Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ta yi ƙwafa, ta ma wurga mata harara, tare da kama hanyar kitchen. “Haka fa... Ai tsakanina da ke sai hange daga nesa... Babu yanda za ki iya da ni Hajjara... Na zame miki ciwon ido, kuma ƙadangaren bakin tulu!” Muryar Mishal ta dakatar da ita, juyowa ta yi ta kalli Mishal ɗin ba ita take kallo ba. Rubutunta ta ci gaba da yi, wata ƙwafar ta kuma yi sannan ta kaɗa kanta ta shiga kitchen ɗin. *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja* RAJA POV. Zaune suke shi da Zuzu a falo, suna tsara yanda za su karɓo wasu kaya da Alhaji Bala ya saka su su karɓo masa, a kai akai yake duba time. Dan ba ya san har lokacin ta shi ya yi ba tare da ya ganta ba. A kwana biyun nan kullum sai ya fita ƙofar estate ɗinsu dan ya ganta, ko ba ta yi masa magana ba, shi yana ɗaga mata hannu, kuma ganinta na masa daɗi, don ya na ganin Momma in her. Kuma shi ne dalilin da yasa ya ke san ganin nata. “...Ni zan fara zuwa, zan yi magana da su, idan ba su yi taurin kai ba... Shikenan, idan kuma sun yi taurin kai... Sai kawai kai ka fahimtar da su...” Raja ya gyaɗa kansa cike da gamsuwa. Sannan ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. “Na fahimta” Idonsa ya ƙara sauƙa a kan agogo, ganin lokacin ya cika yasa shi miƙewa. “Ina zuwa Zuzu...” Daga haka ya yi hanyar fita. Zuzu ya yi murmushi, dan ya harbo jirginsa, ko su kansu za su so ya samu wannan yarinyar me kama da shi, tun da duk lalacewarta ita musulma ce, ba kamar Uchechi ba. Duk da suma ba hankali suka cika ba, amma sun san abinda ya dace. RABI'A POV. “Sorry Anti Adawiyya...Wallahi na je class ɗin kung fu ne, shi yasa na makara” Cewar Mishal a sanda ta matso kusa da Rabi'a dake jiranta a compound ɗin makarantar. Rabi'a ta yi murmushi. “Karki damu ƙanwata” Mishal ta miƙa mata ƙatuwar ledar dake hannunta, sannan tace. “Ga shi Anti...” Rabi ta sa hannu ta karɓa,bkafin ta buɗe ledar tana duba abin da ke ciki, atamfofi da lesuka ta gani a ciki, kuma da alama kayan a ɗinke suke. Mishal ta ci gaba da kallonta cike da tausayawa, don tun bayan da ta bata labarinta tausayinta ya ƙara kamata. Kuma a jiya bayan ta koma gida, ta ɗebo gaba ɗaya kayan sallarta da tai alƙawarin kai mata, ta haɗo da duk wani kayan atamfa da ta san ba sawa take ba, ta haɗa ta aje da zummar za ta kawo mata. “Sis...” “Pls don't... Tun da har kun zama 'yan, to babu godiya a tsakaninmu” Ƙwalla ta taru a idon Rabi, amma sai ta gyaɗawa Mishal kai. “Zan wuce... Baba Ali ya zo tun ɗazu, Sai gobe” Ta ƙarashe ta na barin wuri, Rabi ta rakata da murmushi. Mishal na isa wurin da motar Baba Ali take ta faɗa ciki. “Hafsatu ya aka yi kika makara yau ?” Muryar Baba Alin ta tambaya, yayin da yakewa motar key. “Malamin kungi fu ɗinmu ne ya makarar da mu” Bai sake ce mata komai ba, ya juya kayan motar suka fita daga makarantar. A tsallaken makaranatar idanuwanta suka hango mata shi, wannan fuskar irin ta Adawiyya. A lokacin da ta ganshi, ta ɗauka cewa ɗan uwanta ne, amma sai ba ta cewa Adawiyyan komai ba. Ta jira har zuwa lokacin da Adawiyyan ta bata labarin rayuwarta. Ta yi zaton zata ce mata tana da wa na miji, amma ba ta ji hakan ba. Kuma rashin jin hakan ne yasa ta ɗora ayar tambaya kan lamarin, duk yanda aka yi