Chapter 82
Chapter 82
ta saki wata siriyar tusa, shikenan, wata ƙila tata ta ƙare, kenan da Rabin ta bar gidan Abubakar ba can ta yi ba, tun da ga shi su ma nemanta suke, amma garin yaya har aikin nan ya karye?, don kuwa ita ta san ta sa a yiwa 'yan uwan Maryam aikin da duk tsawon shekarun da Rabi za ta yi a gidan ba za su taɓa neman ganinta ba. “Amma waye kai bawan Allah, ko daga Haɗejia kake ?” Raja ya sosa kansa ya na faɗin. “Sunana Zaid, kuma ba daga haɗejia nake ba” “Laaa!, da ma kai ne Zaid ɗin, ai ko Rabi ta na yawan bani labarinka, sai dai ko da wasa ba ta taɓa faɗa min cewar kuna kama ba” Raja ya ɗaga kafaɗarsa ya na faɗin. “Allah sarki” “To Rabi dai ba ta gidan nan, satin da ya wuce Umma ta koreta, ita kuma sai ta koma gidan kawu Habu, gidan na ɗan gaba da mu” Da farko har hankalin Habiba ya kwanta, jin shi wannan bawan Allahn ba daga haɗejia yake ba, amma kalaman Saratu su ne suka dawo da tsoron sabo. Kuma cikinta bai ƙara rikicewa ba, sai da Raja ya juya ya kalli side ɗinta. Hatta da idanuwansa irin nata ne, banbancin kawai shi ne na sa a lumshe suke, kuma ƙwayar cikinsu kalar ruwan toka ce. Raja ya dawo da dubansa kan Saratu. “Ko za mu je ki raka ni gidan shi kawun?” Ya faɗi wani abu na masa ɗaci a maƙwagoro, dole ya san yanda zai yi da matar nan, dan ko me ya samu Ammatansa ita ce sila. “Innallillahi wa inna ilaihi raji'un... Zaid wai sun ce tun washe gari shi Abba ya zo ya yi masifa kan sai Kawu Habu ya koreta, kuma tun a ranar ta bar gidan nan ɗin” Abun da Saratun ta faɗi kenan, bayan da ta shiga gidan kawu Abubakar ta fito, Raja dake jingine da ƙofar gidan ya gyara tsatuwarsa ya na kallon bakinta, dan so yake ya fahimta shin, da wani yare ma take magana ne?, shi fa bai gane ba, Ammatansa ba ta gidan nan?, to ina ta tafi?. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *21* ~~~ *Look out for those who look out for you. Loyalty means everything...* *** *Unguwar Jama'are, Haɗejia...* RABI POV. “Wai har kun dawo?” Cewar kakarsu Hajiya ta na binsu da kallo, dawowarsu kenan daga kasuwa, sun je siyyayar kayan biki, don a yanzu haka bikin saura wata ɗaya, sai shirye-shirye ake a gidan, duk sun zuzzube a falon Hajiyan suna maida numfashi. “Wallahi Hajiya, kin san yau Lahadi... To kasuwarce a cike, ko siyyayar ma ba mu gama ba, kawai mun dawo ne, kin ga ko zuwa gobe ne sai mu ƙarasa siyyayar” Cewar Kairiyya ta na cire hijabin jikinta, Hajiya ta gyaɗa kai ta na kaɗe ƙuda daga kan furarta. A dai-dai lokacin Nafisa ta shigo, wadda take daga ɓangaren mahaifiyarta, dan ita bata bisu kasuwar ba. Zama ta yi suka shiga firfitar da kayan da suka siyo. “Ku wai ni yanzu wa za mu nema ya mana lalle?” Momi ta tambaya ta na ɗaga wata doguwar riga cikin kayan da suka siyo. “Akwai wannan Balkisan, ƙawar anti Shafa (Yayar Kulsum), ita ma ta iya lalle” Cewar Nafisa. “Ku na iya lalle fa, ku bari sai na muku” Rabi ta faɗi tana dudduba nata kayan da ta siyo. “Ke kuma a ina kika koyi lalle?” Jidda ta tambaya. “A can mana” “Ai kiwa ke za ki mana” “To ke wa zai miki ?” Fati ta tambaya. “Sai ku kira min wadda kuka ce za