Chapter 89
Chapter 89
ita ma take kallon tasa fuskar. Hannunsa na dama ya ɗago ya na kama fuskarta, kafin a hankali ya matso da fuskarsa, ya karkatar da ita gefe kaɗan, leɓɓansa masu ɗumi suka sauƙa a kan nata, ba shiri Rabi ta zaro idanuwanta waje gaba ɗaya, ta saka hannunta ta cukukuye gaban rigarsa, ta ƙanƙame yatsun ƙafarta da suka ɗaga sama saboda kwanciyar da suka yi, ta buɗe bakinta ta na shirin yin magana Zaid ya saka harshensa a cikin bakinta, shi kenan kuma!. Ɗan ragowar hankalin nata da ya rage Raja ya ɓarar mata da shi, ya ɗauketa daga wannan duniyar da muke ciki ya kaita wata can da nisa. Ba ta gane komai, ba kuma ta jin komai sai fitar nunmfashinsa a kan fuskarta, babu abun da take gani sai idanuwansa kusa sosai da nata. Kanta ya cilla zuwa wata nahiyar, ba ta fahimtar komai sai Raja da abin da yake mata a yanzu. “Rabi'a!” Jidda ta kuma kiranta a karo na barkatai, bayan da suka baro wurin Zaid, amma Rabi fur taƙi amsa mata, don haushinta take ji, duk abun da ya sameta a yanzu ita ta jawo mata, ita ta kawota wurin har Zaid ya yi amfani da damar hakan ya sumbaceta cikin wannan daren. Ƙwafa ta yi a ranta tana goge bakinta da hannunta, ita ji take ma kamar har yanzu leɓen nasa na kan nata ne, ji take kamar har yanzu harshensa na cikin bakinta, sarƙafe da nata harshen, shi take kamar har yanzu hannunsa na kan ƙugunta ne, ji take kamar har yanzu tana kwance a kan jikinsa ne. Ƙafa ta sa ta yi fatali da wannan tunanin da ya addabeta, a sanda suka iso ɗakinsu. Bargo ta ɗaga sannan ta kwanta kusa da Rhoda wadda ke kwance a kan gadonta ta na sharɓar bacci. A kai a kai take jan tsaki har da ƙwafa, Jidda na jinta amma ta yi luƙus tana mata dariyar mugunta. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *23* ~~~ *The one thing that holds more power than ‘I love you’, is ‘I got you’...* *** *No.86, Garki 2, Abuja...* *09:00 PM.* RABI POV. A hankali ta zura ƙafarta ta dama cikin kitchen ɗin gidan, sai kuma ta tsaya ta na kallon irin yawan kayan dake cikin falon, sai da ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, kafin ta sako ƙafarta ta hagu ciki. Kamar sauran sassan gidan, shi ma kitchen ɗin ya haɗu. A jiya danginta, wato 'yan uwan mahaifiyarta suka rakota har ɗakin mijinta, kuma a nan suka kwana, ba su tafi ba sai ɗazu da yamma, sun tafi sun barta cikin wannan gidan, bayan da suka mata nasihu kala-kala, sai de kuma ita ba ta jin ko nasiha ɗaya cikin nasihunsu zai yi aiki, don kuwa ba ta jin za su yi wani dogon zama ita da Zaid. Kowa a familynsu burinsa kawai ayi auren, to gashi an yi, ita kuma za ta san yanda za ta yi dan ya saketa, da ta ci gaba da zama da makashi, gwara ta koma can Haɗejian ta ci gaba da zama, . Duk da tasan cewa zuciyarta ba za ta so hakan ba, amma za ta haƙurƙurtar da ita, ta faɗa mata cewar zamanta da Zaid ba zai haifar da ɗa me ido ba. Motsi ta ji a bayanta a lokacin da ta kai tsakiyar kitchen ɗin, da sauri ta juya ta na kallon bakin ƙofar kitchen ɗin, ganin Zaid tsaye a wurin kuma jingine da jikin ƙofa ya sa ta shiga dube-dube a kitchen ɗin, can ta hango set din wuƙa, ba tare da sake wata shawara da zuciyarta ba, ta