓa, sannan ta gode mata, Saratu na tsaye a ƙofar gidan har Rabin ta fice daga lungun. Rabi na fita daga lungunsu ta wuce shagon Yaya, don ba za ta iya zuwa ko ina ba tare da ta sanar masa da halin da take ciki ba. “Ka yi shiru Yaya?” Rabi ta faɗi cikin hawaye, yayin da take zaune a kan benci tana kallon Yaya, bayan da ta gama tsara masa duk halin da ta shiga, da farko da Yayan ya ganta ya yi farin ciki, amma tun da ta fara bashi labarin abun da ya faru da ita sai ta ga yanayin fuskar Yayan ya sauya. “Ba komai” Yayan ya faɗi ya na kawar da kansa, mamaki ya bala'in kama Rabi, yau ita Yaya yakewa magana a haka?, ita ce ta masa magana ya amsa mata ciki-ciki?, me yake faruwa ne?. “Yanzu ya kake ganin za ayi” “Ai yanda za ayi kawai shi ne ki kama gabanki, dan ni babanmu ya min mata, kuma nan da wata ɗaya za ayi auren!” Da farko sai da Rabi ta ji wani irin duka a ƙirjinta, daga baya kuma sai ta yi murmushi me ciwo, to ita wai yanzu ma miye zai bata tsoro ne?, ai taskun rayuwa ba yau ta fara shigarsa ba, halayen ɗan adam babu kalar wanda bata gani ba, uban da ya haifeta ma ya ƙita, waye wani Yaya?, da dan har ya gujeta za ta ji ciwo?, ai da ma haka rayuwar take, wani zai soka da yini, sai ya ƙika da daddare,wani da ma can ba da zuciya ɗaya yake sanka ba, amma kai da ka so shi da zuciya ɗaya idan ka yi haƙuri Allah zai nuna maka ƙarshensa, ga shi yau ita ma ta ga zahirin Yaya. Hawayenta ta goge, dan babu amfanin barinsu su zuba, ba za ta ƙara barin hawayenta su zuba a gaban wani ba, ko kukan za ta yi gwara ta ɓoye a wani wurin ta yi, ganin hawayen mutum na ɗaya daga cikin lagonsa, 'A strong woman will always turn pain into power' haka ta faɗawa kanta, dan haka za ta yi iya bakin iyawarta don ta yaƙi abun da zai durƙusar da ita, saboda haka Yaya bai bata mamaki ba. Miƙewa ta yi tana murmushi ta kalli Yaya a tsakar ido tace. “To Yaya, Allah ya sanya da alkairi, ka gaida sabuwar amaryar, ni na tafi, sai bayan saduwa kuma!” Daga haka ta juya ta fice. Yaya ya ja wani dogon tsaki ya na jan wayarsa, shi mahaukacin ina ne zai yarda ya aureta bayan ta faɗa masa cswar maza har biyar sun mata fyaɗe?, ai yanzu a yanda take bata da maraba da karuwa, ko karan hauka ne ya cije shi ai ba ya yi wannan gangancin ba, gwara ta je ta can, ta ƙarata, wata ƙila ta samu wani ɗan tasha kamar babanta, sai ya temaka mata ya aureta, amma shi dai bai ga abun da zai yi da ita ba, da ma ba ita kaɗai ba ce budurwarsa, idan auren yake so ai sai ya zaɓi ɗaya daga cikin 'yan matansa ya ce zai aura, amma ba Rabi ba, dan a yanzu ta riga ta zama tarihi a rayuwarsa, shi da ma can don kyanta yake santa, yanzu kuwa da aka mata bajo a fuska ub*n wa ya aikeshi aurenta. * “Haka shi Ɗan Lamin yace” Cewar kawu Habu, bayan da Rabin ta gama masa bayanin abun da ke faruwa. Dan tana barin shagon Yaya gidansa ta nufa, durƙushe take a gabansa, yayin da shi kuma yake zaune a kan kujera. Rabi ta gyaɗa masa kai, idanunwata a bushe ƙamas, babu wani damshin ƙwalla ko ɗaya a ciki. Kawu Habu ya ci gaba da kallon Rabi cike da tausayi, ya girgiza kansa sannan yace. “Babu damuwa, tashi ki shiga ɗakin Laure” Miƙewa ta yi sannan ta shiga ɗakin matarsa ta biyu, wato Anti Laure, mace me kirki da karamci. Yaranta biyu da Kawu Habun. Zama ta yi daga bakin gadon Anti Lauren, inda ta sameta tana matsar ƙwalla, kasancewar inda suka yi maganar kusa da windown ɗakinta ne, dan haka Rabi ta fahimci cewar zancen nasu ta ji. “Sannu kin ji Rabi” Rabi ta yi murmushi ta na kauda kai. A hankali Ramatu matar Kawu Habu ta farko ta saki labulen ɗakinta, bayan da ta gama leƙen kawu Habun da Rabi, sannan duk abun da suka tattauna kaf a kunnenta, ita kuma a matsayinta na aminiyar Habiba, ba za ta yi shiri ba tare da ta sanar mata da labarin ba. Dan haka ta lalubo wayarta ta fesawa Habiba kaf abun da ya faru. * Cike da takaici Habiba ta wurga wayarta kan gado, bayan da ta gama sauraron bayanan Ramatun, ita ta ma manta da gidan Habun, ta manta cewar idan aka kori Rabi daga nan can za ta nufa, amma ba komai, wannan ma ba zai gagara ba, ita ta san abun yi. *No.181,Guzape, Abuja...* MISHAL POV. Tana kunna tv a falo aka turo ƙofar falon, hakan ya sa ta juya da sauri ba tare da ta kunna tvn ba, yanayinsa kawai ya bayyanar mata da halin da yake ciki, don ta riga da ta gama gane shi, abu ƙanƙani yake fusata zuciyarsa, kuma kusan kullum haka yake dawowa gidan. Ba ta ce masa ƙala ba face kallonsa da ta yi har ya wuce ɗakinsa, dan ta riga ta gano cewar idan ya na a fusace baya san a masa magana. Bakinta ta taɓe ta kunna tvn, sannan ta juya ta koma kitchen. Girkinta ta ƙarasa, sannan ta ɗebe komai ta shirya a kan danning. Ta dawo falo ta zauna tana kallo, ba ta shirya masa magana ba sai bayan shuɗewar muntuna kusan ashirin. Ta miƙe daga kan kijera, sannan ta nufi ɗakinsa. Bata ƙwanƙwasa ba,

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112