Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

da sakan ɗaya idanuwanta sun kasa barinsa ya huta, tunani barkatai yake a kanta. Ya kasa gane kan marsalar da ta samesa, yasan cewa shi bai taɓa samun kansa a cikin irin wannan halin ba. Bai taɓa so ba, bai san ya yake ba, bai taɓa kusantar inda yake ba, bai taɓa budurwa ba ma, balle yace ya taɓa sanin kalar yanda so yake. Amma a kallon farko da ya mata wani abu a kanta ya samu gu ya yi zaman darshan a zuciyarsa. Kuma sam ba ya jin zai bar hakan ta faru, zai yi duk yanda da zai yi wurin ganin hakan ba ta faru ba. Haba!, Shi ne fa?, ALIYU ZAID BICHI?, Shi ne KULIYA manta sabo, wanda ba ya ɗaukar raini duk ƙanƙantarsa. Abun da tai masa rannan ya dawo tunaninsu, yanda wutar masifa ke ci a idonta, a lokaci guda kuma sai ya ga mamaki ya maye wannan masifar, bai san mamakin me take ba, wata ƙila ganin girmansa ne ya sa ta shiga mamakin, ko kuma wani tunani ne ya haska a cikin kanta, amma dai koma menene shi ba zai bar abun da ke kai kawo a cikin kansa ya auku ba, don ya sani, hakan shi ne zai zame masa babban kuskure a rayuwarsa. Soyyaya tsakaninsa da ƙanwar abokinsa, no way!. Abinda bai sani ba shi ne, ɗan adam ba shi da dama, ko iko na sauya ƙaddararsa zuwa yanda yake so, Allah shi ne wanda yake jujjuya ko wani irin lamari. Sannan kuma wannan ƙaddarar dake shirin faruwa kwanaki kaɗan, ita ce za ta ƙaryata wannan zancen nasa, ta murmushe zancen nasa har garinsa. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriter ••••••••••• *LABARINSU* *© SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *08* ~~~ *You deserve a love that goes to war alongside you, not against you* -Heart spekeaks- *** KULIYA POV. _🎶What should i do?_ _What should I do when we come face to face?_ _Should I cut my fingers while admiringly glancing at your beauty,_ _Like Qibdiyyat when the greatly admired Joseph?_ _Or Should I abnegate your humanhood by saying that you're a noble angel and exalt your creator?_ _How should I be in that day?......🎶_ A hankali waƙar what sould i do? ke tashi daga mpn motar Sharon, wadda Nura Ismail Abou Othaymeen ya rera. Tayoyin matar na garawa a kan titi, yayin da Sharon ke zaune a mazaunin driver, shi kuma Kuliyan na zaune a gefenta yana kallon hanya. “Ina muka yi sir?” Ya juyo ya kalleta, sannan a hankali ya ɗaga kafaɗarasa ta dama. Yana mayar da dubansa gefen hanya. “Gidan Anna” Ya amsa mata a taƙaice, kuma daga hakan bai sake cewa komai ba, har suka iso gidan. Ita ta zaune a mota shi kuma ya fita ya shiga cikin gidan. Babu kowa a falo, dan haka kansa tsaye ya nufi ɗakinta. Tsaye take a jikin loka, ba zai iya cewa ga abinda take ba, amma ya ga sanda wani abu mai kama da farin ciki ya wulƙa ta cikin idonta, a sanda ta yi arba da shi. Kansa ya sunkuyar ƙasa, kafin ya ci gaba da takawa zuwa gabanta. Yana ƙarasawa ya rungumeta. Anna ta rintse idonta, tana jin ƙwalla na shirin zubo mata, ba ƙaramar azabtuwa ta yi ba da hana kanta zuwa duba shi, sai dai ta yi hakan ne kawai don ta ganar da shi kuskurensa. Ba wai dan ba ta san ganinsa ba. Dan Allah ya ɗora mata san Kuliya tun ranar da ta fara ɗora idonta a kansa. Ranar ita ce ke da dutyn yamma. Ta na shara