Chapter 58
Chapter 58
kuwa ba za ta iya auren Raja ba, ko ta na son Yaya ko babta sonsa dole ne ta zauna da shi, don babu yanda za ayi ta kalli tsabar idonsa ta faɗa masa ba ta sonsa. “Ina sansa Anti Saratu. I LOVE ZAID!, i... i... Love him, i feel like The word 'love' is not enough for me to explain the way i love him!” Ta fito ta faɗi duk abun da ta san ta na ji a ciki zuciyarta, ba so kawai takewa Raja ba, har da ƙauna ma tana masa, don soyyayar tasu ta jini ce, su jinin mutum ɗaya ne, shi da mijin Mishal 'ya'yan yayar Umma wadda take yawan basu labarinta ne, su ne 'ya'yan me sunanta, su ne 'ya'yan da kakansu ya basu labari kan an sha nemansu amma ba'a same su ba. Cike da tausayawa Anti Saratu ta ɗagota daga jikinta. “Haƙiƙa Rabi kin gamu da jarabawa, amma babu yan da za mu yi, addu'a ita ce mafita, don haka sai ki dage da addu'a!” *No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja* “To yanzu Anti miye abun yi?” Cewar Siyama cikin kuka, tun da ta dawo gidan Anti Kariman ma ba ta samu sukuni ba, don ji ta yi hankalinta ma ya fi tashi a nan ɗin. Anti Karima ta kalleta na wasu 'yan sakkani, gaba ɗaya ta sauya, kamar ba Siyamanta ba, ta rame ta ƙara baƙi, kamar kazar mayu. “Ba de kin ce yarinya ba ce?” Siyama ta gyaɗamata kai tana share hawaye. Anti Karima ta gyaɗa kai. “To ai cikin sauƙi za mu yi maganinta, ba tare da kin ɗaga hankalinki ko kin tayar da nawa ba... Zo ki ji” Siyama ta miƙa mata kunnenta, ido waje take kallon Anti Karima, bayan da ta faɗa mata abinda za su yi. “Kuka ki na ganin babu matsala?” Ta faɗa cikin karyewar murya. “Mtswwww!, Wata matsalar kuma za'a samu, hakan kawai za mu yi” Siyama ta gyaɗa kanta cike da gamsuwa, duk da ta na jin ɗar-ɗar a cikin ranta, amma sai ta dake ta miƙe ta shige ɗakinta. Anti Karima ta bi bayanta da kallo cike da tausayawa, idan de har Kuliya ya shigo hannunsa ba za ta masa da sauƙi ba, dan sai ta rama abun da ya yiwa ƙanwarta. Ta yi ƙwafa a bayyane tana jan wani littafi dake aje kan coffee table. *No.181, Guzape, Abuja...* MISHAL POV. Zaune take a falo ta na rubutu a cikin littattafanta, ta baje takardu da littatafi a ko ina, don wani assignment ɗin math aka basu me wahalar tsiya, duk da ita ba sosai take yin assignment ɗin math ba, wannan ɗin ma don malamin yace shi ne makin C.A ɗinsu. Shi ya sa ta dage take yi. Ƙofar falon aka turo, Kuliya ya shigo ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar corridor, ita ma ba ta takura da sai ta masa magana ba, don ta lura da ba ƙaramin miskili ba ne, ta taɓe baki ta ci gaba da aikinta. Bayan shuɗewar kusan muntina ashirin sai ga shi ya fito, sanye cikin wata baƙar T-shirt da baƙin sweat trouser. Fuskarsa kawai ta kalla ta ganta a haɗe, babu alamun rahama ko fara'a, da alama dai yau ransa a ɓace yake sosai. A falon ya zauna ba tare da ya mata magana ba, sai wani cin magani yake, ɗagowa da kanta ta yi ta kalleshi, sannan ta ci gaba da rubutunta tana faɗin. “Sannu da zuwa” Ƙin kulata ya yi, don ransa a matuƙar ɓace yake, for the very first time a rayuwarsa ya yi falling assignment, wani abu da kaf