Skip to content

Chapter 98

Chapter 98

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

“Wai da baki nake san yi” Cikin sakan ɗaya wannan fara'ar da ta ɗauke a ɗazu ta dawo, da rarrafe ta ƙarasa kusa da shi tana ɗora hannayenta a kan cinyarsa. “Da gaske wai?... Yaushe?” Kansa ya girgiza. “Sai bayan kin yi candy” Fuska ta kuma ɓatawa tana ɗaukewa hannunta daga kan cinyarsa, bakinta ta turo gaba tana juya masa kai. “To wai kai sai ka sawa mutum rai a kan abu kuma ka zo ka hana shi” Shi de bai ce mata komai ba, ya ci gaba da kallonta yana murmushi. “Ni dan Alah ka bani yanzu” Ta kuma faɗi tana masa fuskar tausayi. Kansa ya kuma girgizawa yana ɗaga kafaɗarsa. “Dan Allah Love Muffin!” Ta faɗi tana kamo fuskarsa, idonta ya cika da ƙwallar kukan shagwaɓa. “A'a fa?!” “Ni dan Allah ka bani ina so....” Kuliya na dariya yace. “Ba matsala ke kika nema ai!” * “Hafsat!” Kuliya ya ƙara kiran sunanta a karo na barkatai. Mishal dake duƙunƙune cikin bargo tana hawaye ta masa banza tana share hawayen. “Magana fa nake...” Ya faɗi yana taɓota. Hannunsa da ya taɓata da shi ta doke. “Ni ka rabu da ni... Kuma Allah sai ya sakamin... Ashe dama ba kayanka ne baƙaƙe ba ka ɗai, zuciyarka ma baƙa ce” Ta faɗi cikin kuka tana ƙara duƙunƙunewa. Kuliya ya ƙunshe dariya yana faɗin. “To me na yi?... Ke ce fa kika ce kina buƙata” Kuka ta fashe da shi tana rintse idonta gam. “Allah ban yarda ba... Kuma idan muka haɗu da Anti Adawiyya sai na faɗa mata abun da ka min” Dariya ya yi mara sauti yana kwanciya a gefenta. “Ki yi haƙuri to” “Anƙi a haƙura ɗin... Wayyo Allah na Anna... Wayyo Aki... Wayyo Anti Adawiyya!” Ta ci gaba da faɗin abun da take faɗi a ɗazu. “Kuma Allah sai ya mana hisabi, wannan sunansa zalunci, kuma Allah ya hana zalunci...” Juyowa ya yi yana kallonta, duk da tana lulluɓe da bargo. “Wai ba a muku biology ne?... Ya kamata a ce an muku a biology” “An mana ai... Ai an mana, amma ai basu ce da wahala irin haka ba... Wayyo Allahna!” Ta faɗi tana ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, saboda ƙasusuwanta da suke mata ciwo, ga wani zazzaɓi dake shirin rufeta, wani irin sanyi take ji yana shiga ko wace kusurwa ta jikinta. Kuliya ya yi dariya me sauti a wanna karon. “Ai da ma ba za su faɗa muku cewar akwai wahala ba” “Dariya kake min ko?...Ko... Ko?... Ko?” Ta ƙarashe tana fashewa da wani kukan. A hankali ya buɗe blanket ɗin, har ya samu damar ganin fuskarta, ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye, ga kuma jan da fuskar ta yi, gashin kanta a yamutse, idon nan ma a koɗe. “Ki yi haƙuri please!... My bad, and I'm truly sorry” Ya faɗi yana rungumeta daga kwancen da take, dukan ƙirjinsa ta shiga yi, dan ita yau gani take nan duniya bata da maƙiyi kamar shi. “I hope we can move past this, ko kina so ni ma na yi kukan?” Sai kuma ta tsaya da dukansa da take, jin yanda muryarsa ta fito a sanyaye. Ta dakata da kukan tana kallon fuskarsa, wadda ya mata yanayin abun tausayi. “To ni ka min alƙawarin ba za ka sake min ba!” Cabɗi jam!, ai wannan ai shi ne wasa farin girki, ya faɗi a zuciyarsa, a fili kuma sai ya kyaɓe fuska yana girgiza mata kai. “Ba zan sake ba” Hanci ta ja tana kallonsa. Yayin da shi kuma a hankali yake motsa babban yatsansa a gefen fuskarta. “I hate you Abu Aswad!” Peck ya mata a goshi. “Mishallyn Aliyu you are the sun, moon, and stars, i love you more than my morning coffee, my heart is pitter-pattering for you” Naushi ta kai masa a ƙirji. “I hate da gaske” “Ni kuka na ce i love you da gasken-gaske... Jikinki akwai zafi sosai, yanzu ki kwanta, gobe sai mu je mu ga likita” Kai ta gyaɗa masa tana lumshe idonta. *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.