Adawiyya ta haɗa jini da abokin yayanta. Dan kamar ta wuce kama haka kawai. Sai mamakin son sanin abin da ya kawo shi wurin ya kamata, me yake a nan ɗin?, sannan me yasa yanayinsa ya sauya ?, duk da a sanda ta ganshi yana cikin halin jinya, hakan bai hanata ganin buɗar idonsa ba. Sai dai yau kuma idon nasa kusan a lumshe suka. Ko dai ba dhi da lafiya ?. Da saƙe-saƙen nan a ranta har suka bar layin suka hau kan titi. Rabi na fita daga gate ɗin makarantar idanuwanta suka hango mata shi tsaye daga can tsalleka, ya jingina da jikin bango, sanye yake cikin wata orange T-shirt, da farin chinos trouser. Hannaynesa duka biyu sanye cikin aljihun wandonsa. Waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallonta ƙasa-ƙasa. Kusan kullum a kwanakin nan sai ta ganshi tsaye a wurin, ba ta san me yake ba, amma kamar jikinta na bata cewar bibiyarta yake, ko kuma yana tsayawa ne a wurin kawai dan ta fito ya ganta. Kanta ta ɗauke, tare da gyarawa ledar hannunta riƙo. Ba tare da ta sake kallonsa ba, ta kama hanyar da ta saba bi. Sai da Raja ya gama ƙare mata kallo, zuciyarsa na faɗa masa abubuwa da dama a kanta, kafin ya ga ta kama hanya tana tafiya. Wani abu daga can ƙasan zuciyarsa yace masa kawai ya bita. Bai yi wata-wata ba wurin bin umarnin, ƙafafuwansa suka soma takawa cike da nutsuwa. Har ya kai kusa da ita, a yayin da suka ci gaba da tafiya tare. Rabi ta yi saurin juyowa ta kalle shi, jin an tsaya kusa da ita, wannan fuskarce dai, mamallakin fuskar ne ke biye da ita. Sai dai ba ita yake kallo ba, hanya yake kalla, kuma har zuwa lokacin hannayensa cikin aljihu. “Sannu Ammata!” Wannan salihar muryar tasa ta furta ya na ci gaba da kallon hanya, sai da gaban Rabi ya faɗi, saboda yanda amon muryar tasa ya kunna wata jiniya a cikin kanta. Ta haɗiye wani abu sannan tace. “Sunana Rabi'a...” “Na sani ai, Ammata!” Ya yi hanzarin katseta. Rabi ta ɗauke kai tana kallon hanyar ita ma. “Daga ina kike zuwa nan ?” Ya tambaya yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, tare da zaro hannunsa na dama daga cikin aljihu, ya kaishi bayan wuyansa, saitin inda tatto ɗin kan zaki yake, yana sosawa. Rabi ta ɗan kalleshi kaɗan, sannan ta amsa da. “Unguwar Madallah, Suleja!” Ta lura da yanda ya ɗan tsaya da tafiyar da yake, kafin kuma ya ci gaba, sai a yanzu ya kalleta tun bayan da ya tsaya kusa da ita. “Kusan tafiyar muntuna arba'in fa kenan ?” “Umhum” Ta amsa da ɗan sakewa, ba kamar yanda suka fara hirar ba. “Amma me yasa kike zuwa nan ?” Rabi'a ta ɗan sunkuyar da kanta ta kalli yatsun ƙafarta, sannan tace. “Aikin shara da goge-goge nake” “Ba kya zuwa makaranta ?” Ya kuma tambaya. Sai ta gyaɗa kanta. “Eh, ba na zuwa..” Ta ba shi ahi amsa a dai-dai lokacin da suka iso bakin titi, sai ya dakata, hakan yasa Rabin ma dakatawa. Shiru ya ratsa tsakaninsu na 'yan wa6sy muntuna... Kafin Raja ya ɗaga hannunsa ya tsayar wani mai mota, sannan ya buɗe mata gidan baya. “Zo ki shiga 'yan mata!” Rabi ta kalleshi,sannan ta kalli motar. “Akwai bus...” “Ammata ba'a mun musu, just enter, kin fahimta ?!” Rabi'a ta haɗiye wani abu, dan ya yi maganara ne yana kallonta da ƙwayar idonsa da take gray color. Ta tara yaɗonta gu ɗaya, sannanta shiga bayan

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112