tsawon fara aikinsa a wurin bai taɓa faruwa da shi ba, a ko da yauashe shi me nasara ne, kuma ba faɗuwar tasa ce kaɗai ta ɓata masa rai ba, sakin me laifin da aka yi ne ya fi ɓata masa rai. Kuma babban abun haushin shi ne, me laifin fyaɗe ya aikata, duk da tarin hujjojjin da suka gabatar a gaban kotu, haka aka kori ƙarar ba tare da la'akari da rayuwar ƙaramar yarinyar da aka lallata ba. Mishal ba ta ƙara bi ta kansa ba sai da ta kakare a wani wuri, kuma ba ta da wanda za ta iya tambaya bayan shi, shi ɗin da a yanzu ba ta da kowa kamarsa, shi ɗin da take zaune da shi gida ɗaya a matsayin miji. Hakan yasa ta ɗauki littafin ta matsa kusa da shi tana faɗin. “Abu Aswad ɗan temaka min...” Wani kallo ya mata daga ita har littafin nata, kafin ya juyar da kansa gefe, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. Mishal ba ta daddara ba ta ƙara miƙa masa littafin. “Dan Allah ka ɗan temaka min iyaka nan ne na kasa...” “Ke wai ba ki da hankali ne?! Ba ki ga a yanayin da na dawo gida ba?!, Ke ba za ki iya yi da kan ki ba?! Dole sai na miki?!” Cike da hargagi yake mata magannar, yayin da ya miƙe tsaye, har wani ɗaga hannu yake kamar me shirin kai mata duka, cike da dauriya Mishal ta miƙe tsaye, don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ido cikin ido ta kalleshi, hannunta riƙe da littafin da kuma pen. “Kai ba ka isa ka ce ba ni da hankali ba, don kawai ina yarinya ba shi zai sa a min kallon mahaukaciya ba, ina da hankali, na kuma san inda ke min ciwo. Don ka dawo gida ranka a ɓace sai ka huce a kaina?, Na ji ina da laifi don na maka magana yayin da kake cikin fishi, amma na roƙeka da kada ka sake min tsawa, saboda ba'a min tsawa!” Tana kawai nan ta tattara kayanta ta yi ɗakinta cikin ƙunar rai. Kuliya ya dafe kansa ya na rintse ido, me ya shiga kansa haka har ya mata tsawa?, ya rab!, ya kamata a ce ya na iya sarrafa fishinsa. * Mishal na zaune a kan wata doguwar kujerar balcony ɗin ɗakinta, littafin math ɗinta ne a je a gefenta, don ta kasa wucewa wurin, ga kuma ranta da ya ɓaci, babban ɗan yatsanta na dama sanye cikin bakinta tana sha, tana kalon hasken farin wata, wai ko zuciyarta za ta washe da wannan baƙin cikin da Abu Aswad ya ɗura mata. Ƙofar ɗakin ta ji an turo, hakan ya sa ta juya ta kalli cikin ɗakin, Kuliya ta ga ya shigo, ya na wani abu kamar mara gaskiya, hakan ya sa ta yi ƙwafa tana juyawa, ta ci gaba da shan hannunta. Ƙaraaowa ya yi ya, ya tsaya a bayanta, sannan ya mata gyaran murya, Mishal ta yi kamar ba ta ji shi ba, hakan ya sa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, littafin math ɗinta dake tsakaninsu ya kalla, sannan ya kalli fuskarta ta cikin hasken farin wata da kuma na wutar nepa. “Wai har yanzu ba ki dena shan hannu ba?” Yanzun ma banza ta masa, a karo na farko Kuliya ya ji haushin kansa, ya ji haushin zuciya da ta ingiza shi har ya aikatawa amanarsa haka, a karon farko ya ji cewar ya yi nadama, ya yi nadamar yi wa wani masifa. Hakan yasa ya ɗaga hannayensa, tare da kama kunnensa. “I am sorry Mishal!” Wasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112