Chapter 85
Chapter 85
da mamarta ta riƙeka?” Kawu Munzali ya tambaya ya na kallon Rhoda dake gefe tana nata hawayen, dan ita ma ta tuna nata dangin. Raja ya gyaɗa kansa. “Eh ita ce, sunanta Rhoda” “Iko sai Allah, har yanzu ba ta musulunta ba kenan?” Ɗaya daga cikin iyayen me sunan Mamman ya tambaya. “Eh... Amma za ta musulunta nan ba da jimawa ba” “Zo nan 'yata, kema ai kin zama 'yar gida” RABI'A POV. Kamar kullum suna zaune a falon Hajiya suna hira, yayin da ita take gefe tana daddana sabuwar wayar da kawu Abdullahi ya mata kyautar ta yau ɗin nan da safe, duka 'yan matan na nan, sai hayaniyarsu suke, kuma bayan su ɗin ma har da yayunsu, waɗanda suka girme musu. “Kai jama'a, kun ji labarin abun da yake faruwa a waje kuwa?” Gaba ɗayansu suka zubawa Hafiza ido, wadda ta shigo tana ta wannan batu, ita Hafizan ba sa'ar su Rabi ba ce, don ta ma girmewa Baby, ƙawar su Shafa yayar Nafisa ce, kuma ita ce BBCn gidan, ko wani sabon labari a bakinta za ka tsince shi. “Faɗa mana mu ji ta gidana” Shafa wadda ke kishingiɗe a kan kujera ta faɗi tana miƙewa zaune. “Wai ɗan gidan Gwaggon mu ne ya zo!” Cike da rashin fahimta kowa yake kallonta. “Wata gwaggon namu?” Momi ta tambaya. “Ke Rabi 'yan biyun Mamanku, me sunanki nake nufi” Ba shiri Rabi ta miƙe zaune tana kallonta, ɗan gidan me sunanta?, Zaid ne ya zo?, ko de ɗayan ne ya zo?, amma ta ina suka san nan ɗin?, kuma wata ƙila ma Raja ne ya biyo ta?... Kuma tunanin nata bai yi wani nisa ba, zarginta ya tabbata, a sanda Hafizan tace. “Kuma ma ni a yanda na ji, haka aka ce wai saurayinta ne, tsabar abu irin na yarinyar nan wai ba ta san ɗan uwanta ba ne, kuma fa an ce kamarsu ɗaya da ita” Dammm!, gaban Rabi ya buga, saurayinta kuma?, haka yace kenan?, duk yadda aka yi ma Raja ne?, Wai shi me ya sa ba zai barta ta hutawa rayuwarta ba ne?. “A'a fa yaya Hafiza, yaran da aka bamu labarin sun mutu” Hafiza ta wurgawa Jidda harara. “Ƙarya zan muku?, kuma ai da aka bamu labarin cewa aka yi sun ɓata, ba sun mutu ba...” A dai-dai lokacin Hajiya ta fito daga ɗakinta, duk abun da suka faɗi babu wanda ba ta ji ba. “Me... Me kuka ce... Ɗan Rabi ne ya zo?” Ko kafin Hafizan da ta buɗe baki ta bata amsa, suka ji sallamar Kawu Abdullahi a ƙofar falon. Miƙewa suka yi a tsaye cikin girmamawa. Bin su ya yi da kallo kafin yace. “Duka ku bamu wuri, Hajiya tana da baƙo” Ɗaya bayan ɗaya suka shiga ɓacewa suna silalewa zuwa ɗakin Hajiyan, har zuwa lokacin Hajiya na tsaye tana kallon Kawu Abdullahi. Isowa ya yi gabanta ya na zaunar da ita. “Ina zuwa Hajiya” Ya faɗi yana fita waje. Jim kaɗan sai ga shi ya dawo, bayansa biye da Alhaji Ali da kuma ƙannen Kawu Abdullahin guda biyu, sai kuma wani saurayi guda ɗaya biye da su, wani saurayi me kama da 'ya'yanta 'yan biyu, wani saurayi me kaka da jikarta ɗaya. Har matashin ya shigo ya zauna kusa da ita idonta a kansa. “Kin ga ikon Allah ko Hajiya?” Ta juyo ta kalli Kawu Abdullahi kafin ta ƙara juyowa ta kalli matashin, kuma a lokacin ne Rhoda ta shigo ta zauna daga can nesa da su. Hawaye ya zubo daga idon Hajiya, hannunta na karkarwa ta kai ta kama