Chapter 10
Chapter 10
yi bata ga abun lafi ba. Ba ƙaramar tsorata Mishal ta yi ba, ta ji ƙofofin numfashinta na neman ɗaukewa, amma duk da haka ta daure ta shiga baza idanunta a falon. Tsaye a bakin kitchen ta ga Hajjara na wani irin murmushi me kama da na mugunta. Dama ita tasan za'a rina, shi yasa sam bata yarda da matar wan nata ba, dan ko abincinta bata ci, ita da kanta take girka abincinta. “Ka yi haƙuri Aky!...” Da ƙyar ta furta hakan, muryarta a shaƙe, dan bata san numfashinta ya ɗauke. “Baki da magana da ta wuce hakan ai, ke kullum cikin aikata laifi, yau kina wannan gobe kina wancan, ni kenan kullum cikin sintiri a hanyar makarantar ku!, Kin girma amma baki san kin girma ba, saboda Allah yanzu yarinya kamar ke ace bata san ciwon kanta ba?, to bari ki ji na faɗa miki idan har baki kama kanki ba, wallahi sai na saɓa miki!” Har yanzu cikin ƙaraji yake maganar, yayin da Mishal ta runtse idonta tana kawar da kanta gefe, duk da isashiyyar iskar dake falon ita sam bata iya jinta a huhunta, sam bata jin wata iska na kai mata inda ya dace. “Haba Abbakar? Ya haka dan Allah?” Mama ta faɗi cikin tausasawa. Abubakar na maida numfashi kamar wanda ya yi gasar tsere ya kalleta. Kafin a fusace ya fice daga falon. Hajjara ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, duk ƙaunar duniya sai a ce Mishal, komai Mishal komai Mishal, hatta da makarantar da take ta fi ta Hammad tsada, kuma har mota ya siya mata tare da ɗaukar mata driver, bayan ita nata ɗan a school bus yake tafiya. Koma dai miye yau ranta ya yi fari tunda har ya mata faɗa. Ta kaɗe gefen rigarta ta yi sama, dan taje ta bawa Fati labari. “Zauna Mishal...” Mama ta faɗi tana zaunar da ita, tare da sauƙewa jakar bayanta, ta ciro littafi a ciki ta shiga mata fiffita. Kafin ta samu ta dawo hayyacinta. “Kin sha maganinki ?” Kai ta gyaɗa mata tana miƙewa, ba tare da tace mata komai ba, ta ɗauki jakarta haɗi da lunchbox ɗinta ta fita. Mama ta bi bayanta da kallo, zuciyarta cike da tausayin yarinyar. “Allah ka kawo mata sauyin rayuwa!....” Wata ƙila ta faɗa a bakin 'yan amin, wata ƙila Allah ya zaɓeta ne dan ta zamo silar yin addu'ar wani abu dake shirin faruwa kwanaki masu zuwa. Addu'ar tata, ita ce ta zama silar faruwar wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwarta a 'yan kwanaki masu zuwa. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryuwar wasu lamura. *Brickhall School, Kaura district, Abuja* *09:40am* RABI'A POV. “Gashi, driverna na bawa saƙo ya siyo min, kuma ya ce ya nema amma bai samo irin wannan ɗayan ba, sai ɗan kwali ya samo...” Cewar Mishal, yayin da take miƙa mata lalle ɗan kwali. Rabi'a ta sa hannu ta karɓa. Tsaye suke a bayan ajujuwan makarantar, a ƙofar store, inda ake aje kayan share-share na makarantar. Rab'a ta juya ta kalli dama da hagun inda suke tsaye. “A ina zamu yi kenan ?” “Ga kujeru a can, muje mu zauna” Kuma da ga haka, suka ƙarasa inda kujerun suke, suka zauna, sannan Rabi ta shiga haɗa lallen. Yayin da Mishal ke dudduba jakarta, a ciki ta ɗauko biscuits, ta buɗe ta shiga ci. Cike da mamaki Rabi'a ta kalleta. “Bakya azumi ne ?” Mishal ta yi murmushi, har karafunan braces ɗin da aka sa mata suna bayyana. “Wahala ce ba zan iya ba, ga zuwa makaranta ga azumi, inaaa!” Rabi'a ta