Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

bata wuce wata biyar ba. Su ne zaune a kan danning table. Wanda ke shaƙe da kayan buɗe baki kala-kala.Da alama jiran kiran sallah suke, dan ƙiris ya rage a kira sallahr. Ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan falon ce ta buɗe, farko keken guragu ne ya fara bayyana, zaune a kan keken kuma, wata matashiyar yarinya ce, wadda ba za ta wuce 9yrs ba. Kallo ɗaya zaka mata ka ga nakasarta, dan bata da hannaye gaba ɗaya, sannan kanta a langwaɓe gefe guda, bakinta nazubar da yawu. Mishal ce ta biyo baya,wadda ita ce ke turo keken, sanye take da wata farar linen tunic dress, da kaɗan rigar ta sauƙo gwiwarta, ga kuma rigar ko hannu bata da shi, kanta babu ɗankwali kamar yanda ta saba zama, gashin kanta tifke cikin braid(kalaba) guda ɗaya, ta saka hair band daga sama. Gaba ɗayansu suka kalli wurin, kuma daga Hajjara har mijin nata basu ɗauke idonsu a kansu ba har suka ƙaraso danning area ɗin. Kujera ɗaya Mishal ta kawar ta mayeta da keken Firdaus, wadda take kira da Daala. Sannan ita ma ta samu kejera kusa da ita ta zauna, sai da ta ɗauki tissue ta gogewa Daalan yawun da ya zubo mata sannan ta juyo tana kallon mutanen dake kan danning ɗin. Hajjara ta kawar da kanta tana taɓe baki, Allah ya sani, har cikin zuciyarta bata san Mishal, wata ƙila dan igiyar aurenta da ta taɓa zama sanadiyyar tsinkewa ne, ko kuma dan rashin kunyar da take mata. Mishal ta kalli yayanta,wanda shi ma ita yake kallo, hannunta na dama ta ɗago, wanda ke riƙe da envelop, ta miƙa masa. Abubakar ya girgiza kansa, ya san duk yanda aka yi wani laifin ta aikata, ba yau ta saba kawo takardu irin wannan ɗin ba, hasalima suna nan tili guda yana ajewa, dan sun ma fi yawan report ɗin ta na makaranta da take kawowa. Abu ɗaya ne yasa ba zai cireta daga makaranta ba kwata-kwata, hazaƙarta ce tasa hakan, dan ba ma shi ba, hatta da makarantar suna tinƙaho da ita, gashi de ba wasu shekaru ne da ita ba, amma girman jikinta ne zaisa ka zaci wata babbace. “Me kuma kika yi ?” Ya tambaya yana karɓar envelope ɗin, kanta ta sunkuyar, tana wasa da yatsunta. Murmushi kawai ya yi a sanda ya buɗe ya karanta, dan bi da bi ya gama haddace kalaman da ke ciki, saboda a kullum abu iri ɗaya suke turo masa tun tana junior. Ya rasa irin abunda ke damun ta. “Hammad yace min yau baki yi azumi ba, bayan shi ma yau yana yi” Ta ɗago da kanta ta kalli Hammad ɗin dake gefen uw*rsa, kamar yanda bata san uwa*r yaron shi ma haka ta tsaneshi, dan kaf halayen uw*rsa babu wanda bai ɗauko ba. “Saboda makarantar da nake zuwa ne...” “Makaranta sai ta hanaki azumi?” Sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin. “Bari na je waje.....” Bayanta ya bi da kallo yana mamakin halin yarinyar, du-du-du ba za ta wuce 17-16 ba, har yau yana tuna yanda ya ɗauketa da hannayensa ranar da aka haifeta, da kuma irin maganar da mahaifiyarsu ta masa a wancan lokacin. _“Sadiq, ka kula da ita, nasan za ta tashi cikin maraici, bata da kowa sai kai, kada ka danƙa renonta a hannun kowa, ciki kuwa harda Amma (tana nufin mahaifiyarta), ka kula da ita, ka kula da ita......”