fuskarsa. “Ji... Jikana!” Ta ƙarashe tana rungume shi, tare da sakin kuka me sauti. Kafin ta sake shi tana ta dudduba jikinsa. A hankali Rabi ta saki labulen ɗakin Hajiya, bayan da ta ɗaga shi ta ga jikan Hajiyan da ya zo, a gaskiya ta yi babban kuskure, ta yi kuskure da ta zama sanadiyyar shigowar makashi ahalinsu, amma kuma ba za ta ce ba ta farin cikin ganinsa ba, kuma ba za ta ce ta na ɓaƙin cikin zuwansa ba, kawai dai halinsa ne yake ba ta tsoro. “Kun ga tabbaci, Wallahi haka yace shi saurayinta ne” Hafiza ta ƙara faɗi tana kallon bayan Rabi, Rabi ta juyo ta kallesu, su ma kuma su duka ita suke kallo. “Wai da gaske ne Rabi?” Cewar Kairiyya. Ta kasa cewa a'a, ta kuma kasa cewa eh, kawai ta ci gaba da tsayuwa a wurin, hannunta riƙe da wayarta. “Ni bari ma na leƙa na ganshi” Cewar Hafizan ta na miƙewa, leƙawar ta yi, Allah ya sa ta ga fuskarsa kuwa. “Ikon Allah, wai kin ga kamar da yake da ita kuwa?” Haka suka riƙa tasowa ɗaya bayan ɗaya suna leƙawa, sai mamaki suke ta yi, yayin da Rabi ta koma gefe tana karanta wasiƙar jaki. Kawu Abdullahi ne ya lura da su, hakan ta sa ya yi gyaran murya, bayan da ya gama bawa Hajiya labarin da Zaid ɗin ya basu. “Leƙen kuma na miye, ai za ku iya fitowa ku ganshi” Da gudu Fati da Kairiyya suka koma ɗakin cike da jin kunya. “Ko ba ku ji ba ne?!. Ku fito ku gaisa da yayan ku!” Ɗaya bayan ɗaya suka shiga fito suna gaisawa da Zaid, amma fur Rabi ta ƙi fitowa. Ba za ta iya fitowa ta haɗa ido da shi ba, gwara ta zauna a ɗakin zai fi mata sauƙi. Ta na cikin saƙe-saƙen nata ne Rhoda ta buɗo ƙofar ɗakin ta shigo, kanta ta ɗaga suka haɗa ido, da sauri ta miƙe ta isa gaban Rhoda suka rungume juna, duk yanda za ta kai da fushi da Raja ba za ta yi da Rhoda ba, don kuwa ita ba ta taɓa ganin aibunta ba. “Ya kike Rabi'a?” Cewar Rhidan ta na sakin Rabi, Rabi ta gyaɗa kanta cikin faɗin. “Ina cikin ƙoshin Lafiya” “Ashe ma kun san juna?” Jidda da ta biyo bayan Rhoda ta faɗa ta na dubansu. Rabi ta gyaɗa kai. “To kawu yace tare za mu kwana da ita, su sun fice, sai ki zo mu koma ɓangarenmu, dan su fati sun wuce” Ba tace komai ba ta kama hannun Rhodan suka raɓa Jidda suka fice. * “Ga su nan, suma 'yan uwanka ne, sai ku kwana tare zuwa gobe...” Cewar Kawu Abdullahi, a lokacin da yake sada Zaid da samarin gidan waɗanda ba su yi aure ba, su huɗu ne cas, Muhammad, Sani, Auwal da Zakar. Raja ya kallesu ya na gyaɗa kansa. A sanda ko wannensu yake gabatar masa da kansa, ɗaya bayan ya ya basu hannu suka gaisa, kafin suka nuna masa shimfiɗa in da zai kwanta, bai kwanta ɗin ba sai kawai ya zauna ya na saƙe-saƙe kala-kala a ransa. * “Rabi!” Rabi ta juya ta kalli Jidda da ta kira sunanta, ta na zaune ne a bakin gadonta, lokacin kusan ƙarfe sha ɗaya, amma Rabin bata samu rintsawa ba, tunani ya hanata ta yi bacci. Jidda ta taso daga kan nata gadon ta dawo ta zauna a bakin gadon Rabi ta na dubanta. “Me yake damunki?” Rabi ta kawar da kanta tana furzar da iska. “Babu komai” “A'a Rabi, duk yadda aka yi da komai. babu komai ba za ki zauna kina tunani ba. Kuma na lura da tun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112