ta muku da farko, sai ta min” Kamar yanda suka saba a kwanakin haka suka shiga hirar bikin, dan daga zarar sun zauna kamar haka ba su da hira da ta wuce ta bikin. Rabi'a ta saki jikinta a cikinsu tana sha'aninta, sai a yanzu take jin kamar rayuwarta ta setu, sai a yanzu da ta dawo cikin 'yan uwanta farin cikinta na da ya dawo, har wata ƙiba ta yi a cikin satin. Kuma babu wani abu dake damunta face shi, wannan sunan; Raja!, har zuwa yau ba ta manta shi ba, ta yi iyaka i yinta amma ta kasa, ko bacci za ta kwanta da ta rintse idonta za ta hango waɗanan lumsassun idanuwan nasa. Ba za ta yi wa kanta ƙarya ba,ta san a cewa tana kewarsa!. KULIYA POV. Ya na daga zaune a falo ya na dudduba wani aiki a cikin ipad ɗinsa, hannunsa na dama riƙe da mug ya na shan coffee. Kamar daga sama ya ji muryarta a kansa. “Abu Aswad... Barrow me your phone please” Kansa ya ɗaga ya kalleta, mug ɗin kare da bakinsa, kamar kullum sanye take cikin ƙananu kuma ɗangallallun kayan da ta saba sakawa, shi har mamaki ma ya yi, a sanda ta faɗa masa cewar kaf cikin kayanta babu atamfa da lace ko makamantansu, ban da ƙananun kaya ba ta da wata sutura, hannunta na dama riƙe yake da littafi, yayin da na hagu kuma yake riƙe da pen. Gashin kanta nannaɗe cikin bun. “Me za ki yi?” Ya tambaya ya na ɗaga kafaɗarsa, tare da aje mug ɗin hannunsa a kan coffee table. “Assignment zan yi please” Sai ya ɗan kalleta na wasu sakkani, kafin ya aje ipad ɗin hannunsa, ya kamo nata hannun na hagu ya zaunar da ita kan cinyarsa. Ya na shirin sakin hannunta ya lura da hannun nata ya yi jajir sosai, kamar wadda ta ƙone. Hannun nata ya saki ya na kama waist ɗinta da hannunsa ɗaya. “Me ya samu hannunki?” Ya tambaya ya na gyara mata gashin kanta na gaba, Mishal ta shaƙi wata iska, kafin tace. “Wani malami ne ya dake ni” Kuliya ya miƙa hannunsa ya ɗauko wayarsa ya miƙa mata. “Me kika yi?” Ya tambaya a hankali. Sai ta turo bakinta gaba. “Note ne ban yi ba... Ai Wallahi da da ne shi ma bai isa ya dake ni ba... Yanzun ma de kawai...” Sai ta yi shiru tana daddana wayar tasa. Kuliya na kallon fuskarta yace. “Yanzun ma dai me?... Yanzu kin girma ko?... Kin zama matar aure” Ta ɗan yi dariya, ta na kallon wayarsa ta amsa masa da. “Ba haka ba ne... Kawai de dan Anti Adawiyya ta min faɗa ne, ita tace duk malamin da ya min wani abu na ƙyaleshi kawai, malamai ba sa cuta sai dai gyara, idan kuma mutum ya cuceni na barshi da Allah, Allah zai saka min, shi ne fa ya sa na yi sanyi, amma ni da akwai malamin da ya isa ya dake ni!...” Kuliya ya ci gaba da kallon bakinta dake furta kalaman, tsakaninta da Allah take bayananta, duk abun da Mishal za ta faɗa daga zuciyarta yake fitowa, ba ta san wani abu ba wai shi ƙarya, kanta tsaye take furta zantikanta, maganar ta ci gaba da masa idonta kan wayar, yanda ta sauƙe su ƙasa sai ka ce rufe su ta yi, dogayen gashin idonta sun kwanta a kan fuskarta, hasken wayar ya ƙara haska masa fuskarta, sai ya ji kamar ya saka makulli ya buɗe zuciyarsa ya sakata a ciki ya kulle, ya nesanta ta daga duk wani abu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112