* ZAID POV. “Zuwa gobe za a tura takardar ƙara kotu, daga nan za a fara zaman shari'a” Cewar wata garjejeyar murya da ke futowa daga cikin wata ipad dake aje gaban Zaid da Rhoda. A tare Rhoda da Zaid suka dubi juna. Kafin wannan muryar ta kuma faɗin. “A yau aka kamo wasu daga cikin waɗanda Alhaji Bala yake hulɗa da su, dan haka kuna cikin haɗari, fatan za ku kula!” “Ok sir” Suka amsa masa a tare, kuma daga haka wayar ta katse. “Yanzu yaushe za ki karɓi musulunci?” Zaid ya tambaya yana duban Rhoda, a sanda yake rufe ipad ɗin. Rhoda ta yi murmushi. “Zuwa ranar da kotu ta yanke hukunci, kuma daga nan zan je na duba dangin Mom. Sai kuma...” Dariya Zaid ya bushe da ita ganin yau ɗaya Rhoda na kunyar furta masa wani abu. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa cikin faɗin: “Iko sai Allah, abun mamaki Rhoda yau ke kike jin kunyata?” Duka ta kai masa tana turo baki. Shi kuma ya yi dariya, dan ya san maganar aurenta take san yi. “Allah Rhoda ke da Ammata kun raina ni, daga na yi abu sai ku kawo min duka... amma ba damuwa, na dena muki wasa” Ya ƙarashe yana haɗe rai kamar gaske. Rhoda ta yi murmushi tana faɗin. “Ba ka ji ne ai” “Ji tsaurin ido, ni fa yayanki ne ba ƙaninki ba?” “Yi haƙuri to” ya yi murmushi uana ci gaba da kallon ƙanwar tasa. “Rhoda ki na san Zakar?” Ya mata tambaya irin wadda ya saba mata a duk sanda magana irin wannan ta haɗosu. Kanta ta gyaɗa masa tana murmushi. “Allah ya tabbatar mana da alkairi Cuzzie” * “Me gida Raja wai ina muka shilla ne?” Cewar Zuzu, wanda ke zaune a back seat na motar Zaid, daga gefensa kuma Jagwado da Alandi ne. A front seat kuma Zaid ne da Rhoda. Zaid ya ɗaga kafaɗarsa. “Ba na faɗa muku cewar aikin mu ya ƙare ba?... To wani wuri nake san kaiku” Daga haka babu wanda ya sake cewa komai cikinsu, har suka ida Rehab, wato gidan da ake kawai mutanen da suke shaye-shaye, ko waɗanda shaye-shayen ya fara taɓawa ƙwaƙwalwa. Su Zuzu ba su fuskanci hakan ba sai da suka ga an shiga da su ciki. *No.86, Garki 2, Abuja...* RABI'A POV. “Ammatan Raja!” Zaid ya kira sunan Rabi, wadda ke kwance a kansa tana daddana wayarta. Yayin da shi kuma yake kwance a kan kujera. Rabi ta ɗauke idonta daga kan wayar da take daddanawa ta kalli fuskarsa. “Au... Ina nufin 'Yan matan Yaya!” Nan da nan Rabi'a ta sha mur, dan ya tuna mata da abun da take san mantawa da shi. Harara ta wurga masa tana juyar da kallonta kan wayarta. Zaid ya yi 'yar dariya. “Wasa nake. Yanzu faɗamin, menene burinki a da, bayan kun yi aure da Yaya?” Sai ta ƙara kallonsa cikin rashin fahimta, kuma tun kafin ta furta cewa bata gane me yake nufi ba yace. “I mean, menene burinki, ko wani fatanki, ko mafarkin da kike, na irin rayuwar da za ki gudanar da shi bayan kun yi aure?” Ba ta yi mamakin sanin Yayan da ya yi ba, dan a yanda

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112