Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

MISHAL POV. Zaune take a ɗakin da yake a matsayin nata. Don ba yau suka saba zuwa Maidugurin ba, hasalima suna zuwa akai-akai. Kuma idan sun zo ɗin a babban family house ɗinsu suke sauƙa. Duk da kasancewar gobe sallah, amma gidan har yanzu be rabu da zuwan baƙi ba. Tun daga hayaniyar dake tashi a gidan za ka gane hakan. Ba su dameta ba, Don Kullum ba ta fita, tana ɗaki, bata san ta fita su haɗu da Yazid. Yazid?, wani mutum da ya so lalata mata rayuwa, wannan mutumin da duk duniya bata tsani wani mahaliƙu kamarsa ba. Shi ne wannan mutumin da a sanadiyyarsa ta gamu da ciwon hysterian da take da shi a yanzu. Kuma dan abun a family ya faru, haka aka rabu da shi ya ci gaba da yawonsa. Yana shiga cikin 'yan uwa kansa ɗage a sama, kamar bai aikata komai ba. Ita kuma da aka yi ƙoƙarin cutarwa ita ce ke ɓuya, ita ce ke ɓoye kanta da barin shiga dangi, har yanzu gani take kamar idan ta idan ta shiga cikinsu suna ganin wannan tabon a jikinta ne. Duk da Allah bai sa ya haike matan ba, amma tana jin zafin abinda ya mata a ranta. A duk sa'ar da za ta ganshi ji take kamar ta fasa ihu, a wasu lokutan ma ganin nasa kawai shi ne ke tada mata ciwonta. Ta ɗan ja gutun tsaki tana ci gaba da buɗe littattafanta. Ita ta tsani aikin makaranata, dan de ba ta san ɗan uwanta ya yi asarar kuɗin da yake kashewa a kan makarantar ta a banza, amma da ba za ta na maida hankali ba. Gashi dai hutun sati ɗaya a ka bayar, saboda ba ƙarshen term ba ne, a tsakiyar term aka basu hutun, amma sai da suka haɗo su da holiday project. Kuma tun barowarsu Abuja abun da take ta ƙoƙarin yi kenan. Amma har yanzu ta kasa gamawa. Ta kuma jan wani tsakin tana ture littatafan, duk aikin ya gundureta, fita take san yi, bata san zaman gidan gaba ɗaya. To amma ta fita ta je ina ?, ta san in ma fitar ce ba za'a barta ta fita ita ɗaya ba, dole za'a haɗata da wani. “Baby!” Kamar daga sama ta ji muryarsa yana kiran sunanta, sunan da kaf duniya babu me kiranta da shi sai 'yan gidansu. Tasan da cewa za su zo, amma ba ta san cewa yau za su zo ɗin ba. Da sauri ta miƙe ta fita daga ɗakin, a falo ta same shi yana ta nemanta. Yana ganinta ya sakar mata wani kyakkyawan murmushin. Da gudu ta ƙarasa kusa da shi, kuma tana zuwa jikinsa ta ɗale shi, duk tsayinsa amma saida ta riƙe masa wuya. “Tun sanda muka zo nake ta nemanki” Wannan dakakiyar muryar tasa ta faɗi. Ta yi kewarsa da ma duk wani ɗan gidansu, dan za ta iya cewa duk familynsu babu wanda take so kamar 'yan gidansu, duk da su ma a Abuja suke da zama,amma bata gajiya da ganinsu. Sunansa Arman, ɗa ne a wurin cousin ɗinta Nimra, wadda ta kasance soja me riƙe da muƙamin general na nigeri. Yaranta uku Arman, Iqra sai Ijaz, kuma gaba ɗaya yaran nata sojoji ne. Wani abu dake ƙara burgeta da gidansu kenan. “Ina Iqra da ijaz?” Ta tambaya tana sakinsa. Kanta a sama wurin kallon fuskarsa, sbd tsayin da ya fita. Kasancewar shi dogo ne, ita kuma gata ba wani tsayi gareta ba. “Suna waje, har da su Ammy muka taho” Zuciyarta kamar ta fito waje don murna, Allah ya dubeta yasa ba za ta yi bikin sallah lami ba, dan tunda har duka mutanen gidansu suka zo, to shikenan, matsalarta ta zaman kaɗaici ta yanki. *Unguwar Madallah, Suleja, Niger State* *07:44am* RABI'A POV. Ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, kallo ɗaya za ka mata fahimci hakan, saboda daga kun haɗa ido za ka ga ta maka murmushi, duk da dama ita gwanarsa ce. Amma na yau ya fi na kullum. Jin kanta take kamar kowa, yau Allah yasa ita ma ta saka sabon kayan da za ta tafi idi da shi. Saɓanin sauran shekarun da ta shafe a gidan, a da sai dai Saratu ta bata kunce ta saka. Amma yau ita ma gata da nata sabon kayan, sai dai duk da haka bata da takalmin sakawa, shi yasa Saratu ta bada ɗaya daga cikin nata, Da murnarta ta zangari takalmin ta saka. Tun da ta fito daga wanka ta saka kayan Mama ke binta da kallo, amma ba ta ce komai ba, har suka shirya suka fito dan tafiya wurin idi. Rabi ba ta san sanda Mama ta dawo gidan ba, ita dai kawai ta farka ta ganta. Kuma ba ta ce komai ba, ta ja bakinta ta yi shiru, tun da har uw*rta tasan abin da take. A bakin ƙofar ɗakinsa suka ga babansu, kowa a cikinsu ya wani ɗauke kai babu ma mai shirin gaishe da shi, sai Saratu da ita, kuma shi ma bai wani amsa musu da mutumci ba, sama-sama ya amsa su. Ita kuma Rabi ba ƙaramin mamakinsa take ba, kusan kwanansa huɗu baya gidan, ko jiya har suka kwanta ba ta ga dawowarsa ba, wata ƙila ma da asuba ya dawo, don ba ƙaramin aikinsa ba ne. Mutumin da ya taɓa kawo karuwa cikin gidan matarsa ta auren sinnah, ai fiye da haka ma zai aikata.. “Ah-ah, Karfa, a ina kuma kika samo sabon kaya ?, in ji dai ba sata ki kai ba?” Muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta juyo da sauri ta kalleta. Rabi ta tsorata, dan jiya basu san an bata wani kaya ba, tana shigowa da ahi ɗaki ta shige, Anti Saratu kawai ta nunawa. “Saurayinta ne ya kawo mata, ba sata ta yi ba” Saratu ta bata amsa. “Sh*iya munafuka! Ashe jiya da kika je siyan katin tsayawa ki kai a lungu ya gama lalube ki sannan ya baki kaya?” Habiba ta faɗi cikin kama baki. “Ai ni na jima banga baƙar munafuka irin wannan yarinyar ba, kin ga fa jiyan da ta dawo, ɓoye kayan ta yi a cikin hijabinta, dan kada mu gani” Mama ta faɗi tana aika mata harara. “Ya isa haka dan Allah, to duk sharrinku a ƙofar gida ya bata, da za ku ɗorawa marainiyar Allah shari, dan Allah Umma ku riƙa duba baya, idan an giram a san an girama” “Kan abu ta kaza-kazacan!, Saratu! Ni ki ke faɗawa irin waɗanan maganganun ?.....” Sararu ta juyar da kanta gefe daga barin kallon Umman, ta kalli Rabi wadda hawaye suka wanke mata fuska tun a sharin farko da aka laƙa mata. Hannunta ta ja suka fita daga gidan, dan ta ga kamar su basu da niyyar zuwa idin, su da suke da niyya gwara su yi sauri, don kada su rasa. Da sauri Ɗan Lami ya bi bayansu, dan ko ba komai yasan akwai 'yan kuɗaɗe a hannun Saratu, shi kuma kuɗaɗen da ya ara sun ƙare kaf, bai ta shi da ko sisi ba. Kuma gashi yana san zuwa idin, ko ba komai Saratun za ta masa kuɗin babir. “Umma da alama fa sai kin ɗau mataki...” Cewar Mama. “Ni kuwa na ga hakan, kada

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112