Chapter 42
Chapter 42
na zuwa shara ajinsu, kuma a duk sanda za ta shiga ajinsu sai sun ci zarafinta. Da ƙyar ta haɗiyewa wani abu, sannan ta ce. “Ba... Ba komai” “Ƙazama kawai! Bar nan!” Ɗaya daga cikin yaran ya faɗi. “Dan Allah dubeta, kamar wata jaka, wai ƙwallo take san bugawa, in banda daƙiƙiya wa ya faɗa miki cewar matan arewa sun iya ball?!” Suka kwashe da dariya suna tafawa, Rabi ta juya za ta bar wurin jiki a sanyaye, sai ta ci karo da Mishal, wadda ke tsaye a bayansu ta na jin duk cin mutuncin da sukewa yayarta. Farin cikin ganin Mishal ɗin ya mantar da Rabi cin zarafin da aka mata yanzu, dan ta haura sati rabonta da ita. Sai dai yanayin fushin dake kwance a kan fuskar Mishal ɗin ya hanata yin komai, Misal ta ci gaba da kallon Rabi'a, hannyenta harɗe a ƙirji, kafi ciki ɗacin murya tace. “Seesee!” Rabi'a ta kasa amsawa. Mishal ta sa hannunta ta janyo Rabi'a zuwa bayata, sannan ta taka har gaban yaran ta fuskance su. Yaran da suka tsorata dan ganin Mishal suka fara ja da baya. Amma sai ta kamo kwalar ɗayansu, sannan ta kai masa mari, ta mangareshi harda haɗa masa da naushi a ciki, ta durƙusar da shi a kan gwiwoyinsa, sannan ta kamo ɗayan ma, shi ma marinsa ta yi, kafin ta durƙusar a shi, haka ta yi wa na ukun ma. Ta ja da baya tana tattare hannun suit ɗin jikinta. “Oya! Ku bata haƙuri!” Tsaresu da ta yi da idanu yasa jiki na rawa suka kalli Rabi'a, a tare suka bata haƙurin. Rabi da ta gama tsinkewa da lamarin Mishal ta kasa ko motsi, wai ahse da ma haka Mishal take?. “Seesee! Did you accept their apologies?” Rabi'a ta yi saurin gyaɗa mata kai tana dubanta. “Ku tashi ku ɓace min da gani” Jiki na ɓari suka miƙe, har da gudunsu wurin barin wajen. “Seesee kina san ball?” Mishal ta tambaya tana kallon Rabi'a, a sanda suka zauna kan ɗaya daga cikin kujerun 'yan kallo dake wurin wasan. Rabi ta kalli filin ball ɗin, sannan ta sauƙe dubanta kan Mishal. “Ina san na buga... ball wani sashe ce na mafarki na... Amma yanzu wannan mafarkin ya mutu, kusan shekaru biyar kenan rabona da bugata, amma har yanzu ina san buga ball” Mishal ta gyaɗa kanta cike da gamsuwa, ita ma kanta ta iya ball, amma ba ta da wani ra'ayi a kan buga ball ɗin, koyon kungu fu ya fiye mata amfani, tun da tana ga idan ta gama makaranata za ta shiga aikin soja ko na DSS. “Abu ne me kyau Seesee, kuma ina san na ga mutum ya tsaya a kan ra'ayinsa, musamman ma mu da muka kasance 'yan arewa, wani yanki da ba'a cika bawa mata hakkin kansu ba, a mafiya yawancin lokuta a arewa ana dannewa mata hakkinsu. A wasu lokutan ma za ki ga iyaye ne ke hana yarinya abun da take san yi, wata ƙila dan maganar mutane, ko dan suna so su aurar da ita, ko kuma dan suna ganin hakan ya saɓawa al'adarsu... Kuma hakan na ɗaya daga cikin abubuwan dake kawo mana koma baya a Nigeria, shi ya sa kudu suka fi mu ta ko wani fanni... Mu da muke da yawan addinin musulunci, addinin da bai tauyewa 'ya mace hakkinta ba, amma kuma al'adu sun danne hakan... Kin ga yanzu kamar wannan ball ɗin da kike san yi, a gaba ɗaya tarihin ƙungiyar ball ta mata a nigeria, 'yar arewa bata taɓa buga ball ba, ban ce babu masu