rarumo wuƙa ɗaya daga cikin set ɗin, ta nuna shi da ita ido waje. “Kada ka shigo nan!” Raja na kallonta ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, hannyensa harɗe a ƙirjinsa, sai murmushi yake zabgawa, don shi a yanzu babu wani abu dake damun ransa, komai nasa ya hau seti, rayuwar ma sai ya ga kamar tana sauri ne. Wai yau Ammatansa ce a cikin gidansa, matsayin matarsa ta aure, halalinsa!. Duk barazanar da za ta masa ba za ta dame shi ba, don shi bai fara santa don ya bari ba, bai aureta don ya saketa ba, ya aureta ne don ya zauna da ita har zuwa ɗan lokacin da Allah ya ɗiba masa cikin duniya. Hannayensa ya ware, tare da zuba su cikin aljihun wandonsa, ya soma takawa zuwa gabanta. Ganin hakan ya ƙarawa Rabi ƙaimi wurin ci gaba da cuna masa wuƙar a setinsa, sai de kuma ko gezau ba ta ga ya na yi ba, nufota yake gadan-gadan, har ya iso gabanta ba ta bar nuna shi da wuƙar ba, sai zare masa ido take kamar za su faɗo, kuma bai dena tahowa gareta ba har saida ya riski wuƙar, har tana taɓa jikinsa. Da sauri Rabi ta janye wuƙar zuwa gefe, ba shiri ta cillar da ita can gefe ta na ƙara matsawa baya, shi ma kuma be fasa ba, binta yake ta na ja da baya, har sai da Rabi ta kai jikin wata cabinet. “Ai ni na san ba za ki iya cutar da ni ba” Ya faɗa yana kafeta da idanuwansa. Rabi'a ta haɗiye wani abu ta na kawar da kanta gefe, kuma ita kanta ta san gaskiya ya faɗa, ba za ta iya cutar da shi ba sam, ko me zai mata ita ba za ta iya masa koman ba. Amma saboda ƙarfin hali irin nata sai cewa ta yi: “Me zai hana ba zan cutar da kai ba. Idan ta kama har kasheka ma sai na yi...” Tana iya jin sautin murmushinsa. Raja ya fitar da duka hannayensa daga cikin aljihu, sannan ya mata rumfa a tsakiyarsu, ya ƙara matsar da fuskarsa kusa da tata dake kallon gefe. “Ba za ki iya ko da cire silin gashi ɗaya daga jikina ba. Saboda... Kina... Sona, ki yarda kawai. Ko ki yarda ko karki yarda Ammatan Raja... You love Raja... Oh i mean Zaid... Yaya Zaid!” Ba shiri Rabi'a ta ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, ta rintse idonta gam-gam, ta shiga kokawa da numfashinta dake shirin fita gaba ɗaya, hannunta dake kan rigar jikinta ta damƙeshi tare da rigar. “You see... Magana ma kawai na miki ta sa kika shiga cikin wannan halin. Ina ga idan na...” Ba tare da ya ƙarashe ba ya sauƙe hannunsa na dama, sannan ha sako shi ta bayanta, yana turota zuwa jikinsa, hakan ya sa Rabi ƙara ƙanƙame idonta, dan haɗuwar jikunansu sai ya sa ta ji kamar wani irin electric shock ne ya faru tsakaninsu. Kuma hakan be isheshi ya gama wargaza tunaninta ba, sai da ya sauƙe ɗayan hannun nasa ya kama gefen fuskarta da shi. Ya na ƙara kusanta fuskarsa da tata. Allah ne ya ara mata ƙarfin da ta yi amfani da shi wurin turashi zuwa baya. “Dan Allah ka rabu da ni. Ni ba na buƙatarka a rayuwata, tun ba yau ba na faɗa maka haɗuwata da kai kuskure ne, ka ƙyaleni Zaid, dan Allah ka ƙyaleni!” Ta ƙarashe hawaye na sauƙo mata. “Ni kuma ina buƙatarki a rayuwata, ina sonki. Ina.... Matuƙar sonki, dan Allah ki fahimta” Rabi'a ta share hawayen idonta, sannan a dake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112