_ Kuma kalamanta na ƙarshe kenan, a kan idonsa a ka shiga da ita ɗakin tiyata. sai kawai fito masa aka yi da jairiya, aka ce ta haihu, amma ta rasu sai dai babyn da ta haifa. “Wai haka za'a zuba ido ana kallon yarinyar nan tana abinda take so?.....” Hajjara ta faɗi a ƙufule, dan Allah ya sani ta gaji da halin yainyar, kuma da ma tun sanda ta ɗora idonta a kan yariyar ta washeta. “Me ta yi ?” Ya furta hakan cikin halin ko in kula, yana ninke takardar da Mishal ɗin ta bashi. “Jiya fa na yi baƙi, baka ga rashin kunyar da ta min a gabansu ba” “Yarinta ce take damunta, idan ta girma za ta dena” Haushi kamar ya kashe Hajjara, dan dama abin da ya saba faɗa mata kenan, a duk sanda ta kawo masa ƙarar Mishal ɗin, yau ɗin ma tsautsayi ne yasa ta kawo ƙararta, a ranta ta yi ƙwafa, Allah ya kawo ranar da za ta ga bayan yarinyar nan. Idonta ya sauƙa a kan Daala dake ta zubar yawu, ita ma yarinyar Hajjaran take kallo. Tawarta ɗaya kenan a duniya, wannan yariyar da Allah yasa ta haifota a nakashe, kuma nakasar yariyar yasa ta gujeta, babu wani abu dake shiga tsakaninta da yariyar irin na uwa da 'yarta, Mishal da Naani ɗin da Abubakar ya ɗauko su ne ke kula da yarinyar har wa yau. Mishal na fita daga falon gidan BQ ta wuce, dan bata da wurin zama a gidan da ya wuce BQ ɗin, in baka sameta a BQ ba zaka sameta tare da Daala suna wasa, dan Allah ya ɗora mata ƙauna da tausayin yarinyar. Ganin yanda Hajjara ke bagarar da lamarin yarinyar saboda nakasar dake tare da ita, ita kuma Allah ya hallici zuciyarta da wani irin tausayi, kuma tausayin ne ke sakawa bata da aminan hira a gidan sai masu aikin gidan. A bakin ƙofar BQ ɗin ta tsaya, tana ƙare musu kallo. Mutum biyar ne zaune a kan bujukura. Ladi, wadda ita ce ke kula da Daala sai mijinta Malam Audu, wanda ke musu gadi, sannan Khalifa, ɗan Mama Ladin na farko, wanda shi ne yake musu sharar garden da ta compound da ma aike idan ya taso, sai Shatu 'yar Mama Ladin ta biyu, sai autar Mama Ladin wato Ummul. A taƙaice de duka ahalin Mama Ladin ne, waɗan da suka kasance ahalinta ita ma, dan bata da wurin zuwa da ya wucenasu, Shatu kuma ita ce wadda zata iya kira da ƙawarta, Mama Ladi ta zame mata uwa. “Ah-ah, Hafsatu, ƙaraso mana” Sai ta yi murmushi har ƙarafunan braces dake saman haƙwaranta na bayyana, tana ci gaba da kallonsu, su ma sai hadaniyar haɗa kayan shan ruwansu suke, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka ci gaba da takawa har zuwa kan bujukurar. Guri ta samu kusa da Shatu ta zauna. “Yau kin yi azumi ?” Mama Ladi ta tambaya, yayin da take juye tiyara a cikin wata doguwar roba, Mishal ta girgiza kanta. “Ban yi ba” “Haba uwata, sau nawa zan faɗa miki cewar kin isa azumi ?, bai kamata ace ki na shan azumu ba gaira ba dalili ba” Cewar Malam Audu yana aje radion hannunsa. “Rabu da ita Baba, ai kullum gaya muku nake cewar yarinyar nan raguwace, amma bakwa yarda” Cewar Khalifa. Mishal ta turo baki gaba tana sosa kanta. “Allah ni ba raguwa ba ce, a class ɗin Kungu fu ɗinmu fa kullum ni nake zuwa a farko, kuma watan da ya auce ma saida na karya wani malamin mu....” Hannunta ta kai ta rufe bakinta, sakamakon suɓul da bakan da ta tuna cewar ta yi, dan tasan yanzu Mama Ladi za ta shiga mata faɗa. “Kema kin san cewa ba dai-dai kika yi ba kenan, shi yasa kika rufe baki” Cewar Mama Ladin

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112