yi dariya, a kamaninta idan ka ganta sai ka ce tana da wasu shekaru masu yawa,amma da zarar ka yi magana da ita ko na minti uku ne za ka fahimci yarintarta ƙarara. “Shekarunki nawa ?” Mishal ta dakata da taunar biscuits ɗin dake bakinta, ta ɗan ɗaga olive green colour eyes ɗinta, tana san ta tuna shekarun nata. Kafin ta sauƙe su a kan Rabi'a dake ɗaure ledar lallen da ta gama haɗawa. “I’m 17, next year zan cika 18....” Rabi ta ɗage girarta cikin murmushi tana kallon lallen da ta gama ɗurewa. “Ki ce babbar yarinya ce...” Mishal ta yi dariya, wani abu da ba kasafai ta cika yinsa ba. “Ke fa shekarun ki nawa ?” “Ki ƙara biyu a kan naki” “Sha tara ?” Rabi'a ta gyaɗa mata kai. Ganin ta gama haɗa lallen yasa Mishal maida sauran biscuits ɗinta cikin jaka, tana karkaɗe hannunta, tare da taune sauran wanda ke bakinta. Ta miƙawa Rabi'a hannunta na dama, sannan Rabi'a ta fara zana mata lallen. “Wow!, Amma fa ta yi kyau” Mishal ta faɗi a karo na barkatai, sanda aka gama zanen lallen, ta ɗaga hannayenta sama yafi sau a ƙirga, sai kallon lallen take tana sakewa. Ba za ta ce when last rabonta da ba. “Nawa ne kuɗin lallen ?” Sai ta ga Rabi'a ta haɗe rai. “Shekaru nawa na baki ?” “Biyu” Ta masa tana mamakin abinda ya haɗa tambayar da ta mata da kuma wannan batun. ”Kinga kenan ni yayarki ce, kuma ina matsayin yayarki ai bazan karɓi kuɗin lallenki ba...” “Yanzu mun zama 'yan uwa kenan ?” Rabi'a ta gyaɗa mata kai tana murmushi. “Adawiyya ?” Zuciyar Rabi'a ta dunguwar a lokaci guda, Adawiyya?!, kaf duniyar nan mutane biyu ne ke kiranta da sunan, Ummanta, da kuma yayarta Baby!. *Unguwar Madallah, Suleja, Niger state* *05:30pm* “Wai har sun muku hutun?” Cewar Saratu, yayin da takewa Rabi ƙananun kalba. “An musu dai” Rabi ta bata amsa. Suna zaune ne a ƙofar ɗakinsu, bayan Rabi'an ta dawo daga wurin aikinta ne ta share gidan tas, duk da wahalar rana da kuma aikin da ta je ta yi, ga kuma azumin dake bakinta. Amma haka ta share gudan tas, kuma bayan ta gama ta ɗora da wanke-wanke. A lokacin Saratun tace mata ta zo su fara kalbar, tun da ta riga ta tsefe. “Ai har ke, tun da de ba za ki je makarantar ba har sai an koma” Rabi dai bata sake cewa komai ba, dan tun da ta ambaci kalmar 'makaranta', tunaninta ya tafi ɗazu, ta shiga tuna abinda ya faru tsakaninta da sabuwar ƙanwarta a ɗazun. “Jibi za mu tafi garinmu, a can za mu yi bikin sallah” Muryar Mishal ɗin ta katseta a ɗazun. Sai kawai ta yi murmushi. “Ina ne garin ku ?” “Maiduguri” Mishal ta bata amsa tana firfita lallen hannunta da iskar bakinta. Rabi'a ta gyaɗa kanta. Tana ƙara tabbatarwa da kanta hasashen da take a kan Mishal ɗin, na kasancewarta shuwa arab. “Shikenan, na san zuwa yanzu an koma break, bari naje na share inda aka ɓata, ki kula da kanki, Allah ya dawo da ku lafiya, sannan ki gaida Mamanki idan kin koma gida” Ta faɗi tana ƙoƙarin tashi, amma maganar Mishal ɗin ta gaba ita ce ta hanata tashin. “Mamata bata raye, kuma tun a sanda zata haifeni ta rasu, ban san babana ba ma, lokacin da cikina ya rasu, tare da yayana kawai na taso.....” Rabi'a ba za ta iya cewa ga abinda take tunanin ba a lokacin, tasan dai kawai ta tsirawa ƙaramar yarinyar ido ne, tana nazarin ya akayi ta rayu tsawon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112