so ba, akwai waɗanda suna san wasan, amma kuma an hana su, ana ganin kamar ball wasan maza ne, yanzu idan kika duba 'yan wasan super falcons, duka 'yan kudu ne, daga yarbawa sai iqbo, musulman cikinsu ma yan kudun ne, babu 'yar arewa ba haushiya ko ƙwara ɗaya... Insha-Allah Seesee zan baki goyon baya, idan har kin tabbatarwa da kanki cewar za ki iya, i will support you” Rabi'a ta yi shiru, ta tsirawa 'yar ƙaramar Mishal ɗin dake gabanta ido, ta yi tunanin sam Mishal ba ta da wayon da za ta iya yin magana kamar haka, duk zantukanta shiririta take ɗaukarsu. Bisa ga mamakinta sai ta ga Mishal ɗin ta na dariya. “Kin ji ni ina ta zuba ko?... Ni ma ban san daga ina zancen yake ta zuwa ba... Kwai ina jinsa ne a baki ne” Suka kuma yin dariya a tare. “Me yasa ba ki zo school ba wancan satin?” “Yayana ne ya rasu, sai kuma auren da aka min!” Rabi ta kasa ganewa abun da take ji, yayanta da ta tace shi kaɗai ne ya rage mata ta ke faɗin ya mutu, kuma ba ma haka ba, wai an mata aure?, Aure?, Kuma wai duk hakan ma ya faru ne cikin sati ɗaya da wasu 'yan kwanaki. “Kin ji abun wani banbarakwai ko?, Yayana ma'aikacin DSS ne, sun fita wani aiki, sai aka harbeshi, abokan aikinsa suka kaishi asibiti, kuma kafin ya rasu sai da ya bayar da aure ne ga wani abokinsa... Ni ma ban san da zancen ba, sai jiya da wani kawunmu ya zo yace wai mijina ya zo ɗaukata, yanzu haka ma shi mijin nawa ne ya kawo ni makaranta” Iko sai Allah, da ma irin haka na faruwa?, Rabi ta tambayi kanta. Ta ɗora hannunta a kan kafaɗar Mishal. “Ki yi haƙuri kin ji ƙanwata, ki ɗauki abun da ya faru da ke a matsayin ƙaddara, kowa yana da tasa kalar ƙaddarar, Allah ya ba ki ikon ɗaukan ƙaddararki, mijinki kuma ki masa biyyaya, ki bishi sau da ƙafa” Mishal ta yi murmushi tana sosa kanta. ”Aure?, Seesee abun mamaki yake ba ni, wai ni ce da aure?” Rabi'a ta yi murmushi. Saboda tuna irin farin cikin da suke kwana su tashi da shi ita da Anti Saratu a kwanakin nan, ba fon komai ba, sai don sabon saurayin da ta yi. _“Na kasa yarda Rabi, wai ni... Ni ce zan yi aure?, Aurena fa yace zai yi Rabi, aure?!”_ Abun da Anti saratun ta faɗa mata ke nan jiya, bayan da Fu'ad ɗin ya zo ya sanar mata da cewar shi aurenta yake san yi, kuma a shirye yake. Babban abun farin cikin ma shi ne, Kawu Habu yayan Abbansu ya yi bincike a kan Fu'ad ɗin, kuma an tabbatar masa da kawawan halaye da ɗabi'unsa. “Da ma haka abun yake ƙanwata, kana naka Allah ma ya na nasa, amma idan aka yi haƙuri aka jure, komai zai dawo dai-dai, ke dai ki yi haƙuri da abin da za ki gani a gidan auren ki, ki ji, ki ƙi ji, ki gani, ki ƙi gani, ki yi haƙuri, sannan ki riƙe addu'a...” Mishal ta shafi gefen fuskarta. “Seesee shi fa mijin da aka aura min ɗin, ba ya yawan magana, sai ya yi ta cin kunu, ni ba na gane kansa” “Haƙuri dai ake ƙanwata, wannan shi ne auren, idan ki ka daure zai dena fushin, har ya riƙa zama yana miki hira” “Wai da gaske ?” Cike da tabbatarwa Rabi ta gyaɗa mata kai. Kuma daga haka ta shiga mata nasihu kala-kala, irin waɗanda Anti Saratu kan mata a lokuta da dama. KULIYA
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112