Skip to content

Chapter 83

Chapter 83

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

na cutarwa da ɓacin rai. “Me nene wannan a haƙorinki?” Sai ta tsaya da maganar da take masa ta kalli fuskarsa, gira ya ɗaga mata cikin sigar tambaya. Sai ta maida idonta kan wayar ta na faɗin. “Datti ne... Dama haka haƙorina yake, duk wata Aki yake kaini a wanke min, da braces aka saka min ma, kwanaki aka zire min su” “Ok gobe zan je na ɗauko ki a school... Daga nan sai mu wuce asbitin a wanke miki” Ta kuma kallonsa. “Angelica ta ce min ma wai an kawo wasu sabin teddies a Jabi Lake Mall, za ka kai ni?” Kuliya ya yi murmushi ya na ƙara matse hannunsa a ƙugunta. Shi ne ya kamata a kira da mijin yarinya. “Har Magic land ma za mu je” Bakin Mishal ya tale cikin dariya. Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta na ci gaba da danna wayarsa. “Abu Aswad?” Muryarta ta kira sunansa bayan wani lokaci, ipad ɗin ya kawar daga fuskarsa ya kalli ƙasan kanta, don har zuwa lokacin ta na kwance a jikinsa. “Hmm” “I hate you” Sai ya yi murmushi ya na ci gaba da kallon ipad ɗin. “And i love you” *Unguwar Madallah, Suleja, Niger State* RAJA POV. “Ku kamata!” Wannan shi ne umarni da ya bawa jami'an da ya zo da su, a yayin da ya shigo cikin gidan su Rabi ba tare da ko neman izini ba, ya jure abubuwa da dama, amma ba zai iya jure rashin Rabi'a ba, zai fiye masa sauƙi ma a ce ya rabu da rayuwarsa, da ace ya rasata, Habiba ta azabtar da ita bakin gwargwado, dan haka lokaci ne da ita ma za ta ɗanɗani kuɗarta, ba ma ita kaɗai ba, har da Ɗan Lami ya sa an kamo shi, dan sai sun faɗa masa inda Rabi'a ta shiga. Habiba ta fashe da kuka a sanda 'yan matan jami'an suka yi kanta, ciki kuwa har da Rhoda, Fatima da Mahmud har da Saratu suna tsaye suna kuka, haka aka kama Habiban aka fita da ita ta na ta roƙonsu. Da ƙyar Raja ya iya dai-daita kansa, sannan ya lalubo ainahin muryarsa ya na kallon Saratu yace. “Ka da ku damu, tambayoyi za a mata kawai, insha-Allah idan ta amsasu da wuri ina me tabbatar muku da za ta iya dawowa a yau ɗin nan, idan kuma ta yi taurin kai, ba zan iya muku alƙawarin dawowarta gareku da wuri ba!...” Ko kafin ya kai ƙarshen maganarsa, Fatima ta ƙarawa kukanta volume ta shige ɗaki, Mahmud ma bayanta ya bi ya na nasa kukan, duk da shi ba wani wayi gareshi ba, shi dai ya ga an tafi da Uammansu. Saratu ta share hawayenta tana faɗin. “Babu komai Zaid, Allah ya bayyanar da gaskiya!” “Na gode” Ya faɗi ya na gyaɗa mata kai, tare da juyawa. “Ammm, baka ji ba” Tsayawa ya yi tare da juyowa ya na kallonta. “Maganace akan Rabi, ina zaton duk inda take a yanzu ba za ta wuce Haɗejia ba!” *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.* RAJA POV. “Wai ina za ka je?” Rhoda ta tambaya, a sanda ta shigo ɗakinsa ta tarar da shi ya na haɗa kaya a cikin jakarsa. Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya furta. “Haɗejia!” Trayn hannunta ta aje ta na faɗin. “Haɗejia?... Me za ka yi a haɗejia?” Ya zuge duffle bag ɗin da ya saka kayansa kala biyar a ciki, sannan ya juyo ya kalleta. “Yayar Ammata ta ce min ta na can... Dan haka dole na je nemanta, wata ƙila ma na haɗu da dangin Momma” Ya faɗi cikin karyayyar murya, Rhoda ta iso gabansa ta dafa kafaɗarsa. “Kada ka damu Zaid.... Za mu samota, and ina so mu je tare” Kansa ya girgiza mata. “No Rhoda, ban sani ba ma ko za ta amince da ni, sanin kanki ne fishi take da ni, ba na san abubuwa su ƙara cakuɗewa” Rhoda ta girgiza masa kai. “Tun bayan da muka san juna komai tare muke, dan haka wannan ma tare za mu yi, ko wani ƙalu bale tare muka fuskance shi, shi ya sa ba zan barka kai kaɗai ba” Kallonta kawai ya ci gaba da yi, kafin ya ɗaga kafaɗarsa ya na sunkuyar da kansa ƙasa. “But dole ki sauya yanayin shigarki...” Jikinta ta kalla ta na dariya. “Wannan ba damuwa ba ne Dude, hatta da sunana sai na manta da shi indai a kanka ne, ballantana ma da na kusa dena saka irin waɗanan kayan, na kusa musulunta fa!” Maganar tata ta tuna masa da zagayen halin da suke ciki gaba ɗaya, ta tuna masa da bincinken da suke kan waɗanda suka yi wa Rabi'a fyaɗe, ta sa ya tuna case ɗinsu da Alhaji Bala. “So yanzu ka san address ɗin gidan da za mu je?” Kansa ya gyaɗa ya na ɗaukewa jakar. “Saratu have told me everything a kan gidan... But a mota za mu tafi, babu jirgin da zai je kano a gobe da safe, shi ya sa zamu tafi da motar” *Magic Land, Abuja.* YUSHAL POV. Ticket suka fara siya, kafin suka shiga ciki, ko wani kalar game Mishal ta ga ni sai ta ce sai sun buga, kuma idan sun buga ɗin ita take cinyewa, don shi bai iya ba, ita kuwa babu wanda bata sani ba. Lilo ma babu kalar wanda bata hau ba, Kuliya kam guda ɗaya ya gwada hawa, bai sauƙo ba sai da hajijiya, hakan ta sa yace ba zai sake hawa ba. Sai da ta buga wasanni sosai, kafin suka siyi ice-cream suka samu wasu kujeru can daga baya, suka zauna suna sha. “Ki bi ice-cream ɗin nan a hankali fa Teddy Bear, saboda mura” Kuliya ya faɗi ya na kallonta, ganin yanda take shan ice-cream ɗin kamar wani abinci. “Babu fa abun da zai yi” Ta faɗi da ice-cream ɗi a bakinta, Kuliya ya girgiza kansa ya na ɗaga wayarsa, saboda kiran da Sharon dake shigowa wayar. Ya ɗan jima ya na wayar, kafin wayar tasa ta ƙare, juyowa ya yi ya kalli Mishal. Wadda ta gama shan ice-cream ɗin tana ta kalle-kalle a wurin. “Kin gama?” Ya tambaya ya na miƙewa tsaye, tare da ɗaga kafaɗarsa ta dama. Ita ma sai ta miƙe tana turo baki. “ummm” Hannunsa ya kai ya gyara mata zaman gyalen kanta, sannan ya saka hannunsa a aljihu ya zaro wani hanki, ya na faɗin. “Ji bi yanda kika ɓata bakinki” Ya faɗi ya na goge mata bakin. Kafin ya jata suka bar wurin, asbitin da aka saba mata wankin haƙori suka je, aka mata wankin haƙorin, kafin suka wuce Jabi mall. Siyyaya suka yi sosai, kuma duk kayan wasa sun fi yawa a ciki, don da ma tace ta bar nata a gida. Kuma daga nan Gidan Anna suka wuce, nan ma sun jima,dan sai dare suka bar gidan. *Anyone can tell you that they love you, but it takes an authentic soul to show you that they so* *** RAJA POV. Da misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa cikin garin haɗejia, bayan doguwar tafiyar da suka kwashe a mota, kasancewar unguwar Jama'aren da aka musu kwatance, ta na a farkon gari ne, kuma su ta kano road suka shigo

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112