Chapter 110
Chapter 110
zo ƙarshe. Bayan shuɗewar tsawon shekaru, sai a yau ne Rhoda ta samu adalci kan abun da aka aikata mata, ba ma ita kaɗai ba, hatta da Rabi a yau ne aka sama mata 'yanci. Daga kotun kai tsaye Zaid ya wuce da Rhoda masallacin da ya yi magana da limaminsa, dan shi yake so ya bawa Rhoda kalimatu shahadah. *No.86, Garki 2, Abuja...* *08:00* Rabi da Zaid ne zaune a falo suna kallo a tv. Rhoda kuma na ɗakin da Rabi ta ware mata, dan yau a gidan zata kwana. “Mts! Ammata na manta da kifinki a mota, bari na je na kawo miki” Cewar Zaid yana miƙewa tare da barin falon. Rabi ta sunkuyar da kanta ta kalli cikinta. Tun bayan dawowarta gidan take ta neman hanyar da za ta faɗawa Zaid wannan kyakkyawan labarin, amma ta rasa ta inda zata fara. Kallo ta ci gaba da binsa da shi, har ya dawo hannunsa riƙe da leda, ya buɗe ledar, ƙamshin kayan haɗin da aka yi amfani da su wurin haɗa kifin ya bugi hancints, hakan ya sa ta ji amai ya zo mata. Ba shiri ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta. Baki sake Zaid ya bi bayanta da kallo, kafin shi ma ya miƙe ya nufi ɗakinta da ya ga ta shiga. Ko da ya isa ɗakin sai ya tarar da har ta faɗa bayi, ta kuma kulle kofar bayin. Maganar duniya mata amma ta ƙi amsa shi hakan ya sa ya juyo, ya na shirin barin ɗakin, idonsa ya sauƙa kan wata takarda aje a kan hijabinta. Don haka sai fasa fitar, ya dawo ya ɗauki takardar ya shiga karantawa. Sai da Rabi ta gama aman nata, ta wanke bakinta, sannan ta fito. Damm, gabanta ya buga, ganin Zaid tsaye a tsakiyar ɗakin, hannunsa riƙe da takardar da ta manta bata ɓoye ba, kuma ba ma wannan ne ya ɗaga mata hankali ba, wani irin kallo da ta ga yana mata shi ya haɗe kayan cikinta waje guda. Da ƙyar ta haɗiye yawu ta fara takawa tana nufarsa. “Adawiyya miye wannan?” Ya tambaya yana nuna mata takardar, sai da cikin Rabi ya yamutsa, jin yanda amon muryarsa ya fito a ƙasashe. “Ba magana nake miki ba?!” Ya faɗa cikin tsawa, yana ƙoƙarin saka ƙaton dutse, dan danne ɓacin ran dake taso masa. Abun ya bala'in ɓata masa rai, a matsayinsa na uban ɗan cikinta, kamata ya yi ace ta sanar da shi, amma me ya sa za ta ɓoye masa?. Sosai Rabi ta tsora, ganin yanda ya buɗe lumsassun idanuwansa a kanta. Hakan wani abu ne da bata taɓa gani ba a tare da shi, nan take ta fara in'ina. “Ko ba ni ne uban cikin jikinki ba ya kamata ace na sani, ballantana na san da cewa ni ne ubansa, me ya sa za ki ɓoye min?!” A wannan karon kam ita ma Rabi ranta sai ya fara ɓaci. Dan haka tace. “Miye laifi na a nan?, ni kai na ban san cewa ina ɗauke da ciki ba, sai bayan da Anna ta ankarar da ni, hakan ya sa na je na yi gwaji a yau ɗin nan, kuma shi ma gwajin ya tabbatar da ina ɗauke da juna biyu. Tun bayan dawowarka nake ta neman hanyar da zan bi na faɗa maka, amma na rasa, shi ne na yi laifi?...” “A'a kam, ba ki yi laifi ba!. Tun ɗazu na dawo gidan, me yasa da na dawo ba ji faɗa min ba?!” “Ya isheni haka Zaid!” Ta faɗi ita ma a tsawace tana kallon cikin idonsa. “Wai akaina aka fara ciki?. Na ce maka ƙoƙarin gano hanyar da ta dace na faɗa maka nake, amma sai ka hau ni da faɗa?, na ga dai ba wata tara cikin ya yi ba tare da na sanar maka ba!” “Ya yi kyau Adawiyya, yau kanki tsaye kike kiran sunan, a kan wannan cikin kike gaya mun duk maganar da ta zo bakinki ko?, ki riƙe abunki na bar miki!” Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya aje mata takardar ba. Rabi ta zame ƙasa tana fashewa da kuka. Me ya sa ma za ta bari har sheɗan ya shiga tsakaninsu?, kuma ai shi ma ya na da laifi, mi ye na saurin fusatar haka?, tun bayan aurensu ba su taɓa faɗa ba sai yau, hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, har ta kwanta bata dena kuka. Bacci ma a ranar sai ya gagareta. Ta rasa inda za ta sa kanta, musamman idan ta tuna da yanda ta ɗaga masa murya, abun sai ya soketa a zuciya. Ganin zama cikin kukan ba zai finsheta ba ya sa ta miƙe salin'alin ta nufi ɗakinsa, ƙofar ta tura a hankali tana saka kai ciki. A kunne ta samu wutar ɗakin, shi kuma ya na zaune daga kan gado, ya zuro da ƙafafaunsa ƙasan gadon. Kuma duk da ya bawa ƙofar baya, tana iya ganin yanda ya yi tagumi. Wani kuka me ƙarfi ya ƙwace mata, dan gani take kamar ita ce silar rashin kwanciya baccin nasa. Da gudu ta hau kan gadon nasa, ta shiga rarrafe a kan gadon, har ta isa inda yake, tana isa dab da shi, ta zura hannayenta ta bayansa, suka kewayo ta gaba, kanta ta kwantar a bayansa tana fashewa da kuka. Zaid ya rintse idonsa, zuciyarsa na masa zugi, yanzu haka zaman da ya yi na nadama ne, sai bayan da ya zo kwanciya ya ga rashin kyautawarsa kan abun da ya mata, be kamata ace ya ɗaga mata murya haka ba, kuma be kanata a ce ya fusata daga ganin takarda ba. Zaman da ya yi anan yana ta tsara yanda za ayi ya bata haƙuri ne gobe da safe, sai ga shi kuma ita ta zo da kanta dan ta ba shi haƙurin. “Ka yi haƙuri Raj, na tuba!” Da ƙarfi ya sauƙe ajiyar zuciyar, sannan ya saka hannayensa a kan nata yana rabasu daga ruƙon da ta masa, sannan a hankali ya sauƙo da ido daga kan gadon, ta dawo gabansa ta tsaya. Ya ɗan ɗaga kansa ya kalleta, fuskar nan sharkaf da hawaye. Sai ya raba cinyarsa biyu, ya zaunar da ita akan ta dama. Tana zama a kan cinyar tasa ta ƙara shigewa cikin jikinsa, tana nanata masa kalaman ban haƙuri. Shi ma rungumeta ya yi, ninkun ƙauna da santa na ƙara shiga cikin zuciyarsa. “Ya isa haka Adawiyya, ko tsakanin harshe da haƙuri ana samun saɓani. Wannan karon sheɗan ya yi nasara a kanmu, dan haka sai mu kiyaye nan gaba” Kanta ta gyaɗa masa tana shanye kukan nata. “I'm sorry too, na faɗa miki maganganu masu zafi” Kanta ta girgiza tana ɗagowa daga jikinsa. Hannunsa ya kai kan cikinta, yana jin santa da kuma na abun da ke cikinta na ƙara kama shi. “Ina sonki Ammatana. Wannan babbar kyautar taki ta fi min komai a yanzu” Ƙara kwanciya ta yi a jikinsa tana lumshe ido. “Allah alhamdulillah” Ya faɗi yana ƙara matseta a jikinsa. “Ina sanki 'yan matan Zaid” “Ina sanka Kayali! (Arabic:My choice)” Sai ya ɗan kalleta kaɗan. “Da ma ke kika zaɓeni?. Ca nake ai ƙaddara ta zaɓa miki ni” Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112