a gidan marayun da ta samu aiki, wanda ke garin kano, a lokacin tana cikin matsananciyar buƙatar kuɗi. Hakan yasa a sanda aka mata tayin aikin ta karɓa ba tare da wani tunani ba. A garden ta ga wani yaro zaune kan duwatsu, ya ba ta baya, hakan yasa ba ta kalli fuskarsa ba. Kuma ganinsa a wurin ya ba ta mamaki, don a lokaci irin wannan yaran gidan ba sa zama a ko ina da ya wuce islamiyya, don lokacin ɗaukar darasi ne. Kuma tasan da cewa sauran yaran yanzu haka suna can, amma to wannan me yake a nan. “Kai yaro!, me kake a nan ?” Ta tambayi abun da ke yawo a cikin kanta, a sanda ta ƙarasa kusa da shi, ɗagowa ya yi da kansa ya kalleta. A kallo ɗaya da ya yiwa matar ya ji cewar zai iya yarda da ita. Saboda tun bayan zuwansa gidan marayun bai ƙara yarda da kowa ba, ba ya shiga cikin sauran yaran gidan, ba ya cin abinci tare da su, ba ya walwala, ba ya komai, sai tunanin ɗan uwansa da ya cika zuciyarsa. “Ka na jin yunwa ne ?” Annan ta kuma tambaya a wancan lokacin, sai ya girgiza mata kai. Ita kuma sai ta gyaɗa kanta, don ta fahimce shi, da alama sabon zuwa ne, kasancewar ba ta taɓa ganinsa a gidan ba, kuma rashin sakewa na faruwa da sabbin zuwa gidan. Hakan yasa ta zauna kusa da shi, ta na jingine tsintiyar hannunta a jiki wata bishi. “Kana ji ko!, ban san me yasa ka zo nan gidan ba, amma ina fatan ka ɗau haƙuri, ka dangana da rashin da ka yi, dan nasan duk wanda ya zo nan to ya yi wani rashin ne... Idan ka kwantar da hankalinka, ka saba da kowa a nan ka ji?” Maganarta da shi ke nan a wancan lokacin. A yanzu kuma sai ta ɗago shi daga jikinta tana kallon fuskarsa. “Anna i am so sorry, ba zan sake ba...” Ya zaɓi ya bata haƙuri, dan yasan fushi take da shi, Annan ta kai hannu ta riƙe fuskarsa. “Ka kiyaye Aliyu, kasan da cewa ba mu da kowa sai junanmu...” Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya gyaɗa mata kai. Daga bakin ƙofar ɗakin, Siyama ta saki murmushi, haɗi da ajiyar zuciya, jin cewar masoyinta na cikin ƙoshin lafiya, a cikin kwana huɗun duk sanda za ta tambayi Anna game da shi ba ta bata amsa, sai dai ta yi banza da ita. Ita kanta ta san cewar ta na cikin tashin hankali, dan har watq ƙwarya-ƙwaryar rama ta yi, ramar rashin sanin halin da abun santa ke ciki. Ta kuma yin wani murmushin, ta na karanta wasiƙar jaki, kanta take hangowa a tsakiyar hannayen Kuliya, wani mafarki da ta saba yinsa a farke. Hannunta na dama ta kai ta ɗan daki goshinta, sannan ta bar ƙofar ɗakin, ranta wasai. *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja* MISHAL POV. Zaune take a falon gisansu, ta na rubuta assignment ɗin da aka basu yau, yayin da Daala ke zaune a gefenta, ta na yi ta na ɗan yiwa Daalan hira. Takun da ta ji daga kan stairs yasa ta kalli wurin, ganin Hajjara ce yasa ta sakar mata murmushin mugunta, irin wanda take mata a duk sanda za su haɗa ido a kwanakin nan. Sannan ta ci gaba da rubutunta. Wani malolon baƙin ciki ya tokare maƙoshin Hajjara, tun bayan ranar da suka dawo daga asibitin nan Abubakar ya hau fushi da ita. Sai da ta haɗa shi da kawunsu sannan ya saurareta, ba su shirya ba sai da ya bar mata kakkauran warning a kan Mishal. A ranta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112